71 Yaya Ramlatu ce tayi dubarar d'auko babyn dake ta tsanyara kuka alamu sun nuna cewar yaron yana da qoshin lafiya dan tunda ya sauka ya cika musu kunne da kuka.........Hajia Rabi tace"Namiji ne ko mace."? Yaya Ramaltu na murmushi tana sake riqe yaron a hannunta tace."Namiji ne gashinan tubarkallah masha Allah." Hajia ta rike Naja'atu sosai a jikinta tana fad'in "To Allah ya raya shi tafarkin addinin musulunci." Suka amsa da amin amin........Yaya Ramlatu ta nad'e yaron a towel ta ajiyeshi kan gado da sauri tazo ta taimakawa hajia Rabi gurin rirriqe Naja'atun dake ta wani irin nishi!!! 'Yan dabaru suka shiga yi mata domin mahaifa ta fad'o amma abun yaci tura Hajia ganin lokaci yana ja mahaifar taqi ta fad'o sai kawai ta yanke shawara akan su tafi asibiti zaifi kwanciyar hankali......... Hankali a tashe Ramlatu ta bude wardrobe cikin sauri ta dauko riga da zani na atampa, hajian ta kar'ba tana kokarin sanya mata Allah sarki Naja'atu Idan kuka ga Naja'atu a lokacin sai kun tausaya mata dan tayi masifar galabaita kokarin kwanciya ma takeyi hajia na hana ta.........Hajia Rabi ce ta shigo d'akin da sauri ta kalli Ramlatu da fadin " Taimaka mu kamata yanzu nasa 'Dan Azimi ya fito da mota." Sai suka fara kokarin miqar da ita, tana lanjarewa kuka take da fad'in su yafe mata mutuwa za tayi, lokacin da take wannan maganar gabad'ayansu jikinsu mutuwa yay Hajia kuwa da yake mai saurin kuka ce tuni hawaye sun 'balle mata. Ya Ramlatu tace"Ba zaki mutu ba Naja'atu insha Allah zakiyi dogon zango a duniya kiyi hakuri kinji ko ita haihuwa haka take da sammatsi muna zuwa asibiti zasu taimaka miki." Girgiza kanta kawai take tana karanto sunayen Allah dari ba d'aya a zuciyarta. Hajia tace"Yana da kyau aje a sanar da iyayenta halin da ake ciki." Ya Ramlatu tace"Hakane bari nasa Dan Azimi ya buga musu kofa." Naja'atu riqe hannunta tayi tana girgiza mata kai magana takeso tayi amma bakinta yayi nauyi wani irin ciwo mararta yake mata, Hajia Rabi ta riqeta a jikinta tana tofa mata Addua duk sun rasa yanda zasuyi ita ba miji ba ballantana a kirasa yazo ya dauketa yasa a mota........Cigaba sukayi dayi mata taimako irin na gida, cikin ikon Allah ta dinga wani irin yunkuri kamar wacce zata sake sabuwar haihuwa mahaifar ce ta fad'o kafin wani uban jini ya biyo bayanta. Gabad'ayansu suka shiga godewa Allah dan ganin yanda ya gajarta musu wahala basu sha wahalar zuwa asibiti ba amma a zahirin gaskiya haihuwar tazo da tangard'a! amma dai tunda Allah ya raba lafiya sai su gode masa........Kafin gari ya waye komai yayi tsaf! Hajia Rabi da Yaya Ramlatu sun gyara maijego da babynta mai kama da ubansa, dakin yayi tsaf dashi sai qamshin turaran wuta yakeyi.....Da Asubah Hajia ta sanar da Alhaji haihuwar ya dinga murna da farin ciki yana Allah Allah a idar da Sallar ya sanar da Mahaifin yarinyar, to shima Malam yayi farin ciki dajin cewa yarinyar shi ta haihu cikin koshin lafiya, cike da farin ciki ya shiga gida domin ya sanarwa da matarsa halin da ake ciki. Yaya Ramlatu itake tsaye a kan Naja'atu da yaronta dan da gari ya waye ma itace