MADADI 1-END

MADADI Page 81 to 90

Bayan fitar hajia Rabi da minti biyar ta dago kanta tana satar kallon mahaifiyar tata wada take ta kokarin sanja tasha daga freedom ta mayar redio kanoAm a hankali ta matsa kusa da ita ta riqe hannayenta murya na rawa tace”Baba dan Allah ki yafe min wallahi nayi nadamar abinda nayi muku kuma ni kaina nasan nayi kuskure mai muni nabi son zuciyata na jefa kaina a wahala, sai dai kuma a duk sanda naji kuna maganar kan cewa qaddarata ce hakan sai naji sanyi a cikin raina, yanzu babban burina shine na haihu lafiya na koma dakin mijina dana bujirewa auransa hakika yanzu na gane alkairi kuke nufi dashi ba sharri ba, nagane kuma babu wani d’a namiji da zan aura yaso ni kamar yanda Abbah Abbas ke sona Baba ku taya ni addua akan Allah ya mayar da aurana dashi.”

Baba Talatu ta ri’ke hannunta tace”Alhamdullhi dama ina adduar Akan Allah ya nuna min zuwan wannan rana da zaki gane muhimancin abinda mukayi miki *MADADI BA HARAM! BANE* kamar yanda kika dauka a baya kina ganin mun cutar dake saboda munce ki maye gurbin ‘yar uwarki Halimatu Naja’atu mune muka haifeki ba zamu ta’ba cutar dake ba, cancanta da nagarta muka hango shiyasa muke miki shawarar auran wannan bawan Allahn, a yanzu dai zamu iya cewa rabon wannan cikin na jikin ki yasa abubuwa da yawa suka kasance, babu abunda zamu ce sai dai muce Allah ya sauke ki lafiya bayan nan kuma mu roki Allah ya daidaita auranku dake da Alhaji Abbas domin shine babban burin mu dani da mahaifin ki.”

To har bayan la’asar Naja’atu na tare da baba talatu suna labari kamar babu abinda ya faru, sosai Naja’atu ta sake a gidan ta daina d’ari-d’ari dan abinci ma tare suka ci abin gwanin ban sha’awa, koda baba malam ya dawo ya tarar dasu suna hira sai yaji dadi sosai ya zauna kan abun zaman sa ana hirar dashi a fakaice yana yi mata nasiha kan zamantakewar rayuwa da yanda zata kula da kanta da duniyar baki daya….Sosai Nasihar malam take ratsa jikinta kafin ta bar gidan jikinta yayi sanyi sosai! ta dinga neman afuwarsa dangane da abubuwan da suka faru, lokacin baba malam ya nuna mata cewar shi dama duk abubuwan dake faruwa da rayuwarta bai qullace ta ba ya dauki al’amarin a matsayin qaddara wacce ko wane d’an adam yake tafiya da ita.

Daf da magariba ta fito daga gidan malam hannunta ri’ke da ledar magungunta kai tsaye gidan Alhaji ta nufa tana tafiya tana kallon kasa dan bata so ta dago kanta ta kalli fuskar wanda ta sani a unguwar gani take kamar ta zama abun kallo a gurin jama’a shiyasa ta sunkuyar da kanta………Sai data isa daf da gate din gidan sannan ta dago kanta aikuwa suka had’a ido dashi yana kokarin fitowa daga mota, d’an tsayawa tayi a bakin gate din tana murmushi har ya karaso inda take ta d’an risina tana gaishe shi ya amsa a nutse tare da tambayarta daga inda take dan bai ga sanda ta fito daga gidan baba malam din ba…..bayani tayi masa cewar tun bayan dawowarsu daga asibiti take gidan sai yanzu ta fito. Yace.”Ta shiga gida idan ya fito daga massalaci zai shigo yaga magungunan nata.

Cike da kuzari ta shiga gidan tana jin wani farin ciki na ratsa mata zuciya yanda ya amsa mata gaisuwarta da sakin fuska shine yafi komai faranta mata rai! jikinta na bata har yanzu da sauran sonta a cikin zuciyarta watakila shima yana jira ne ta haihu ya mayar da ita gidansa, wannan tunanin ya sanya zuciyarta tayi haske.

 Lokacin data shiga gidan hajia bata falo ta hau sama domin ta gabatar da sallah, sai kawai ta nufi dakin dakinta da take kwana, ta ajiye ledar maganin kan drowar ta cire hijabin dake jikinta ta shiga toilet domin ta dauro alwala……….Tana fitowa ta shimfida dadduma ta saka hijabinta ta kalli gabas………Bayan ta idar da sallar tana zaune kan dadduma tana jan istigifari a cikin ranta sai zuciyarta ta shiga kwad’aita mata abubuwan ciye ciyen wanda ta saba ci lokacin da take jos gidan Mmn Sajida…Duk daran duniya sai taci kaza mai ku’li-ku’li dasu albasa da sauran kayan had’i! ta kan rasa a ina Mmn Sajida take sanyawa ana siyo mata wannan kazar mai dad’in tsiya……Yawun bakinta ne ya tsinke hankalinta yayi masifar tashi idan fa ba ta samu damar cin wannan gashashshiyar kaza mai quli quli ba akwai matsala! miqewa tayi tana jin jiri jiri ta nufi falo tana had’a hanya kamar wacce bata ganin gabanta.

