MADADI Page 91 to 100

Zainab tayi shuru yace.”Gobe da safe ki kankareshi dan baiyi miki kyau ba sannan wannan uban gashin dokin da kika sa a kanki ana gama taron suna ki kwance shi bazan lamunci shigowar shed’anu gidana ba. Tace”Abbah Mufida kitson nan ansha wuya kafin ayi kuma dubu kusan ashirin na biya akayi min ya za’ayi kace na tsefe!
Yace.”Babu ruwana da kudin da kika biya ni dai umarni na baki.” Zainab ta shiga halin damuwa, babyn dake kwance a kusa da ita ya dauka ya dubata sosai ya ajiye ta tare da miqewa hanyar futa ya nufa….Tace.”Abbah Mufida dama ina so na fad’a maka cewar su aunt Hauwa sun gayyato mai DJ zai zo yay mana da yamma.”
Yace.”Waye me DJ. “? Kai tsaye tace” Ina nufin mai Dan Asharrale inaso ka bani kudin li…… katse ta yay da sauri yace”A gidan nawa za’a buga min DJ.”? Dawo yay ya tsaya a kanta ya wani tamke fuska yace”Wai shin Zainab kin manta daga inda kika fito ne na lura gabadaya dake da ‘yan uwanki duk shagalallu ne kun fito daga tsatso mai kyau amma kuna neman ku shagala wannan abubuwan da kuke na tabbata Ya sheik bai sani ba to ni da kaina zan sanar masa dan ni ba irin shashashan mazan da ‘yan uwanki ke aura bane in banda rashin hankali har ki dube ni kice zaki kawo min ‘Dan Asharrale yazo yay me? To kada ki kuskura wallahi tun wuri su da suka gayyoto shi su dakatar dashi dan mutukar yazo min gida sai na daureshi sannan kema na baki mamaki.” Zainab ta dinga kuka tana bashi hakuri tsabar ‘bacin rai yasa ko sauraranta baiyi ba ya kada kansa ya fita da dakin yana mamakin al’amarin ashe da yarinyar nan bata fad’a masa ba da sai dai ya samu labarin zuwan Dan Asharrale gidansa. da kuwa ya dauki tsatstsauran mataki a kanta dan ba zata kawo masa bidia a gida ba.
Washe gari ranar suna yarinya taci sunan kakarta Hajia Zainab (Abu) sai ya kasance Yarinyar ta amsa sunan mamanta da kakarta amma dai shi uban ‘yar sunan babarsa yasa kai tsaye kuma yace a dinga kiranta da Ummi Hajia taji dadin samun takawara ta dinga murna tare da adduar Allah ya raya mai sunanta……….Bangaran Najaatu kuwa da tayi alkawari kan cewa babu inda za taje, sai kuma daga baya tayi wani tunani tayi sauri tayi shiri na mussaman ado da kwalliya tayi mai k’ayatarwa ta fito falo tana zabga kamshi turarruka masu kamshi da daukar hankali…
Nan ta samu Ya Ramlatu da wasu daga cikin Family din Hajia suna zaune ta gaisa dasu a mutunce! Ta kalli Ramlatu da fad’in.” Ba yanzu zamu tafi bane.”? Ya Ramlatu tace”ko kawai kibi hajia Rabi ku tafi kada rana tayi ni zan jira zuwansu Hajia Rakiya sai mu had’u gabadayanmu mu biyo bayanku.
Tace”To shikkenan, sama ta hau tayi sallama da hajia ta sauko Ya Ramlatu tace” Daddy tunda yay bacci a bayana to ki barshi kawai na tawo dashi.
Tace”Kada fa ya tashi yayi miki rigima irin na jiya.
Dariya ta d’anyi tace”Ba zai tashi ba insha Allah ai su Hajia Rakiyan suna hanya muma ba zamu dade ba zamu biyo bayanku.
Tace to shikkenan sai kin tawo.
Naja’atu tana sane ta yafa qaramin mayafi mara sirri ga yanayin dinki jikinta riga da siket sun matseta swiss les ne mai tsada amma tasa anyi mata matsatstsan d’inki! tana sane tasa kayan saboda tasan baya son suyi irin shigar su fita da ita..
Taji dadin ganin dukk motocinsa a harabar gidan da alama bai futa ba, kai tsaye bangaran maijego suka nufa…..’Yan uwanta ne duk a gurin suka gaisa a tsaitsaye suka wuce ciki.