tayi wa yaron wanka ta shiryashi cikin kayan sanyi sannan ta kai Naja'atu toilet ta gasa mata jikinta sosai tasa ta ta zauna a cikin ruwan d'umi! Naja'atu ta dinga mamakin irin dawainiyar da Ramlatu keyi mata ko a mafarki bata ta'ba tunanin hakan na iya faruwa ba. Kafin takwas na safe Naja'atu tasha gayu tayi kyau tamkar ba ita ba, Ya ramlatu ta taimaka mata ta shirya jikinta cikin wani Swiss les mai kyau! Hajia kuwa da kanta ta shiga kicin tayi mata abun kari na mussaman sannan ta zauna a kusa da ita sai data tabbatar da taci ta koshi tukkuna ta fita daga dakin......Bayan kowa ya gama shige da ficensa a dakin, Naja'atu a hankali ta kai hannu inda yaron yake ta daukoshi ta riqe a hannunta, tsira masa ido tayi kawai tana kallonsa, yaron kamar sa daya da ubansa tamkar Bash yayi kaki! ya tofar, wasu irin hawaye ne masu zafi suka shiga zobo mata, wai yau itace ke dauke da d'an Bash a hannunta, ashe dai sai ta fara haifawa Bash d'a kafin ta haifawa Abbah Abbas, gabanta ne ya fad'i Data tuna irin kauce kaucen da Abbah Abbas din ke mata, to yanzu dai gashi ta haihu lafiya kome zai biyo baya oho! itakam idan Abbah bai mai da ita gidansa ba to tana jin ita da aure har abadah! Hawayen take sharewa wasu na sake kwararowa, cikin wannan halin ya shiga dakin ya sameta. Bata san ma ya shigo ba sai qamshin turaransa ne ya sanar mata shigowar tasa, da sauri ta dago kanta tana kallonsa suka tsirawa juna ido.........Dauke kansa yayi daga kallonta cikin nutsuwa ya zauna gefanta tare dasa hannunsa ya kar'bi yaron yana dubashi. Tausayinsa da tsantsar kaunarsa suka sake karya mata zuciya sai kawai ta dukufar da kanta ta cigaba da rera kuka wanda na rasa ko na menene! Abbah bakinsa yasa kunnan yaron dama da hagu yayi masa kiransa sallah sau uku sannan yasa masa kalmar shahada duk dai a kunnuwan nasa ya d'ago kanshi cikin nutsuwa ya tsirawa fuskar yaron ido..........Hausawa sukace labarin zuciya a tambayi fuska ni kaina a lokacin dana kalli fuskarsa sai dana tausayawa masa, dan kallon fuskar yaron tasa yasa ya tuno da abubuwan da suka shud'e yana tunanin da Naja'atu na gidansa da tuni wannan yaron dake riqe a hannunsa nasa ne, kallon fuskar yaron tasa ya tuno da fuskar ubansa duk da sau daya ya ta'ba ganin Bash amma baya ta'ba tunanin zai mance kammaninsa, Tamaza! yayi yayi saurin aro dauriya da jarumta ya kalleta tare da fad'in "Sannu ina fatan babu abunda ke damunki."! shuru tayi masa ta kasa magana saboda kukan da yaci karfinta Gyaran murya yayi a nutse ya kira sunanta." Naja'atu." Dago kanta tayi tana kallonsa hawaye na sake zubowa, "Kukan me kikeyi bayan Allah ya sauke ki lafiya ai sai ki gode masa." Murya na rawa tace"Abbah tausayin ka nake ji wallahi dan Allah ka gafarta min abunda nayi maka wallahi ban zubar maka da ciki ba." Kawai sai ya tsaya yana kallonta, Kafin yayi murmushi ya dan sunkuyar da kansa yana nazarin maganarta, wai tausayi shi maganar ma dariya ta bashi Yace."Cikina daya zube a jikinki dama haka Allah ya hukunta, maganar tausayi kuma ki daina nima na kusa samun k'aruwa ko baki da labarin amaryata