MADADI Page 91 to 100

Shuru tayi ta kasa magana ba wai dan bata da abinda cewa ba kawai tana ganin kamar shurun shi yafi amfani saboda gudun kada ta fada masa wata maganar yace tayi masa rashin kunya.
Halisa tace” Ni sai nake ganin ai ba wani abu bane dan ta bar yaron a gurin Yaya Ramlatu tunda yanzu zasu zo maganar hijabi kuma ka ajiyeshi a gefe yau daya dan tasa mayafi ai ba laifi bane tunda bata da nauyin kowa a kanta kuma ni wallahi banga abunda mayafinta ya nuna ba. tana yar dariya ta karashe maganar.
Yace.” Ni na gani ai tunda ke baki gani ba, sannan ni nasan tana da wata munufa ta yafa mayafin tunda keda ita duk kun san bana son irin wannan mayafan marasa sirri saboda haka idan zaku tafi ki kar’bi hijabi gurin Halisa ki suturta jikinki baki burgeni ba idan dani kikayi…….Halisa tace”Ikon Allah shikkenan sai tayi kwalliya dan kai kad’ai bazawara ce fa kuma kowa yasan zawarawa da ‘yan mata gurin ado da kwalliya me zai sanya ka damu kanka…..Yace.”Ai shine abinda nake so ki fahinta ta bud’e tsaraicinta ne dan ni ko wani a waje ya gani yaji sha’awa to ni duk irin wannan basa burgeni.”
Jin abinda yake cewa ne yasa tace”Haba Abbah yanzu dan Allah ina tsaraici anan.”? Tafada tana cire mayafin jikinta tare da gyara zamanta a kan kujerar. Saurin dauke kansa yay sakamakon ganin tudun nonowanta da suka fito ta saman riga…..Aunty Halisa tace”To nima dai haka na gani wallahi.” Najaatu ta cigaba da cewa”Wallahi ni banyi kwalliyata dan kowa ba dan kaina nayi kuma Aunty Halisa ni bazan fitar da tsaraicina saboda na samu mijin aure ba saboda nasan ko yanzu na bukaci aure zanyi tunda ni nasan kaina ba k’aramar mace bace.”
Halisa ta dinga dariya tana kallonsa yana tsaye yana kallonsu, kowa dai yay zagi a kasuwa yasan da wanda yake, shuru kawai yay musu ya zauna kan kujera mai cin mutum daya, agogon hannunsa ya duba, ya kalli Mussadiq dake fama da game yace”Jeka gurun Zainab kace tazo amma tazo da baby Ummi.”
Yaron ya ajiye game din da sauri ya tafi aiken da akai masa.
Abbah shuru yay yana jin Halisa na fad’in “Najaatu kin birgeni wallahi ai dama nace ke ba k’aramar mace bace koda baki sa mayafi ba ya kasance kullum a cikin hijabi kike na tabbata ba zaki rasa miji ba haba ai ido ba mudu ba yasan ‘kima.”
Shiru yay bai tanka ba dan ya lura Halisa naso ta tona masa asiri a gurin yarinyar shiyasa yaja bakinsa yay shuru ya shiga girgiza kafafunsa….Halisa kallonsa take a fakaice tana ‘boye dariyarta ita wallahi idan yana muzurai a kan rashin gaskiya dariya yake bata wai shi lallai ba zai fito fili ya nuna cewar ya damu da yarinyar ba alhalin duk gashinan ya nuna alama a zahiri kowa ya gani.
Zainab ta shigo falon rugume da ‘yarta ganin Halisa da Najaatu na hira cikin fahimtar juna yasa taji haushin hakan, dauke kanta tayi ta nufi gurun mijinta….Baby Ummi ya kar’ba daga hannuta ya rungumeta a gefan hannunsa na hagu sai ya janyo zainab din ya d’ora a cinyarsa, ya rike kungunta da hannunsa na dama wayarsa ya bata yace tayi musu hoto…….Wannan al’amari ya duguzunma zuciyar Najaatu da Halisa ba kamar najaatu da taji gurin na juyawa da ita, Ita kuwa Halisa d’aga murya tayi tace”Me yasa ba kaje can gurinta kunyi hoton ba ai ina ganin kamar hakan sai yafi armashi.”
Yace.”Akwai jamaa a gurun ne ko banda ikon nayi abinda nake so a inda na gada dama.” Ta’be bakinta tayi tace”Aa kayi komai babu damuwa ai.”