Zainab tayi kyau har ta gaji kana ganinta kaga matar Alhaji gold yaji a ko’ina ga wata uwar shadda tasa wacce taji uban surfani irin na manyan mata…Najaatu kallo daya tayi mata ta dauke kanta, kishi ne yake taso mata tana danneshi…To itama Zainab din nata bangaran ganin zahirin Najaatun ya firgitata jikinta yay sanyi dan bata ta’ba tsammanin cika da kasaitarta ya kai hakaba ashe cikakkiyar macace abar alfaharin ko wane da namiji lallai hijabi ba karamin sururta mace yake ba.
Ta dinga satar kallon Najaatun tana jin wata shakkarta gabad’aya bata so ta had’u da mijinta dan kada ya ‘kyasa (Maman Hanan kinga mutuniyar ki ko ???? sai kace tsinken sakace sai iyayin tsiya) Najaatu na hankalce da irin kallon da take mata sai kawai ta miqe da fad’n “Hajia bari na shiga gurin Aunty Halisa mu gaisa.
Hajia Rabi tace” To shikkenan nima zan shigo yanzu insha Allah.” Najaatu ta juya tana wata iyar tafiya ta taqama! Zainab kasa dauke idonta tayi daga kanta har ta fita daga dakin.
Da sallama a bakinta ta tura kofar falon ta shiga, Abbah Abbas na tsaye a tsakiyar falon yana magana da Saddiqa Halisa kuma na zaune a kan kujera tayi ado daidai misali Mussadiq da Mufida na kusa da ita a zaune.
Ganin shigowarta yasa yaran suka ruga a guje suka rungumeta suna murna…Halisa na murmushi tace”Najaatu ke kika fara zuwa kenan sannu da zuwa karaso ki zauna.
A nutse ta riqe hannun Mussadiq suka karasa falon ta samu guri ta zauna a nutse ta kalleshi yana tsaye a inda yake yana mata wani irin kallo mai kama da harara ita tasan ko kallon menene sai ta basar tace”Abbah ina kwana? ‘kin amsawa yay ya kalli Saddiqa da fad’in ta tashi maza taje gurin Zainab tace ta duba masa gilas d’insa a dakinta, Saddiqa tayi saurin miqewa domin tafiya aiken da yayi mata, Najaatu ba tayi zuciya ba ta sake gaishe shi, a dakile ya amsa ya bar gurin… murmushi kawai tayi ta juya suka cigaba da magana da Halisa……
*Littafin na kudi ne…..!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abun yake Vip gruop#600 normal group #300 account….. 0542382124…Binta umar gtbabk…Idan kati zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number.
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
79******Halisa na murmushi tace” Ya kuma naganki a haka ina kika baro maigidan nawa.”? Tace”Yana goye a bayan Yaya Ramlatu lokacin da zamu tawo yana bacci shine tace na kyaleshi kawai ta tawo dashi.” Halisa tace” Ayya amma kin shiga gurin maijegon ko.”? “Eh Hajia Rabi ma can na baro ta.” Shuru falon yayi kowa yana tunani a cikin ransa……Kamshin turaransa ne ya sanya dukkaninsu suka dago kai suna kallonsa, Najaatu kallon sharia kawai tayi masa tayi kasa da kanta tana jin wani irin yanayi a jikinta, a duk lokacin da zata kalleshi sai sonsa da kaunarsa sun sake karuwa a cikin zuciyarta, Abbah Abbas kwata kwata baya tsufa kullum kara masa kuruciya ake babu wanda zai kalleshi yace yayi shekara hamsin a duniya saboda shi mutum ne dan gayu mai kula da kansa, Yanzu ma yayi ado cikin wani had’addan filtex irin na maza dark blue abinka da farin mutum sai yayi masa wani irin kyau, hula mai farin zanen zare yay amfani da ita, kafarsa sanye da takalmi sau ciki baki sai shaninig yake, farin gilashin da yake sakaye a idonsa yayi masa masifar kyau, Najaatu ta dinga jin wani irin sanyi na ziyartar jikinta sha’awarsa ce take taso mata a jikinta sai ta shiga tunawa da irin zazzafar soyayyar da ya dinga nuna mata a lokacin da suke tare…….Muryarsa taji yana magana…”Yau ma kin bar yaron nan a gida ko ashe ke ba’a isa a fad’a miki magana guda kiji ba? yanzu meye amfanin saka wannan mayafin na jikinki da kin sani kin yar dashi a hanya dan bashi da wani amfani tunda gashinan a zahiri komai na jikinki ana gani.