nada ciki." Yafad'a yana kallonta ido da ido Sai taga maganar tasa kamar akwai cin fuska a ciki, a sanyaye tace"Na sani Allah ya rabasu lafiya." Ya amsa da ''ameen ya Allah Wane suna kike so a sakawa yaron ki."Da sauri ta kalleshi, yace."Eh inaso nayi masa hud'uba ne kafin na tashi. Tace"Ko wane suna asa masa. "A'a kina da ikon ki za'bi sunan da kike so a saka masa dan haka ki duba dai. Kai tsaye tace" Kasa masa sunanka tunda a yanzu kai ka zame masa uba." Girgiza kansa yayi yace."Kece 'Yata shi wannan sai dai a kirasa da jika na, dan haka ba sunana ya kamata a saka masa ba na Malam za'asa masa ko kuma a saka masa sunan babansa Bashir." Da sauri tace"Abbah dan Allah kada kasa masa sunan wannan mugun mutumin azzalimi wanda ya kwashe kayansa daga gaban ma'aiki, ni sunanka nakeso kawai kasa masa. Yace."Ki daina tsine masa kina kwashe masa albarka yana a matsayin uban danki sannan ita shiriya ta Allah ce watakila Allah ya shiryeshi ya dawo ku daidaita kanku........Fad'ar wannan magana da yayi sai ta sake tunzura ta dinga zazzagin Bash din tana tsine masa albarka da fadin Sai dai ta mutu babu aure akan ta koma gidan Bash har da cewa insha Allahu ba zaiga annabi ba. Abbah da kyar ya sata tayi shuru a maimakon ta tsaya ta cigaba da sauraran nasihar da yake mata kawai sai ta kwanta ta juya masa baya zafafan hawaye na zubo mata Yaron ya ajiye mata a kusa da ita ya fita daga dakin yana mamakin al'amarin.....Kafin ya tafi harkokinsa sai ya tsaya ta tambayi hajia ko da akwai abinda ake bukata, hajia ta fad'a masa duk abinda ake bukata yace insha Allahu zai turo yaronsa Aikuwa wajejan sha biyu na rana Abdulhamid ya kawo uban naman rago gami da kaji gyararru da kayan tea da uban cefane mai yawa...........A take Hajia ta umarci Yaya Ramlatu data taimakwa Jummai mai aiki da suyi wa Naja'atu miya irin ta masu jego. Sai bayan la'asar iyalin Abbah Abbas suka sauka a gidan dukkaninsu har da yaran tinda washe garin ranar haihuwar jumaa ce sun taso daga makaranta da wuri yaran sai murna sukeyi zasuje suga d'an jinjiri......To bayan sun gaisa da hajia kai tsaye dakin da maijego take suka nufa...Naja'atu da aunty Maryam suna hira sukaji sallamarsu, halisa kamar ba itaba ta karasa cikin dakin da faraa a tare da ita take fadin"Lallai haihuwa da lafiya abar alfahari ce gaskiya na taya ki murna naja'atu Allah ya raya ya baki lafiya." Aunty maryam ta amsa da ameen tana miqa mata yaron, Halisa ta karba tana dariya kamar ba itaba suka gaisa da Aunty maryam din cikin sakin fuska, aunty maryam ta dinga mamakin al'amarin, Zainab kuwa sai dauke kai take tana ya mutsa fuska, aunty maryam tace "Sannu uwar biyu kema ai kin kusa Allah dai ya raba lafiya." A hankali ta amsa da "Ameen." Najaatu ta dan kalleta na minti biyu ta kau da kanta ta rasa me yasa gabad'aya Zainab din ke bata haushi iyayinta shine abinda tafi tsana a tare da ita Halisa ta gama duba yaron ta miqawa Zainab da fad'in ''Gashi ki daukeshi kema kisa albarka." Zainab ta ya mutsa fuska da fad'in aunt Halisa bana iya daukarsa ni kai dai nasan abunda ke damuna Allah yasa