MADADI Page 91 to 100

Hajia tace”To ita kuma tace min akan tace ka mayar da Najaatu gidanka ne kake jin haushinta wanda dalilin wannan maganar da tayi maka yasa kake gaba da ita sannan baka siya mata abin futar suna ba.”
Shuru yay bakinsa ya mutu lallai Halisa bata da kirki shi zata tonawa asiri baiyi tsammanin zata iya kawo kararsa akan wannan dalilin ba, tabbas daya san abinda zata aikata kenan toda ya tsaya ya saurareta sun rabu lafiya, duk sanda zai tunu da furucinta a kan Najaatu sai yaji wani irin mugun haushinta ya rufeshi shiyasa ya watsar da lamarinta ya’ki siya mata komai ya kuma ki bata kudi duk da yasan zata bukace su domin tayi hidimar haihuwar Zainab dasu.
Hajia ta cigaba da cewa”Yanzu meye laifin Najaatu da har zaka dinga gudunta haba kai kuwa! wallahi mu duk mun dauka kana da qudirin mayar da ita dakinta dan ganin irin hidimar da kake mata ashe kai ba haka abun yake a zuciyarka ba, menene abun gudu a tare da yarinyar kayi hakuri ka tausaya mata ita da d’anta ka mayar da ita dakinta komai ya wuce ni a matsayina na wacce ta haifeka nake baka umarni akan haka Najaatu matar arziki ce sannan dukkanin abunda ya faru tsakaninka da ita qaddara ce da rabon wannan yaro da take goye dashi, dukkaninmu idan yarinyar nan ta koma dakinta sai munfi farin ciki akan ta sake wani auran…….Sannan sai magana akan Halisa inaso itama kayi mata abunda ya dace duk da ba itace ta haihu ba yana da kyau kayi mata wani abun wanda zai faranta zuciyarta haka akasan adalin namiji.”
Abbah Abbas kasa cewa komai yayi dan gabadaya Hajia ta gama kashe masa jikinsa da maganganunta tabbas bashi da yanda zaiyi ya bijirewa umarninta dole ne ya mayar da Najaatu dakinta tinda ta riga ta umarce shi….Hularsa ya dauka yasa yace.”Shikkenan Hajia tunda kin bukaci da ayi hakan za’ayi insha Allah ina rokon Allah yasa hakan shine alkairi maganar Halisa kuma idan na koma gida zan zauna da ita insha Allah.
Hajia tayi murmushin jin dadi tace”To nagode sosai da wannan alfarmar da kayi min baka bijirewa umarnina ba naji dadi kwarai da gaske ina maka fatan alkairi tare da samu farin ciki har karshen rayuwarka.
Ya amsa da ameen ya rabbi hajia babu wani abu da zaki nema a gurina na kasa yi miki saboda nasan kome na zama a duniya ta dalilinki ne da tasirin aduoin da kike min saboda haka insha Allah Najaatu zata koma dakinta kamar yanda kika bukata amma inaso yaron yay wayo tukkuna sai ayi maganar daurin aure.”
Hajia tayi shuru tana nazarin maganarsa Eh hakan kamar shine maslaha amma kamar za’a ja dogon lokaci….Tace.”To shikkenan hakan yayi Allah ya nuna mana lokacin da zata yaye yaron sai a d’aura auren ko kuma dai za’a daura auran kawai sai tayi zamanta a gida idan ta yaye yaron sai ta tare.”
Yace.”A’a bari dai ta yaye shi tukkuna ina ganin hakan kamar sai yafi.” Baya so taje ta dauki ciki ga k’aramin goyo yaron zai iya lalacewa shiyasa yace haka….To itama hajian ta fahimci abinda yake nufi sai tace”To Allah ya nuna mana….Miqewa yay tare yi mata sallama, a sauka lafiya tayi masa tare da bada sakon gaisuwarta gasu Saddaqa……..lokacin daya shiga gidan samun Halisa yay a qame a kujera tayi kici kici da fuska, tsaf ta shirya masa da duk wani tashin hankalin da zai shigo dashi
Ganinta cikin shirin ko ta kwana yasa ya sassauta fuskarsa domin baya neman wani bala’i yaji ma da wanda ya shigo dashi gidan, sai kawai ya shige dakinsa ba tare da ya tanka mata ba.
