MADADI Page 91 to 100

Ana kokarin shiga massalaci domin sallar magariba adaidaita sahu ta tsaya a kofar gidan alhaji…..Motar Abbah Abbas da taga ni a fake a inda ya saba ajiyewa yasa gabanta ya tsananta faduwa. Tana kokarin dauko kudi a jakarta ya fito daga gidan Alhajin fuskarsa tamkar hadarin dake dab da zubar da ruwa, tunda yazo gidan ya samu yaro na kuka da neman uwarsa ransa ya ‘baci ya tambayi Yaya Ramlatu ina take? tace Ta tafi gidan kunshi…..Ai sai ya shiga surfa mata masifa kamar ubanta harda cewa rashin hankali ne da zata kama d’aukar yaro ta rabashi da uwarsa yini guda saboda haka ai sai ta daukeshi ta kaiwa uwarsa kada su kashe shi.” Ya Ramlatu ta dinga mamakin tsawar da yake buga mata sai so take ta fahimtar dashi yaki fahinta wai itama ta mayar da kanta karamar yarinya mara tunani, Hajiya da taga abun nasa naso ya wuce gona da iri tace”To wai kai ina ruwanka ne? ko auran yarinyar nan kake da zaka takura mata kunshi ta tafi domin ta gyara kanta kuma bamu dauka yaron nan zai tashi ya dinga rigima irin hakaba itama watakila rashin abun hawa ne ya tsayar da ita dan haka abar maganar haka uwar yaron itama nasan tana can hankalinta a tashe…….Cikin wannan ‘bacin ran ya fito daga gidan sai kuma yaci karo da wani dan samarin nan sun kewaye ta sun hanata wucewa wai sai ta basu number…. Ganinsa yasa ta kid’ime! pose dinta ta fad’i ta sunkuya dauka saurayin shima ya tsuguna hannunwansu ya hadu guri daya. tana dagowa ta wanka masa mari jiki na kyarma ta dauki pose dinta ta barsu a gurin….Komai a kan idonsa ya faru yana kallonta tana tawowa yana ji kamar idan ta karaso yayi wurgi da ita saboda jin wani mahaukacin kishi dake taso masa, gifta shi tayi da sauri ta tura karamar kofar gidan ta shiga gabanta sai wani irin bugawa yake……matasan samarin nan kuwa adaidata sahun suka shiga takaici kamar ya kashe su su basu samu number ba gashi sun sha mari amma babu komai tunda sunga inda ta shiga watarana zasu kawo mata ziyara dansu basu yarda matar aure ce….Abbah sai da yaga Adaidata sahun ya bar gurin sannan ya wuce cikin massalaci yana jin wani irin zafi a cikin zuciyarsa.
Najaatu na shiga gidan taji yo muryar daddy nata zabga ihu! da sauri ta shiga falon ta tarar dasu sunyi cirko cirko hajia rabi na rike da waya a hannunta tana kokarin nemo number…..Sallamarta yasa duk suka kalli bakin kofar shigowa Ya Ramlatu ta karasa gurinta da sauri ta miqa mata yaron da fadin”Kar’beshi kada azo a tafi dani yanzu yanzu aka gama cin mutuncina.”
Hajia Rabi tasa dariya da fad’in “Wallahi Ramlatu baki da dama waye zai tafi dake.”? Rike baki tayi tace” Haba Hajia kina kallonsa fa ya dinga zazzaga kamar zai doke ni ke kyace shine yake gaba dani wallahi Abbas ya raina ni sosai amma babu komai.
Najaatu taji tausayinta ya kamata tace”Dan Allah Yaya Ramlatu kiyi hakuri wallahi dana san zan dade gurin k’unshin nan da na tafi da yaron nan yau goslow akayi sosai da kyar ma na samu abun hawa.” Hajia tace”Nima sai da na zargi haka wallahi to me yasa baki kira Dan Azimi yazo ya daukeki ba.” Tace”Gabadaya hankalina bai kai nayi tunanin hakaba wallahi.
Hajia Rabi tace gashinan kuwa kwalliya ta biya kudin sabulu kunshin yayi kyau sosai da sosai.” Najaatu ta nemi guri ta zauna tana kokarin ciro nono tasawa yaron a baki tace”Wai ma duk da haka akwai wanda suka rigani darajar Salimat budurwar Salim naci akayi min da wuri.” Hajia Rabi tace” lallai zuwa gidan ‘kunshin sai mutum yayi da gaske…Hajia tace”Aikuwa dai kafin ayi kwalliya sai an ji jiki mu lokacin mu idan muka daure kafafun mu da lalle shikkenan bukata ta biya mu wayi gari rad’au damu amma zamani yanzu komai ya sanja Allah ya kyauta.” tana ta gama maganarta miqe da niyyar zuwa tayi sallah Yaya Ramlatu da hajia Rabi ma tafiya sukayi sallah suka barta ita kadai a falon tana shayar da d’anta tare da tunanin irin kallon da taga Abbah Abbas nayi mata a d’azu! yanda taga fuskarsa a murtuke yasa dik hankalinta ya tashi tana tsoron ya shigo yay mata fad’a.