masa albarka." Babu wanda yaji dadin abinda tayi ai ko yaya ne ta daukeshi koda kuwa bata jin dadin jikinta...Naja'atu taji haushi sosai sai dai ta bawa zuciyarta hakuri ta cigaba da amsawa Halisa maganar da suke......Su Saddiqa ne suka shigo dakin suna murmushi. Aunty Maryam tace"Yawwa dama tun dazu 'kaninku yake neman ku da har yayi fushi na bashi hakuri." Da sauri mussadiq ya karasa kusa da Halisa yana dariya yana leqa fuskar yaron, Halisa tace zauna nasa maka shi a jikinka. Ya zauna da sauri tasa masa yaron ya rungumeshi su Saddiqa na leqen fuskarsa! Aunty Maryam ta kalli Mufida da fad'in "Albishirin ku." Mufida tace"Goro." Aunty maryam na dariya tace"To dai yaro yaci sunan Abbanku dan sunan da mamansa ta za'ba masa kenan." Ai gabad'aya sai yaran suka shiga murna da farin ciki Halisa na 'yar dariya tace"To ikon Allah ashe sunan maigida aka saka masa gaskiya dole na fito da kyau ranar suna." Aunty Maryam ta dinga dariya tana fad'in "Aikuwa hakan nada kyau. Zainab kamar ruwa ya cinyeta a dakin tayi d'if bakin ciki kamar ya kasheta jin wai sunan mjinta ta sakawa yaronta yasa ta sake jin wani sabon kishi na taso mata....Gabadaya zaman dakin ne ya gundureta mutukar zata waiwaya ta kalli Naja'atu shar da ita tana dariya da farin ciki to ji take kamar zata mutu saboda bakin ciki....Miqewa kawai tayi ta kama hanya fita, dukkaninsu suka bita da kallo har ta futa babu wanda yayi mata magana a cikinsu.....To aunty maryam dai da Halisa ba yara bane dukkaninsu sun gane abinda ke damun yarinyar itama Naja'atun taso ta fahimci wani abu kawai ta share abun ne dan a zauna lafiya amma zahirin gaskiya irin halin ko in kulan da Zainab ke nuna mata yana yi mata ciwo. Zainab falo ta fito ta zauna ita kadai abun duniya ya isheta, ita kuwa Yaya Ramlatu sai shige da fuce takeyi a tsakanin Dakin maijego da kicin tana sakin habaici ga Zainab din(???? mai hali baya fasa halinsa hausawa suka ce idan ka kwana biyu ba kaga mutum ba to kana ganinsa ka fara tambayarsa halinsa) Zainab muzanta tayi kwarai da gaske sai ta shiga data sanin fitowa falon , sunkuyar da kanta tayi kuka na kokarin kufce mata....Yaya Ramlatu bata qyale Zainab ta sarara ba sai da taga hajia ta sakko tukkuna ta rabu da ita. Har yamma suna gidan aunty maryam kuwa ganin yamma tayi yasa tayi musu sallama ta tafi gidanta......Halisa da Zainab suka zauna jiran zuwan mijinsu domin haka yace su zauna su jirashi idan yazo sai su tafi tare.....Daf da magariba Abbah da Abbah magaji suka shiga gidan Alhajin Abbah Abbas da kansa ya jagoranci Abokin nasa har dakin da maijegon take ya shiga ya duba yaro da mamansa, Naja'atu kasa hada ido tayi dashi sabida kunya kuma tayi mamakin yanda ya dauki yaron nata yayi masa addua sosai, ta dinga jin wani iri a jikinta tana tuno irin rashin arzikin da dinga yi musu a lokacin auranta da Bash! tana can tunanin abinda ya shud'e suka fita daga dakin ba tare da ta sani ba. *Littafin na kudi ne.....!* Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar karantawa ga yanda abin yake....Vip gruop#600 normal group #300 account... 