MADADI 1-END

MADADI Page 91 to 100

Najaatu duk wani abu da ake bata da labarinsa dan tunda aka tsayar da maganar daurin aure shi bai kirata ya fada mata ba kuma har yanzu babu wata kyakkyawar alaka a tsakaninsu, tana dai jin maganar sama sama a gurun hajia da Yaya Ramlatu suma kuma babu wacce tace mata komai a kan al’amarin…….Ranar Lahadi da safe yazo gidan, Hajia na sama tana sallar walha Yaya Ramlatu da Hajia Rabi sun tafi asibiti duba Salim ashe tun ranar da Naburago ya watsa masa kudin auransa ya kwanta ciwo kamar ba zaiyi rai ba, sai da aka kwantar dashi a asibiti sannan Sakina ta aiko aka sanar da mahaifiyarsa shine fa Alhaji yace maza maza suje su duba jikin nasa ai hannunka baya ru’bewa ka yanke ka yar……..Tana daki tana gyara jakar kayanta yay sallama a dakin, gabanta ya fadi dajin miryarsa, daidaita nutsuwarta tayi ta dan juya tana amsawa …..Idonsa kuri kan gashinta wanda akayi mata wani irin kitso mai kyau jelolin gashin sun dan sauka bayanta, Najaatu nada gashi daidai gwargwado gashi baki mai daukar ido……Ganin yana mata wani irin kallo ne yasa ta lalubi dankwalinta ta daura, a sanyaye tace”Abbah sannu da zuwa.”

Da sassauci a tare dashi ya amsa tare da neman guri ya zauna yana kallonta, gaishe tayi ta dan gyara zamanta tana jira taji da abinda yazo dashi.

Gyaran mirya yay as’usul yace.”Naji gidan shuru tunda na shigo banji motsin mutum ba ina fata dai lafiya.”? Tace”Wallahi tun safe Alhaji da Hajia Rabi yaya 

Ramlatu suka tafi asibitin gadon kaya wai ashe Salim ne bai da lafiya yana can a kwance, ita kuma hajia na sama tana sallar walha.” shuru yay na minti biyu kafin yace.”Tun yaushe ne baida lafiyar.”? Tace”Wallahi ban sani ba jiya Matar babansa ta aiko aka fad’a.” 

Allah ya sawwake.” yafada yana me tsurawa yatsun hannunta ido….Dakin yay shuru kowa na tunani, Abbah tunanin ta inda zai fara yake, da kyar ya iya kiran sunanta.

Ta daga kanta ta kalleshi kafin ta mayar dashi kasa 

“Kina da labarin maganar daurin auramu ranar jumaa mai zuwa kuwa.”? Gabanta ya fadi tayi saurin kallonsa, girarsa ya daga mata ya lumshe idonsa, a hankali yace.” Naso na bari yaronki ya kara kwari amma na kasa saboda ni kadai nasan yanda nake jinki a cikin zuciyata, Halisa tace ba zan ta’ba samun nutsuwa ba sai dake sai nake kokarin k’aryata maganarta saboda ina ganin ke baki isa ki tauyemin rayuwata ta kowane fanni ba, ashe so ba haka yake ba, dalilin yin hakan da nayi yasa ya mayar dani sakarai mara nutsuwa gami da saninan muhumacinsa, hakika a cikin ‘yan kwanakin nan ni kadai nasan irin azabtuwar da nake a kanki Najaatu zan sake auranki a karo na biyu inaso ki bani hankalinki da nutsuwarki da dukkanin kulawarki bana so a yanzu dani dake muyi auran Madadi inaso muyi aure naso da kauna wanda zamu rayu a cikinsa cikin farin ciki da walwala har karshen rayuwarmu.”

Wani irin farin ciki ya ciki mata zuciyarta hawayen farin ciki ya shiga sauka akan kumatunta, mirya na rawa tace”Abbah ka daina kokwanto akaina a yanzu zan aureka na zauna da kai tsakani na da Allah, Wallahi ban ta’ba kaunar wani namiji ba kamar ka, Abbah bani da za’bi sai naka bani da bakin godiya a gareka kayi min dukkanin sadaukarwa a rayuwata inaso yau na fad’a maka da bakina cewar ina sonka wanda ban san iya adadinsa ba, ina rokonka daka yafe min abubuwan da suka faru a baya kuruciya ce da kuma qaddara yanzu zan zauna zaman aure da kai tsakani da Allah da kuma so da kauna insha Allah.”

