MADADI 1-END

MADADI Page 91 to 100

Sun kai kimanin Mintina ashirin a dakin Zainab din kafi su miqe Hajia tace zasu shiga gurin halisa su gaisa.” Zainab tace”To hajia nagode sosai Allah ya qara girma.” Hajia ta amsa da ameeen sannan suka fita daga dakin.

Yanayin yanda suka samu Halisa cikin damuwa yasa daga hajian har Najaatun suka tausaya mata, Halisa bata ‘boyewa hajia abinda ke damunta ba sai da fad’a mata komai Hajia tace”Kada ta damu insha Allahu ita da kanta za tai masa maganar zuwa asibitin insha Allahu kuma za’a dace idan anje dan haka ta daina damuwa.” Halisa taji dadin zuwan hajian sosai da sosai kuma tasan tunda tace zatayi masa magana to zai dauki al’amarin da muhimanci……..Hajia da Najaatu basu jima sosai ba sukayi mata sallama suka fito, Halisa har bakin mota ta rakasu sai da direba yaja motar sannan ta koma gurinta tana jin sassauci a cikin zuciyarta amma hakika abinda ‘Yan uwan Zainab sukeyi a gidan ya fara bata haushi ‘barna da samun gurin da sukayi yayi yawa basu da hankali ko kadan kuma sun fito da kwadayinsu a fili kamar ba ‘ya’yan fitaccen malami ba.

To har dai yanzu abinda ke faruwa a tsakaninta dashi shike faruwa tunda ta dawo gaisuwa ce kawai a tsakaninsu daga ita babu wata magana sai dai kallo, watarana idan yazo tana zaune a falo barin falon takeyi bayan sun gaisa dan ta tsani munafikin kallon da yake mata wanda daga zarar yaga zasu had’a ido sai yay sauri ya dauke kansa, haushin hakan yasa take barin gurin inda shi kuma yake jin haushin hakan yafi so ta zauna yana dan kallonta ko yafi fahintar abunda suke tattaunawa da mahaifiyarsa.

Ranar kwana biyar da haihuwa yasa Abdulhamid ya kai kayan barka gidan Alhajin kamar yanda hajia ta umarceshi….akwati uku manya shaqe da kaya sai kace amarya, akwatin babyn ma guda daya ce amma na Zainab har uku….ita kanta hajian sai da tayi mamakin abun harda set din gold masu nauyi da tsada!….Ya Ramlatu ta dinga masifa da fad’in “Wannan kayan sunyi yawa kuma basu dace da yarinyar ba haba sai kace hauka bayan lefan da akayi mata saboda ta haihu sai a sake yi mata wani.

Hajia ta katseta da fad’in ” Ke bana son ganin ido dan Allah ko wace haihuwa da goshinta meye dan anyi mata ai haihuwar fari ce saboda haka kada na sake jin wannan magana duk abinda zainab ta samu rabonta ne.

Ramlatu tace”Hajia duba fa kiga wannan uwar sarqa ki daga kiji nauyinta anya Abbas yana sane yake ‘barnatar da dukiyarsa bayan ga ‘ya’ya ya fara tarawa abun yay yawa.” Hajia tace”Ni dai nace ki bar maganar nan kome zainab ta samu rabonta ne saboda haka ki hada komai a inda yake anjima da yamma sai kuje ku kai musu.”

Ramlatu shuru kawai tayi tana mamakin al’amarin…..To itama Najaatu nata ‘bangaran sai da taji wani iri daurewa kawai tayi tana kokarin cire kanta daga abinda be shafeta ba amma ita kanta wannan set din gold din ya bata sha’awa sosai….

*Littafin na kudi ne….!*

Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya ga yanda abun yake…..Vip gruop#600 normal group #300 account… 0542382124…Binta umar gtbabk

WhatsApp number

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

*MADADI 76_77*

Abinda su hajia basu sani ba shine tun ranar kwana biyu da haihuwar Zainab ta tisa shi a gaba ta dinga lissafa masa abubuwan da take so, Allah sarki Abbah sarkin adalci sai yace to ta fada masa iya adadin kudin da take bukata, bata fada masa a ranar ba sai ta bari babbar yarta tazo ta fad’a mata inda ita kuma kai tsaye tace”ki fada masa dubu dari biyar zai baki. Zainab tayi shuru tana mamakin uban kudin da yayartata ta tsuga! tace.”Anya aunty kudin basuyi yawa ba.”? Murmushi tayi tace”Idan miliyan kikace kina bukata yana da ikon da zai baki mijinki fa yana da kudi ne wanda be san a dadinsu ba meye a ciki dan ya baki dubu dari biyar ‘ya guda fa kika haifar masa darajar dan mutum yafi komai.” Zainab tace”To zan gwada nagani anty bana so yaga rashin hankalina wallahi.