0542382124....Binta umar gtbank... Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* Takwara nima ina bayanki gaskiya abun na Abbah Abbas yayi yawa, haba yace shi ba mayar da ita zaiyi ba to me yasa yake damun kansa a kan al'amuranta hidimar tayi yawa???? kuma Zainab macace dole tayi kishi tunda halak ne! itama Halisa ruwa ne ya daki babban zakara shiyasa tayi sanyi......gaskiya Zainab da Halisa suna da hakuri☺️...........Nafisat maganarki haka take Najaatu dawa ta dogara da har takewa wata al'kawarin zata bata jari???? Kawai ta samu mutum sai tatikeshi take koda yake ai yace saboda Allah da Annabi yake mata hidima! hummm! to maji ma gani dai wai an bunne tsuhowa da ranta???? *MADADI* 72*****Naja'atu sai wajajen tara na dare da samu sukunin kiran wayar su Mmn Sajida ta fad'a musu ta haihu! Mmn Sajida kamar ta fasa wayar dan murna a gurguje ta shiga gidan Mmn Ladi ta sheda mata, Mmn Ladi na murna da farin ciki ta kar'bi wayar tana mata barka tare da fatan Allah ya raya abunda aka samu.....Sun juma suna hira da juna kafin tayi musu sallama cike da jin kaunarsu a cikin ranta. To a takaice dai Sai da Naja'atu ta kwana uku da haihuwa tukkuna Baba Talatu tazo ta duba taga abinda ta haifa daukar yaron tayi tai masa addua daidai gwargwado tabbas komai qinka da abu idan Allah ya qaddara faruwarsa babu yanda za'akayi, babu shakka rabon wannan yaro ne ya raba auran *MADADIN* da suka daura amma suna fatan Allah ya mayar dashi da alkairi...............Bayan ta gama zancan zucci da take sai ta kalli Naja'atun a nutse tace" 'Dazu Magaji yake fad'a min cewar wai kin za'bawa yaro suna hakane ko."? A sanyaye tace"Eh Baba nace ayi masa hud'uba da sunan Abbah Abbas dan ganin yanda yake hidima nasan babu abinda zanyi na biya shi dawainiyar da yake dani amma hausawa na cewa yaba kyauta tukwici a ganina sunansa yafi cancanta a sakawa yaron." Baba Talatu tace"Lallai kinyi tunani mai kyau Naja'atu kuma nayi farin ciki sosai da wannan yaro yaci sunan Alhaji Abbas ina rokon Allah yasa ya gaji irin halinsa." Kanta a 'kasa ta amsa da ameen ya Allah." Baba malam ma da yaji sunan da Naja'atu ta za'bawa yaron yaji dadi sosai saboda haka A daran ranar da Baba Talatu ta fad'a masa maganar ya aika aka dauko masa yaron yayi masa hud'uba da sunan Abbas kamar yanda Naja'atun ta buqata.. 'Bangaran Abbah Abbas kuwa koda ya samu labarin anyiwa yaro huduba da sunansa beyi mamaki ba saboda dama kafin hakan ta kasance sunyi maganar da ita kawai sai yayi fatan alkairi tare da yiwa yaron adduar shiriya maidaiciya........Washe garin ranar yana zuwa Kasuwa ya kira Abdulhamid ya umarce shi daya shiga kasuwa ya had'o kayan baby duk wani abu da yasan masu haihuwa na bukata ya siyo idan ma bai gane ba yayi tambaya a gurin yace a hada masa set biyu, yana nufin dana Naja'atu dana Zainab duk da ita bata haihu ba yana ganin idan ya siya ya huta tunda itama a kan hanya take cikinta yanzu yana wata bakwai. Abudulhamid ya nufi kasuwar wambai dama dan wajejen ne, kai tsaye gurin masu siyar da kayan bebis ya nufa, yace a had'a masa kayan jarirai. Mutumin