MADADI Page 91 to 100

Daidai kofar gate din Zainab ta dinga jiyo hayaniyarsu sai shewa sukeyi da fad’in gobe har d’an asharrale zasu dauko su cashe! Motar ta kawai ta shiga ta fita daga gidan, kai tsaye kofar na’isa ta nufa.
Lokacin data isa gidan Hajia da Ramlatu na zaune a palo suna hira Najaatu na daki tana bacci….Halisa ta samu guri ta zauna fuskarta a ba’ce! Hajia tace”Halisa Allah yasa dai lafiya na ganki da tsakar rana ina fata dai ba wata matsala bace…..Halisa kasa magana tayi sabida tunda take bata ta’ba kawo kararsa gurin iyayensa ba ba dan bayayi mata laifi ba kawai tana hakuri ne amma hakika yau ya kaita bangon makura….Ta gaida hajian murya na rawa ta shiga sheda mata abunda yake faruwa, Tace”Saboda nace ya mayar da Najaatu gidansa yake jin haushina kullum babu kalma mai dadi to yau dan nayi masa magana akan hakkina dana yara ya farfad’a min magana iya son ransa Hajia wallahi ina hakuri da halin Abban mufida ina ganin zan tafi gida kawai na bashi guri.”
Hajia tayi shuru tana nazarin maganar Ramlatu kuwa hasala tayi tace”Ai wannan yarinya fitinanniya ce wallahi watakila ma ita ta hanashi yay muku komai aini tunda ta zugashi ya dauko min police ta fita daga raina, kuma haka kawai saboda kin bashi shawarar arziki sai ya dinga jin haushinki to meye da Najaatun da yake gudunta.”
Najaatu jin hayaniya a falo yasa ta fito daga daki ta samu guri ta zauna tana kallonsu da so ta fahimci inda maganar ta dosa…..Halisa tace”Wallahi kuwa Yaya Ramlatu Abban Mufida wani iri ne yana son abu amma sai ya dinga nunawa baya so saboda nace idan ya tsaya wasa wani zai aureta duk da jegonta shine fa yake Jin haushina.” Hajia tace”Duk dai yanzu magana ta kare kiyi hakuri ki koma gida kada ki tafi gidanku idan yazo da yamma zanji dalilinsa na danne miki hakki maganar zuwa asibiti dama munyi dashi kancewar sai bayan suna hankali ya kwanta zai kaiki yace watakila ma dubai zakuje a dubaki sosai.”
Jin wannan magana da hajia tayi yasa Halisa taji sassaucin akan bacin ran dake zuciyarta sai ta miqe tana gyara mayafinta da fadin ita zata tafi.” Hajia da Yaya Ramlatu suka sake tausarta akan kada tace fa zata je gida ta koma dakinta, nan ta tabbatar musu da cewar gidan zan ta koma insha Allah….Bayan fitar Halisa Najaatu tunani ta shigayi ta fahimci maganganun da Halisa takeyi a kanta wato saboda tace masa ya mayar da ita yake gaba da ita to ita kuwa wace iriyar kiyayya yake mata da har zai dinga gaba da wani a kanta…..Allah sarki Halisa ashe yanzu tana kaunarta tunda gashi har tana cewa mijinta ya dawo da ita. jin hawaye na kokarin su zubo mata ne yasa ta miqe da sauri ta bar gurin.
Hawaye na sauka a kan kumatun ta ta zaune gefan gado tana tunanin abinda zai taimake ta, gabadaya ji tayi zaman gidan Alhajin ya fita daga ranta, ba dan komai sai dan tayi nesa dashi da duk abinda ya shafe shi tana ganin idan ya daina ganinta sai tafi martaba da daraja a idonsa, me yay zafi da har zai dauki fushi da gaba akanta ashe dama haka kiyayyar ta tayi girma a zuciyarsa……….. yanzu idan tace zata koma gidan Malam su hajia hankalinsu zai tashi kuma ba zasuji dadi ba sannan zasu dinga tunanin ko wani abun suke mata na rashin kyautawa yasa take gudun zama dasu, amma da badan hakaba da wallahi barin gidan za tayi domin ba taga amfanin zamanta a ciki ba
Tana wanka tana tunanin maganarsu da Mmn Sajida….Itafa gani take dukkanin wani abu na jan hankali da za tayi masa bai zama lallai ya kalleta da qima da daraja ba , amma dai tana ganin zata kwatanta yin wasu abubuwan ko Allah zai sa a dace.
