MADADI 1-END

MADADI Page 81 to 90

Hajia tace”To ba ita kadai ba muma gashinan ya samu wani halin ikon Allah kenan Allah to Ubangiji Allah dai ya rabasu lafiya….Ya Ramlatu ta amsa da ameen tana jin dadin yanda mahaifiyar tata ta sake tana amsa mata maganarta.

Abbah yana fita motarsa ya shiga kai tsaye ya nufi inda yasan zai samo mata irin kazar da take buqata! *???? Ikon Allah a gaskiyar magana wannan soyayyar za tayi wahalar samu*

Ayi hakuri yau banyi posting a kan kari ba????????

*Littafin na kudi ne….!*

Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abin yake…..Vip group #600 normal gruop#300…account… 0542382124…Binta umar gtbank…Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

67****To tundaga wannan rana Abbah Abbas ya d’orawa kansa nauyin siyo kaza mai yaji da qul-quli bama kazar kawai yake siyo mata ba harda sauran kayan kwad’ayi yake kawo mata, kafin kice kwabo Naja’atu ta sanja dik wannan ramar babu tayi qiba sosai saboda tana samun kulawa ta kowane bangare! Iyayenta kuwa rasa bakin magana sukayi danganin irin karamci da kulawar da ‘yarsu take samu a gidan Alhaji Samaila ya sanya kullum basa gajiya dayi musu addua gami da fatan gamawa da duniya lafiya hakika Alhaji Sama’ila dashi da iyalinsa sun nuna musu kara gami da kauna sun dauki naja’atu sun ri’keta tamkar sune suka haifata basu da abinda zasu yi musu face adduar dacewa da samun rahamar ubangiji.

*Bayan sati biyu*

Al’amuran sunyi wa Abbah Abbas sauqi katuwar rumfarsa wacce wuta ta cinye ta dawo sabuwar dal kamar ma wani abu bai faru ba, a yanzu kayan da suke cikin rumfar sunfi nada yawa rumfar cike take da irin kayayyakin da jama’a ke bukata, kada ku dauka ko yaci bashi a gurin abokan sana’arsa ko daya Allah babu yanda baya zartar da ikonsa Abbah Abbas dalilin wannan abu da ya same shi ya janyo masa samun alkairi sosai daga gurin abokanan sana’arsa ta kwangila ita kanta gwamnatin garin sai da ta bashi tallafi dan ganin irin hidimar da yake mata hausawa dama suka ce wani hanin ga Allah baiwa ne, Abbah ya samu matasa wanda suka rasa aikin yi ya samar musu gurbi a cikin rumfunan sa dake kasuwar, Yanzu Abdulhamid shine a matsayin babban yaronsa ya yarda da yaron sosai ya amince da gaskiya da amanarsa shiyasa yaja shi a jikinsa yana nuna masa yanda harkokin kasuwanci suke saboda gaba baya so duk wanda yake karkashinsa ya dawwama a gurin yi masa bauta ya fiso kowa ya tsaya da kafafunsa shiyasa ko kad’an baya yiwa yaransa mugunta ta kowane fanni suna jin dadin zama dashi

*( Haka ake so shugaba ya zama adali mai kaunar cigaban na qasa dashi mafi akasarin abinda yake damun wasu ‘yan kasuwar kenan kiga mutum kullum kansa ya sanyi daga zarar yaga wanda yake qasa dashi zai tashi sai ya mayar dashi ya dankwafe! kullum dai yafi so yayi ta zama a karkashinsa yana masa wahala…..Wannan ba adalci bane idan kana so kayi qarko jama’a su dinga fad’in alkairin ka to kada ka saka ganin kyashi da ganin ido a cikin al’amuranka idan ka samu abunda ka samu sai ka sakarwa na qasa da kai shima ya samu….Allah ka karemu da ganin kyashi da hassada)*

*BASH!*

To Bash ya samu nasarar k’etara kasar Najeria inda kai tsaye ya sauka a ‘kasar ghana tare da maqudan kudaden da suka sato a bank….Akwai abokansa a garin saboda haka yana sauka a airport ya kira daya daga cikinsu, ko minti talatin baiyi ba a gurin wata zungureriyar bakar mota tazo ta daukeshi, koda ya shiga motar sai yaga duk guyz ne irinsa shi kadai ne musulmi ma a cikinsu dukkaninsu kafurai ne yawancin su ma had’uwa kawai sukayi da juna kowanne da kasar da ya fito.