ya tambayashi namiji ko mace." Da sauri ya dauko wayarsa ya kira Abbah Abbas din ya tambayeshi, yace A had'a na maza duka duk da bawai amincewa yayi da scanning din Zainab ba yasan hasashe ne abun bai zama lallai ta haifi Namiji ba kamar yanda suka fad'a! ya dai siya kawai idan mace ta haifa ya sake siyan wasu. Sannan yace masa ya wuce da kayan gida ya kai b'angaran Zainab zai kirata a waya ya fad'a mata. Tsaf aka had'a kaya saiti biyu iri daya Abdulhamid ya shiryasu a mota ya nufi gidan Ubangidan nasa Abbah na gama waya da Abdulhamid ya kira Zainab ya fada mata cewar Abdulhamid zai zo da kayan jarirai sai ta za'bi wanda take so ta barwa Naja'atu nata....Zainab ta rasa inda maganarsa ta dosa sai kawai ta amsa da to sukayi sallama. Abdulhamid yazo ya jibge mata kaya a bakin gate din gurinta bayan fitarsa ta tsirawa kayan ido ikon Allah komai iri d'aya komai biyu sai kace kayan tagwaye sai ta shiga zargin anya kuwa ba shine uban yaron ba, to idan ba hakaba ya za'ayi ya dinga daidaitashi da d'ansa. Kamar za tayi kuka ta nufi gurin Halisa, taje ta tattagota suka zo suka tsaya a gaban kayan suna kallo....Halisa ta sauke ajiyar zuciya tana dudduba kayan tace" Saura ragon suna shine kawai abunda ya rage amma wannan hidima tayi yawa, ni kam banta'ba ganin mutum mara zuciya irin Abban Mufida ba wallahi." Yanda ta fadi maganar zaka fahimci a fusace take, dan duk abinda yake akan Naja'atun bai ta'ba qular da ita irin yau ba, haka kawai saboda rashin zuciya ya dinga daukar yaro yana daidaitashi da nasa gaskiya abunda yake yayi yawa wallahi Zainab kuwa fashewa tayi da kuka da fad'in "Kin san Allah aunty Halisa hakuri na ya kusa 'karewa nifa ba zan iya jurar wannan wulakancin ba wallahi!...Yama za'ayi ya dinga daidaita ta damu muna a matsayin matayensa komai zaiyi mana sai yayi mata ke wata hidimar ma da yake mata bayayi mana, ba dole muyi zargin akwai wani abu qasa ba ni wallahi bana son namiji munafiki ki duba kiga kwanaki yanda ya fitittuke yana kokarin ci mana mutunci a kanta ina dalili wallahi bazan zauna hawan jini ya kama ni ba." Zainab na kuka ta qarashe maganarta. Halisa tace"A'a Zainab kibi hankali kusan wata takwas kina zaune da mutumin nan amma har yanzu kin kasa gane halinsa Abbahn Mufida idan yasa kansa abu babu wanda ya isa ya hanashi, kuma wallahi ki iya bakinki rashin kunya babu inda zata kai ki ki kyaleshi kawai muga iya gudun ruwansa ai shi dai da bakinsa yace ba dawo da ita zaiyi ba to duk ranar da yazo mana da maganar zai dawo da ita mu kuma a ranar zamu mayar masa da martani.....Sannan ki daina sakar masa fuska nima zai daina ganin walwalata kwana biyu haba abun ya wuce gona da iri kawai saboda yaga munyi masa shuru sai ya dinga yi mana abunda yaga dama." Zainab tace"Nifa aunty Halisa ban iya 'boye abu a raina ba shiyasa ko gidanmu sukeyi min kallon mara kunya a gaskiya idan ba'a nan din ba to babu a inda za'a dinga cimin fuska na haqura ki duba kiga wannan aikin dan Allah kawai an kama an siyo min kayan haihuwa da wata mtssw!." takarashe maganar tare da jan tsaki. Halisa ta'be bakinta