K’wafa tayi tana girgiza kanta ta dauka zai shigo da bala’i sai taga akasin hakan tayi murmushi cikin zuciyarta tace”Ashe abun rainin hankali ne da samun sake to daga yanzu idan kayi min abunda be gamsar dani ba xan tunkari mahaifiyarka na fada mata magana ta qare…’Kin tashi tayi tabi bayansa har ya gama abunda yake ya fito cikin jallabiya ruwan toka….Kusa da ita ya zauna yana kallonta yace.” Abunda kikayi kin kyauta kenan? abunda ba kiyi da kuruciya ba shine yanzu saboda shashanci zakiyi gabadaya kishi ya rufe miki ido kin manta ke irin abubuwan da nayi miki a baya sabida kawai kinga kayan haihuwar Zainab kin tashi hankalinki harda zuwa ki fad’awa hajia laifina bana muamular arzki dake saboda kince na mayar da Najaatu naqi shine nake gaba dake ko? Kallonsa tayi tace”Ai ba qarya nayi ba baka kulani baka cin abincina” Yace “cikin nida dake waye gaba da wani? wa ya cancanci ya d’urkusuwa dan uwansa”.
Murmushi tayi tace” Abinda yake faruwa kenan tsakanin ma’aurata wai dan Allah Abban mufida me yasa kuke da iko ne sau nawa ina maka magana ina girki ina ajiye maka baka ko saurarata ballantana kaci abincina akan kawai na baka shawarar arziki ashe kai so kake nai ta binka ina baka hakuri alhalin ni na nayi maka alkairi ka mayar min da sharri wallahi banga laifin da nayi maka ba wanda zai sanya nayi ta baka hakuri ba.”
Yace.”Ya isa haka! maganar dawo da Najaatu ce dai duk ta janyo wannan abu to sai hankalinki ya kwanta hajia ta bani umarni na dawo da ita shikkenan magana sai ta qare.Tace”Abbahn mufida kenan koda hajia bata baka umarni ba to kai zaka bawa kanka umarni dan haka kamar yanda kace a bar maganar an barta kai da Najaatun ina muku fatan alkairi tare da zaman lafiya mai d’orewa…..Cikin ransa ya amsa da ameen kafin gurin yay shuru na minti uku…Gyaran murya yay yace.”Yanzu me kike bukata.” Tace”Yanzu kuma lokaci ya qure ai gobe suna mai zanyi da kudi.”
Yace duk da haka hakkinki ne ai ko bayan suna zaki iya amfani dasu ta wata hanyar sabida haka kema zan sa miki kudi a account d’inki shikkenan na fita kada ki sake zuwa kice ina tauye miki hakkinki dan ni duk neman da nake akan iyalina nake banga abunda zai hanani na faranta muku rai ba.”
Halisa akayi murmushi ana wani girgiza jiki “To nagode sosai Allah ya qara budi na alkairi.” Amsawa yay da amin ya miqe tare da fad’in zai shiga gurin Zainab ya dubata.
Ba tace masa komai ba har ya fita daga dakin, lallai zuwa gurin hajia yayi mata amfani tunda gashi nan ya zauna suna maganar arziki babu hayaniyar daya saba.
Zainab maijego tayi shar shar da ita, mai kitso da lalle (‘kunshi) har gida tazo tayi mata kitson attaccement mai uban yawa sannan akayi mata jan lalle da baki gabadaya faratan ta tasa musu (jan farce) sai kace wata inyamura dan gabadaya kammanin ta sun sanja……Tana zaune ita da masu taya ta zaman jego sai hira suke tare da shirye shiryen yanda shagalin bikin suna zai kasance dan har sun biya mai d’an Asharrale (DJ) kudi zai zo da yamma ya baje kolinsa, abunda sukeyi tamkar ba ‘Ya’yan shehin malami ba.
Ganin ya shigo dakin yasa suka shiga gaisheshi suka fita daga dakin da sauri.
Zama yay kusa da ita yana kallonta cike da mamaki yace.”Wannan wane irin kitso ne akanki irin na arna shin nauyin abinda akayi miki kitson dashi baya damunki sannan kin saka wani abu a faratanki ko kyau ba suyi miki ba, dan Allah idan za kuyi kwalliya kusan irin wacce zaku dinga yi.
Zainab jikinta yay sanyi jin yanda ya gwale mata kwalliyarta sam bata dauka zai ga rashin kyawunta ba kasancewar ta sanshi shi ma’abocin san ado ne.
A sanyaye tace”Ai sabida nasan bana sallah yasa nayi kitson attachment sannan nayi ado da jan farce.
Yace.”Duk da haka zaki gayyato shedanu jikinki wannan kwalliyar da kuke ita kesa sanyawa abubuwa da yawa su faru daku ina laifi ma da kikayi ‘kunshi amma meye na rufe farcenki da wani jan abu.”