Kujera ta samu ta zauna hawaye na kokarin kufce mata, idan ta tuno da gashshiyar kazar jos mai dad’i ji take kamar tayi tsuntsuwa taje taci……Hajia ta sauko ta sameta a takure a guri guda..Tace”Naja’atu kin dawo kenan? nace ai yau kinyi yinin gidan malam ai naji dadin hakan sosai sannan Hajia Rabi ta sheda min bayanin da likita yayi a kanki gaskiya nayi farin ciki jin cewar lafiyarki lau dake da yaron dake cikinki.”

Murmushi kawai ta iya yi tayi shuru tana kallon guri guda! Hajia tace”A’a yana ganki wani iri ko bakya jin dadi ne.”? Girgiza kanta tayi tana yar dariya tace”Aa wallahi lafiyata lau.” Hajia ta bita da kallo tana kokarin ta fahimci wani a tare da ita!

Yaya Ramlatu ce ta shigo ta samu guri ta zauna a kan kujera Yaya Ramlatu dai kunya tasa ta kasa zama a gurin hajia sai ta gudu gurin Hajia Rabi can ta kai kayanta da Salim ya kawo mata sai dai ta shigo su gaisa………..Hajia tace”Gaskiya ban yarda ba akwai abunda ke damunki kada ki ‘boye min damuwarki naja’atu ni uwarki ce ki sheda min damuwarki.

“Murya na rawa tace” Wallahi bani da damuwar komai hajia.” Taqi fad’in maganar ne domin kada suga zaqewarta bata so ta dinga nuna musu kamar sun gaza dayi mata wani abun shiyasa takasa fad’a mata abinda take so

Abbah ya shigo ya tarar hajia na maganar, sai da suka gaisa tukkuna ya shiga tambayar abinda ke faruwa…..Hajia tace”Gata nan dai tunda ta shigo na ganta cikin wani irin yanayi jikina na bani kamar akwai abinda ke damunta.”

Naja’atu ganin Abbah Abbas din ya sake karya mata zuciya sai kawai hawayen da take ‘boyewa suka shiga zubowa.” Tasa gefan hijabinta tana kare fuskarta…su hajia basu gani ba amma shi ya fahimci kuka take, gyaran murya yayi as’usul kafin yace.”Naja’atu kina da damuwa me yasa ba zaki fad’a ba shuru ba zai amfana miki da komai ba idan baki fad’i lalurar ki ba zaki cutar da kan ki duba da cewar ke d’in ba lafiya kika cika ba, idan wani abu ke damunki kiyi bayani insha Allah za’a san yanda za’ayi.” Falon yayi shuru suna jiran suji ta bakinta.

Ita kuwa kukanta ne ya tsananta dan da alama shagwa’bar data kwana biyu bata ta’ba ba yau ita za tayi.

Al’amarin ya bashi mamaki ya kuma bawa su hajia mamaki sai kuka takeyi taqi magana….Yaya Ramlatu cikin kokarin sake wanke kanta tace”Haba ‘yar nan daga tambaya sai kuka dan Allah kiyi shuru ki daina kuka kada ki tayar mana da hankali wai shin meke damunki ne me kike so.”?

Cikin shashshekar kuka tace”Yaya Ramlatu kaza mai yaji da quli-quli nake so naci.”

Gabad’ayansu suka saki baki suna kallonta, danshi Abbah kasa ‘boye mamakinsa yayi yana ‘yar dariya yace.”Sabida kawai zaki ci kaza mai yaji da quli – quli sai ki dinga yiwa mutane kuka saboda shagwa’ba.” Hajia tace”nima dai abun ya bani mamaki wallahi haba Naja’atu meye abin kuka da damuwa da kin fad’a ai da tuni an siyo miki a bakin titi haba banji dadin wannan abuba wallahi bari na kira Dan azimi yaje *Murtala soya* ya siyo miki.” Kokarin miqewa take ya dakatar da ita da fad’in “Zauna hajia bari na siyo mata da kaina.” Hajia ta koma ta zauna da fadin “Yawwa dan Allah kayi sauri oh! ikon Allah ashe matsalar kenan.” Ya Ramlatu na murmushi tace”Ai hajia kin san dama wani cikin haka yake da azalzala idan yaso abu idan bai samu abunda yake so ba sai ya saka uwarsa a wani hali! na tashin hankali.”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button