tayi tace"Allah y kyauta na fad'a miki ba tsayayya zakiyi masa ba ki 'bullo masa ta bayan gida idan kika ce zakiyi masa rashin kunya duk abin arzikin da yake da mahaifinki bai hanashi ya kora ki gida ba." Zainab jikinta yayi sanyi jin maganar da Halisa tayi, gaskiya tana jin tsoron faruwar hakan saboda tasan halin mahaifinta bashi da wasa idan ma yaji kan abinda take rigima a kai zai iya hukuntata, tana ganin zata 'bullo masa ta bayan gida kamar yanda Halisa ta bata shawara. Wuce wa tayi ta bar gurin ba tare data ta'ba komai a cikin kayan ba............Hasken solar daya haske harabar gidan nasa baisa ya lura da kayan dake gibge a guri guda ba, kasancewar girkin Halisa ne sai ya nufi gurin zainab din ya gurguje domin ya dubata. .A kwance ya sameta a dakinta yara suna falo su kadai....Yayi mamakin hakan kasance duk dare tana zama tare da yaran a falo har sai ya shigo gidan ita kuwa Zainab tana jin shigowarsa dakin sai ta shiga baccin karya yayi ta kiran sunanta tana ji taqi magana, kawai sai ya qyaleta da tunanin anjima kafin ya kwanta ya sake shigowa ya dubata watakila lokacin ta tashi. To koda ya shiga gurin Halisan ma bai samu tar'ba mai kyau ba, ta bashi abinci amma bata zauna ta bari ya gama ci ba ta bar gurin...Zuwa tayi ta kwanta ta bacci ya dauketa....Abbah bai kawo komai a ranshi ba, daya gama dube dubensa a loptop kamar yanda ya saba sai ya sake komawa gurin Zainab din nan ya tarar har ta kulle kofar falon daga ciki kamar tasan zai dawo, kasa hakuri yayi yana tsaye a gurun ya kira wayarta lokacin bata kwanta ba kuma bata kashe wayar ba amma tana kallo yana kira bata daga ba." Girgiza kansa yay ya kama hanya da niyyar barin gurin yana nazarin wani abu a cikin zuciyarsa.......Cin karo yayi da abu yayi saurin kuna hasken wayarsa yana dubawa......Ya kai minti biyar yana nazarin kayan kafin ya gane kayan daya sa Abdulhamid ya kawo ne! to meye amfanin barinsu a waje? tambayar kansa yake! wannan ya nuna masa cewar Zainab duk abinda tayi masa a yanzu tana da manufa! takaici al'amarin yasa shi jan karamin tsaki ya bar gurin tare da tunanin halin quruciyar yarinyar yasan dai duk abunda takeyi akan Naja'atu take yinsa. To al'amarin su Halisa fa ya tsananta kwana biyu sun had'e masa kai babu wacce ke sakar masa fuska, tun abun na bashi dariya da mamaki har ya dawo bashi haushi! daya gaji da bibiyarsu sai shima ya dauke musu wuta ya shiga sabgarsa da yaran sa idan ya dawo gida yayi abinda zaiyi ya shige dakinsa ya kwanta ba wacce yake cin abincinta, kayan jirajirai kuwa daya fahimci akansu suke jin haushi, sai ya sake qudurtar kuntata musu bai dauki kayan ya kai gidan Alhajin ba sai da yasa aka kawo masa manya manya atampopi guda uku da legos less masu tsada biyu sai wani boyel mai uban kyau da tsada da saitin takalmi da jakarsa, a falon Zainab ya ajiye kayan sabida yasan dole zata kira Halisa ta gani, aikuwa a ranar kasa komai sukayi a gidan kowacce al'amarin yafi karfinta! wato fushin da suke yi ma kamar tunzurashi suke......Zainab cutar karya ta kirkira ta dinga kuka tana lanjarewa darajar abinda