A daran sukaje gurin canjin kudi zunzurutun kudad’en da bash yaje musu dashi su sanja aka basu irin na ‘kasar……….Duniya sabuwa suka bud’e dama akwai ‘yan garin guda biyu wanda suke da daurin gindi kasancewar iyayansu ‘kososhi ne a cikin gidan gomanati. shiyasa duk ta’addacin da suke babu wanda ke musu magana, suyi shaye shaye su kama yaran mutane suyi musu fyad’e komai kankantar yarinyar mutukar tsautsayi ya ritsa da ita to basa saurara mata, dan akwai lokacin da suka shiga wata bording skull a garin, suka haikewa yaran mutane sai da sukayi raping din sama da mata talatin suka fito suka barsu cikin jini da wahala, abun mamaki gwamnati ba ta wani dauki mataki mai tsauri a kansu ba……Bash yayi masifar jin dadin had’uwa da guyz d’in nan suka bud’e shafin iskanci irin wanda suke so, sace sace shaye shaye fyad’e Luwad’i da duk wani mummunar aikin da Allah ya haramta yi sukeyi Bash tuni ya kafurta kansa ya zama kafuri tunda yaje garin bai kalli gabas da sunan zai gaishe da Ubangiji ba sharholiyarsa kawai yake babu abunda ya dameshi.

Munira kuwa tayi ciki da Muktar ya koreta daga gidansa yace tun wuri taje ta nemi uban danta kuma ya fasa auranta domin abinda yake bukata a gurinta ya samu saboda haka idan ta sake zuwar masa gida sai ya karya mata kafafu! Munira ganin bata da gata yasa ta hakura ta kyaleshi ammafa taci kuka ta koshi kuma tayi nadamar wautar data tafka, yanzu tana gidan kanwar mamanta mai suna Hajia Zulai bakar wahala take bata a cewar matar lokacin da ludayin su yake kan dawo basu taimaka mata da komai ba dan haka bata ga wanda zai dauko wahala ya dora mata ba, Munira hakuri kawai take a gidan Hajia Zulai ita taci mutuncinta ‘Ya’yanta su wulakantata watarana da yunwa take kwana ga ciki a jikinta Munira ta gane duniya abar tsoro ce dan idan ta juya maka baya sai ka zama tamkar kashi a idanun mutane.

Alhaji Aminu da matarsa kuwa suna can a kulle dan har yanzu ba’a yanke hukunci ba an dai rufesu a kebantaccen guri, gwamnati tasa a cigaba da bukince inda Bash din ya fake dan tuntuni an yankewa sauran abokan nasa hukunci kisa bayan sun gama zaman gidan kaso na shekara goma……Tsanani tashin hankali Alhaji Aminu da Mommy suka shiga suka dinga kuka suna dana sanin abinda suka aikata na dora d’ansu a turba mara kyau, duk bayan sati biyu sai ‘yan jarida abokanan aikinsa sunzo sun titsiye shi da tambayoyi kamar ma da gayya suke zuwa su turkeshi, takaicin hakan yasa ciwon hawan jini ya kamashi, yau da lafiya gobe babu.

 ****

To zamantakewar gidan Abbah Abbas sai dai muce alhamdullahi dan a tsakanin Halisa da Zainab an samu fahimtar juna duk ta dalilin jajurcewar jagoran nasu wato shi wanda ya ajiyesu a gidan, tuntuni Zainab ta daina rawar kai wanda ada take ta daidaita nutsuwarta yanzu ta kanta ma takeyi cikinta yayi wata hud’u! jikinta ya soma amsawa hankali ya fara shiga jikinta! gabad’aya sai tayi rauni ta kasa daukar lalurar mijin nata kamar wacce ta kusa haihuwa haka ta koma ciki wata hud’u, amma har ya fito kasancewar ta mai jiki da tumbi shiyasa cikin yayi saurin nuna kansa….Abbah nada tausayi sosai shiyasa baya takura mata da fitina lalla’bata yake da dukkanin abinda take so burinsa kawai ta sauka lafiya.

‘Bangaran Halisa ta samu lafiya sosai dan a jikinta ma tana jin hakan ta daina jin kyaikyayi ta kuma daina zubar da ruwan da takeyi, sai ta fad’a masa cewar yana da kyau ta sake komawa asibiti su dubata domin su tabbatar mata da ingantuwar lafiyarta, da yake shima a cikin matsala yake sai ya dauketa da kansa ya kaita asibitin, Aikuwa kyakykyawan result ya fito Halisa kwayoyin cutar Gloria da take dauke dasu sun mutu yanzu mu’amula ta aure zata iya cigaba da gudana a tsakaninsu, amma dai duk da haka sai da Dr Sa’adatu ta rubuta musu wani magani wanda ‘ka’ida ita dashi ne zasuyi amfani dashi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button