Tace”Baki da wayo zainab na fada miki fa yanzu ne lokacin ki amma tunda kina ganin kamar wani abu shikkenn kanki zaki cuta ba wani ba, yanzu idan ya baki kudin nan sun isa ki siyi komai na qawa da kece raini ke har sai sunyi miki saura sai ki ajiye a account dinki kyayi wata bukatar dasu 

Zainab tace”To shikkenan bari ya shigo da daddare zan fada masa.”

Zainab tayi mamaki lokacin data fada masa a dadin kudin da take bukata yace babu matsala zai saka mata a account dinta in yaso duk abunda take bukata baby ke bukata sai tasa ‘yan uwanta su cire kudin su siya mata…….Zainab yana fita ta dinga murna da farin ciki kanta na sake girma tana tunkaho da cewar ita din ‘yar gaban goshi ce wannan zunzurutun kudin da ya bata tayi hidimar haihuwarta yasa ta daina jin haushin abubuwan da yayi wa Najaatu a lokacin data haihu, ta tabbata kyauta da hannun bayarwa a jinin jikinsa yake……koda yan uwanta suka zo ta nuna musu shedar kudin a wayarta sai suka dinga mamaki! wasu daga cikinsu har sai da hassadar su ta fito fili, babbar yarsu aunty Hauwa tace”To sai ki bani Atm din ki naje da kaina zan had’o miki kaya na alfarma wanda zaki fita kunya dashi ranar suna.” haka kuwa akayi aunty Hauwa yayar Zainab itace duk ta had’o kayan barka saboda tsabar rashin hankali duk ta qarar da kudin gurin siyawa ‘yar uwarta 

kayan banza da wofi amma baby ta tashi da akwati daya itama ba wasu kayan kirki ne a ciki ba. 

Ita kanta Halisa da aka kai kayan ta shiga ta gansu sai da tayi mamaki! daurewa kawai tayi ta dudduba tasa albarka ta nufi gurinta, aikuwa tana fita ‘yan uwan Zainab suka shiga dariya kowa na fadin albarkacin bakinsa akanta wai ‘yar bakin ciki ce hassada tasa ta kasa zama ta duba kayan a tsanake, ita kuwa zainab sai wani figala take tana fad’in ita waye yasan abunda akayi mata a baya saboda haka taje tayi ta hassadarta idan ma mutuwa za tayi ta mutu babu ruwanta.” Babu wanda yay mata fadan arziki sai ma qara zugata da suke idan tayi arbain tace ya siya mata mota. kai tsaye tace”Dama ai yanzu abinda yake gabana kenan naga ina hawa babbar mota wacce tafi ta Halisan kudi da girma.”

Halisa kuwa sa masa ido kawai tayi taga iya gudun ruwansa, shin ita da yara me ya tanadar musu na fitar suna ai ko turaman atamfofi ya kawo musu suma su sanya, tun ranar da sukayi cacar baki akan Najaatu suke sama sama da juna dan haka ana ya gobe suna ta same shi yana shiryawa zai fita tace”Naga kayan barka na Zainab sai nace to mu ina namu kayan fitar suna ni da yara.”

Ba tare da ya kalleta ba yace.”Kinyi magana kina bukata ne? Tace”Sai nayi magana zaka san abinda ya dace a qallah dai ai muma ka kawo mana namu ba sai nayi magana ba tunda muna da hakki.

Yace.”Itama bani naje nayi mata siyayya ba dan bani da lokaci kudi na bata kuma kin san dole ayi mata hidima tunda haihuwa tayi.” Tace”Ina ruwana da haihuwa tayi ni ina maka maganar akan hakkina da yara na.” Afusace! yace.”Ke! Halisa ba zanyi ba! uwata ce ke zaki sani a gaba kina nuna min abunda ya dace to ba zanyi ba nace! kusa wanda kuke dashi.” Yana gama maganarsa ya buge rigarsa tare da daukar wayoyinsa ya qara gaba….Halisa ta jima tana mamakin wannan al’amarin ta dinga tunanin hukuncin da zata dauka a kansa, miqewa tayi a guruguje tayi wanka ta fito ta shirya key din motarta ta dauka ta kama hanyar fita 

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button