Shiryawa tayi tsaf! ta fito ta samesu har yanzu suna falon suna tattauna maganar, sai ta nuna tamkar ba taji abinda suke magana a kai ba…..Hajia tace”Ya na ganki da hijabi ko gidan Malam zaki shiga.”? Tace”Eh inaso na shiga mu gaisa bayan na dawo daga gidan Lalle (‘Kunshi) inaso nayi kwalliyar suna.” Hajia tace”Aikuwa yana da kyau hakan to da akwai kudi a gurinki ne.” Tace”Eh akwai wanda zasu ishe ni.” Yaya Ramlatu tace”To ko zaki bar Daddy a gida kyafi samun nutsuwa gurin zaman kunshin.” kokarin kwanto yaron take daga bayanta tana fadin ” Aikuwa kin kawo shawara mai kyau Yaya Ramlatu dan yana iya rikice min da rigima ya hana lalle na yayi kyau. Yaya Ramlatu ta kar’be shi da zanin goyonsa ta miqe tana kokarin goya shi a baya tace”Ai har kyaje ki dawo yana baya idan ya tashi a bacci sai a dama masa madara.” Hajia tace”Duk da haka dai kada ki zauna kada a shiga hakkinsa.” Tana kokarin fita tace”Insha Allah bazan jima ba zan dawo.
Gidan Lallen kabuga ne kuma lokacin da taje akwai mutane dan ma mai lallen kawar Salimat ce budurwar Salim wacce a lokacin auranta da Bash yasa ta gane gidan…..Dalilin wannan sanayyar yasa Bilki mai kunshi ta tsallake mutanan dake gabanta ta kama kafafun Najaatu tana yi mata, aikuwa jamaar dake gurin suka dinga surutu kowa na ganin an shiga hakkinsa….Tace” Dan Allah kuyi hakuri na bar karamin yaro ne a gida kuyi min uziri.” jin haka yasa wasu suka daina magana wasu kuwa fushi sukayi suka tafi…..Bilki ta dauki lalle mai tsayi da ado da yawa, Najaatu tace”Bilki da kinyi min takaitacce tunda kinga akwai jamaa a gabanki.” tace”na riga na dauki mai ado dole kema sai kin jure zama.” shuru kawai tayi ta zubawa kafafunta ido wanda bilki ke zane su da jan lalle.
Kafafuwa da hannuwa akayi mata jan lalle mai kyau da burgewa sosai kunshin ya dauki hankulan jamaar dake gurin suka dinga so ayi musu irinsa.
Sai bayan biyar da Rabi na yamma sannan ta cire lallen ya wani fito rad’au a kafafunta na hannun ma yayi abun burgewa, Najaatu sosai tayi farin ciki da yanda Bilki ta fito da ita kamar wata amarya…..Dubu biyar ta bata saboda jin dadin abinda tayi mata bayan haka kuma zuwanta yasa wasu costoms din sun tafi shiyasa ta bata wannan kudin……………Ta jima a bakin titi tana neman abun hawa bata samu ba, da yake yamma tayi duk ‘yan kasuwa sun tashi tun daga mandawari ake fama da goslow har titin kabuga gurin ya had’e sosai masu motocin gida dana haya kowa na kokarin wuce wa, da kyar ta samu a daidaita sahu wanda zaije kofar na’isa amma kuma duk maza ne a ciki su biyu…..Ganin bata da mafita yasa kawai tayi kundubala ta shiga, aikuwa samarin nan suka dameta da hira da yake aboki da aboki ne duk a tunaninsu sun dauka budurwa ce wai dan Allah ta basu number wayarta, Najaatu shuru tayi musu tayi bala’in shan kunu! na kusa da ita ne ya kalli hannunta data dora a jikin k’arfen adaidata sahun yace”Baby wannan lallen yay kyau nawa ne kudinsa na biya gaskiya kina da kyau gaki da aji wallahi kin burgeni kuma ina shaawar auranki.”
Tace”Kai dan Allah ku kyaleni da surutu lalura ce ta fito dani kuma ni ba budurwa bace matar aurece.
Dariya kawai sukayi suna fadin”Aikwai ‘yan mata irinki da yawa masu kiran kansu da matan aure amma basu bane matar aure ta fita daban baby….Takaici yasa tayi musu shuru tana Allah Allah ta sauka…..kawai sai taji suna cewa mai adaidata sahun kada ya saukesu a inda zasu sauka suna so su rakata gida….Gabanta ya fadi ta kallesu rai a bace tace”Wallahi zaku janyowa kan ku wato na fada muku ni matar aure ce kuna gaddama ko okey.” Daga haka sai kawai taja bakinta tayi shuru ta kyalesu tana jinsu suna ta dariya da surutai a kan maganarta.