Tana kokarin barin falon ya shigo….Tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na fad’uwa. Nasa ‘bangaran ganin nonota guda a bayyane yasa hankalinsa ya tashi sai yaji gabadaya ma yana nema ya rasa karsashinsa….Najaatu sam ta manta tana shayar da d’anta nono shiyasa bata gyara ba, Da kyar ya karasa shigowa yana ta bin ta da kallo ‘kunshin dake kafafunta da hannayenta ya tsirawa ido, yayi masa kyau a ido, dauke kansa yay daga kallon kafafunta yay gyaran murya kamar koda yaushe Yace.”Najaatu wane irin rashin hankali da rashin imani ne yasa zaki tafi yawon banza ki bar yaro karami irin wannan a gida yay ta kuka kin san hakkin d’an adam kuwa.”? A kausashe yay maganar….Ta dan kalleshi tana zum’bura baki tace”Abbah ba yawo naje ba naje gurun ‘kunshi ne.” Da sauri yace.”Wa kika ajiye da zakiyi wa kwalliya ko kina da miji ne.”? Gabanta ya fadi ta kalleshi tace”Sai ina da miji zanyi kwalliya ai mace da ado aka santa.”
Yace.” Sam Ban san da wannan maganar ba kawai dai kin fita ke kad’ai ne dan ki samu samari kuma na gani kin samo to mutukar yawo zaki dinga fita kina barin yaro zan samu Baba malam na sheda masa abinda kikeyi nasan shi zakiji maganarsa tunda ni kin raina tawa maganar saboda kina samun daurin gindi a gurinsu hajia! dan haka wannan itace maganata ta karshe da zanyi miki kada ki kuskura ki kara barin yaro a gida ki fita yawon zagayen samun zawarawa.”
Kuka take sosai tace”Wai dan Allah Abbah wannan wace irin magana kake kana kallon ‘kunshi fa a kafafuna amma kake cewa ina tafiya yawon samo zawarawa ashe har sai na fita zagaye bazawari zai biyo ni ni ba’irin wannan zawarawan bace ko yanzu nayi niyyar aure sai nayi saboda inada wanda zan aura a hannu.” Ta fadi wannan maganar ne danta tunzura shi, aikuwa ya tunzuru ya dinga zazzaga mata fad’a da fad’in “kamar shi zata sashi a gaba tana yi masa rashin kunya to zai fita harkar ta tunda ta zama ‘yar kanta, fad’a yake mata sosai harda miqewa tsaye kishi na nema yasa ya fad’i a gurin.
Hajia ta sauko daga sama da sauri tana fad’in “me yake faruwa ne wannan fad’a da kake yi kwana biyu ya isa fad’a a gida fad’a a inda bai dace ba to ita kuma Najaatu mai tayi maka.”?
Zama yay kan kujera yana numfarfashi, ya cire hularsa ya ajiye kawai ya shiga girgiza kafafunsa….Najaatu daukar d’anta tayi ta bar gurin tun kafin zuciyarta tayi bundiga…..Hajia ta kalleshi tana so ya samu sassauci ta fad’a masa hukuncin data yanke dan ta gaji da wannan hargagin da yake…….
78***Hajia sai da ta tabbatar da cewar ya dawo cikin hayyacinsa sannan ta fara magana kamar haka.” ‘Dazu da safe Halisa tazo gidan nan cikin ‘bacin rai tare da qudirin tafiya gidansu akan abubuwan da kake a gidanka na rashin kyautawa to naji ta banki ta kuma na rarrasheta tayi hakuri ta koma gida inaso kai ma yanzu naji ta bakinka kan abunda ke faruwa a tsakaninka da ita.”
Shuru yayi yana mamakin maganar Halisa ta kawo shi qara gurin mahaifiyarsa akan wani dalili me yay mata mai zafi da zata kawo kararsa gaban mahaifiyarsa, Hajia ganin yay shiru yasa tace”Kai nake saurare.”
Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace.”Hajia a zahirin gaskiya ni ban san abinda nayi mata wanda ya sanya har ta kawo miki ka’ra ta wannan shine dalilin da yasa kika ga nayi shuru ina mamakin maganar saboda d’azu da safe lafiya lau muka rabu na tafi kasuwa.