Ya dinga wani murmushin farin ciki da jin dadi yana wani lumshe idanunsa a kanta, mirmushi tayi ta sunkuyar da kanta k’asa tana wasa da hannayenta yace.”Nayi farin cikin jin wannan magana taki Najaatu ashe yanzu ina da babban matsayi a cikin zuciyarki ban sani ba, a gaskiya dole wannan karon nayi shiri mai kyau inaso na nuna miki ni daban nake da sauran maza sai kin kasance a matsayin matata zaki gazgata hakan.” Yakare maganar yana jifanta da wani shu’umin kallo…Kunya ce ta rufe ta da sauri ta rufe fuskarta tana dariya.

*ALHAMDULLILAHI FAD’AN MASOYA HUTU NE INJI BAHAUSHE*

Salim zazza’bi typoid ne yaci karfinsa inda har ya ta’ba masa hanjin jikinsa,wannan bayanin likitan dake kula dashi yayiwa Alhaji hankalinsa ya tashi Yaya Ramlatu kuwa kuka kawai take tana fad’in ”Yanzu wata da wattani d’anta yana kwance yana ciwo a kasa fada mata wato da sai dai taji labarin mutuwarsa kenan, babu shakka abunda Sakina tayi mata bata kyauta ba

Ita dai Sakina hakuri kawai take bata dan gabadayan su Hankalinsu ya tashi jin cewar hanjin cikinsa ya ‘bule dole sai anyi masa aiki.

Abbah Abbas ma da yazo dubashi sai da hankalinsa ya tashi, a take yasa hannu ya kuma biya zunzurutun kud’aden da asibitin ke bukata yace maza a shiga dashi teater , Allah sarki Yaya Ramlatu kuka kawai take dan gani take tamkar gawarsa za’a fito mata da ita, sai dai kuma ba a nan take ita cuta ba mutuwa bace mai lafiya ma yana iya mutuwa ya bar wanda yake da shekara goma yana jinya…….Lafiya lau aka fito da Salim anyi aiki cikin nasara yanzu abinda yay saura kula da shan magani akan ‘ka’ida.

*****

Alhaji Aminu Dan jarida da kyar ya samu gurin zama bayan fitowarsu daga prison sai kowa ya gudunsu dalilin daya sa kenan ya harhada ‘yan kudaden da suka rage masa ya gudu k’yauyen zaria shida iyalinsa ya samu ya siyi wani lalataccen gida, sauran kudin suka siyi kayan abinci….Mommy ta fara sanar sai da gwanjo a cikin kyauyen sai ta shiga cikin gari ta siyo tazo ta baza a kofar gidan jama’ar garin na siya da wannan sanaa suke rufawa kansu asiri. A lokacin 

Munira ta dade da haihuwa inda ta haifi Da namiji a hannun kanwar Momynta Laila…….’Kaskanci da wulakanci babu irin wanda Munira bata gani ba, taci wuya sosai wanda sai da ta kai ta kawo ta daina fitowa waje dan da ta fito za’a soma yi mata waka mai cikin shega babanta karto d’an uwanta ‘barawo wasu yaran ma har jifanta suke wannan dalilin yasa take zama a gida taci kukanta ta koshi Lailah ta ta cigaba da azabtar da ita….Tunda ta samu labarin dawowar iyayenta ta gudu ta koma gurinsu, dan gwara tayi rayuwa a cikin kyauyen da suke a kan azabar da Laila take gana mata.

*RANAR JUMA’A*

Ranar aka daura auran Abbah Abbas da Najaatu a karo na biyu daurin auran yayi albarka sosai dan ya samu halartar manya manyan mutane 

daga bangaran Alhaji Abbas mai girma governor dashi da mukarrabansa ma sun samu hallatar daurin auran Abbah Abbas ranar kasa rufe bakinsa yay sai murmushi yake yana gaisawa da jamaa cikin walwala da farin ciki………Najaatu ta sake zama matarsa a karo na biyu ai dole ya nunawa Ubangiji farin cikinsa..

*’Kawata kada kiyi wasa da wanke bakin ki domun ana saurin gane tsabtar mutum ta ha’koransa…..Akwai damuwa ace wai idan kikayi brush da safe ba zaki sakeyin wani ba sai wata safiyar???? to idan kuna marking lov da oga yana muradin ya sha bakinki yaji wari ko datti abinci kina tunanin zai sake marmarin kusantar bakin ki????????‍♀️ tsotsar bakin juna gurin mu’amula ta aure na qarawa ma’aurata amarshi da son kasantuwa da junansu, duk wata macen da mijinta baya had’a baki da ita ta bunkici kanta,????rashin gyara da kula da kanki zai janyo miki babbar matsala k’awata…….Idan kinyi bursh da asubah da safe kafin ki karya ki sake yin wani, da daddare kafin ki kwanta kiyi wani ki dauki kaninfari guda biyu kisa a bakinki kina tsotsa, kaninfari yana da mutukar sirri a tare dake kada kiyi wasa dayin amfanin dashi, dan Allah kada kiyi saken da zai sanya mijinki ya dinga gudun had’a baki dake????*

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button