Ya kalli su Saddiqa da fad’in su taso suzo gurinsa, yaran suka kewaye shi Zainab na zaune daram! a cinyarsa tana ta daukarsu a hoto farin ciki kamar ya kasheta hakika tayi farin ciki da yanda ya nuna musu cewa ita mai muhimanci ce a rayuwarsa, in da shi kuma anasa bangaran da biyu yake haka duk dan ya cuzguna musu, aikuwa ya hango tsantsar kishi da tashin hankali a idanun Najaatu dan har ja idanunta sukayi saboda tsabar bacin rai da takaici……Sai da suka gama dauke dauke hotonsu sannan yazo inda suke zaune da yake duguwar kujera ce sai ya shiga tsakaninsu, Najaatu kamar ta miqe ta bar gurin haka taji sai dai ta daure ta matsa gefe saboda jin yanda ya takureta….Baby Ummi ya kar’ba ya riqe yasa su Saddiqa suka shigo kowa ya tsaya, sannan ya umarci Zainab din ta daukesu, hakan be mata ciwo ba saboda tasan ita ya fara nunawa muhimanci…..Zainab tayi musu kusan biyar ta miqa masa wayar, tare da fad’in “Zata koma gurin ‘yan uwanta! Babyn ya miqa mata tare da fatan a tashi taro lafiya…..Ta ‘karbi ‘yarta ta tafi ba tare da ta kula kowa a gurin ba…..Shima tana fita ya miqe daga tsakiyarsu ya kama hanyar futa, babu wanda ya kulashi sai yaransa sune sukayi masa adawo lafiya.
Ya amsa cike da walwala da farin ciki yasan yau da Halisa Da Najaatu dukkaninsu ba zasu yini cikin farin ciki ba, wato harshi zasu sa a gaba sunawa dariya sun mayar dashi sakarai shiyasa yay musu haka. bayan fitarsa Najaatu mamaki take sosai da yanda Halisa tayi sanyi yanzu gabadaya ta mayar da rayuwa ba wani abuba, idan da lokacin baya ne ai bai isa yayi mata irin wannan rashin kyautawa a falonta ba gaskiya kamar da akwai cin fuska a ciki sai taga kamar ma ita ta fita jin haushin al’amarin amma dai yanda ta dauke kanta daga kan abunda yayi yasa taji ta burgeta mutuka
Taron sunan Zainab yayi kyau ya kuma k’ayatar anci ansha maijego ta fito sosai dan sai da tayi shigar kaya kala goma cikinsu duk babu na yarwa abunda yay musu cikas kawai rashin Dan Asharrale amma dai duk da haka ba suyi bikin Lami ba sai da suka saka (Mp) mai kid’an tsiya suka dinga jin wakokin *Gwanja* suna cashewa sai rawa suke suna murguda mazaunai maijego dadi ya isheta ta dinga yi musu liki…..Gabadaya d’abi’un ‘yan uwan Zainab na banza ne ‘ya’yan malam ne amma kuma sunqi halin malam rashin arziki kawai suke yanda ransu yake so.
*BAYAN SATI BIYU*
Al’amura suna ta gudanawa yanda ya kamata, ta bangaran Najaatu ta bude wuta sosai da ado da kwalliya da ta daidaici lokacin zuwansa gidan zata fito ta zauna kan kujera tana baza kamshi tururuka…Ita kanta hajia sai da taji dad’in salon da yarinyar ta tsiro dashi tasan tabbas yin hakan zai sake janyo hankalinsa kanta, aikuwa dai a tsakankanin kwanakin daurewa kawai yake yi amma yarinyar na mutukar galabaitar da zuciyarsa dan dai kawai mutum ne mai dauriya da dauke kansa a kan abu shiyasa baya bari kowa ya gane halin da yake ciki, duk sanda zai shiga gidan yakan sakaye idanunsa da gilashi gudun kada kwayoyin idonsa su nuna abinda yake zuciyarsa…..Najaatu halin ko’in kulan da yake nuna mata bai dameta ba kwalliya da sauran abubuwa ba zata daina ba tunda ta fahimci suna tasiri a tare dashi….. Da yake tana da yawan gashi mai kitso har gida take zuwa ta ‘bata lokaci gurin tsantsara mata kunshi kuwa da ya goge zatayi wani……..Al’amarin daya sanya shi tunanin sanja shawara akan wacce sukayi da hajia yana ganin kamar d’aura auran a kurkusa shine kwanciyar hankalinsa idan yace zai cigaba da zama tsayin watanni yana ganin yarinyar hankalinsa na tashi to babu shakka zai iya shiga halin ni ‘yasu dalilin daya sa ya yanke shawarar tunkarar abokinsa da maganar…..Abbah Magaji yace”To tunda kana ganin hakan yayi maka shikkenan sai kawai ka sanya a ranar da kakeso a daura auran.” Yace.”Yau insha Allah idan na shiga unguwar zan zauna da Malam da Alhaji a kan maganar.” Abbah Magaji yace.”To shikkenan Allah ya sanya alkairi yasa anyi kenan.” Ya amsa da ameen ameen.