yake cikinta ya kulata..Ita kuwa Halisa shareta yayi ya daina shiga sabgarta......Ranar suna da sassafe ya dauki yaransa ya kaisu gidan yayi tafiyarsa sabgarsa, Halisa taga al'amarin na nema ya zama babba sai ta shirya tsaf da turaman atamfofinta guda biyu ta nufi gidan Alhajin...Ita kuwa Zainab cewa tayi babu inda za taje bata da lafiya. Halisa bata saurareta ba ta tafi tare da daukar alkawarin bashi hakuri dangane da abunda sukayi masa........... *Littafin na kudi ne....!* Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya ga yanda abin yake Vip group #600 normal group #300 account... 0542382124...Binta umar gtbank....Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan number *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* *BA HARAM BANE!* 73****To alhamdullilahi duk wani abunda ake bukatar ayiwa mai haihuwa Abbah Abbas da iyayensa sunyiwa Naja'atu sun tsaya a kanta sun mata gata fiye da wacce take da miji anyi suna cikin walwala da farin ciki Naja'atu har kuka tayi a ranar sunan ganin yanda kowa yake nuna mata kauna ita da d'anta, a gaskiya kafin samun mutane masu karamci irinsu Alhaji da Hajia sai an bincika, dama kuma barewa ba za tayi gudu danta yayi rarrafe ba, babu shakka Abbah Abbas shine zai zama magajinsu dan gabad'aya shine yake kwatanta hallayar iyayen nasa Abbah Abbas kwata kwata abin duniya bai rufe masa ido ba shi har so yake ma mutum yazo neman abu a gurinsa ya dauka ya bashi, a kasuwa kuwa bai san iya adadin mutanan daya yafewa bashika ba, shiyasa gashinan kullum Allah qara daukaka darajarsa yake yana samun addua ta kowane bangare. Halisa jiki a sanyaye ta dawo gida tana ta mamakin yanda al'amura suke kasancewa, mijinta ya siyawa mejego raguna biyu manya manya sannan ya siyi wanda akayi miyar suna duk a bakin Ramlatu take jin maganar, hakikanin gaskiya jikinta yayi sanyi da irin qaunar da yakewa yarinyar tana ganin dawo da ita gidansa shine yafi masa alkairi sai kawai ta yanke shawarar watsar da makamanta za ta kuma tunkareshi da maganar Naja'atun taji mai zai sake cewa. Ranar dama itace take da girki ta fito falo ta sameshi yana abunda ya saba, da kyar ya saurareta dan har yanzu haushin abinda sukai masa yake ji......Yace."Ai kin bani mamaki Halisa ina tunanin kece ta farkon wacce zata fadawa wani halina, meye a cikin abubuwan da nakewa Najaatu da duk zaku tayar da hankalin ku akai har kuna had'e min kai saboda baku da hankali! to inaso na tuna miki abunda kika manta, Naja'atu bata da wanda ya fini tunda tun tana shekara hudu take a hannuna nine na rainata tana riqe ta tamkar 'yar dana haifa a cikina ni ta sani duk wani nauyi nata yana kaina, koda iyayenta nada halin daukar d:awainiyarta to bazan bari ba saboda tun farko sun dauke ta sun bani ita, wannan dalilin ya sanya nake kokarin ganin na sauke nauyin amanarta dake kaina, duk ki ture ta wasu abubuwan da suka faru a tsakanina da ita, ni ba mutum ne me riqe abu a cikin ransa ba, da ina da wannan d'abiar to na tabbata ba zan kalli inda take ba, ballantana na 'batar da kwabona a kanta, sannan idan banda abunku ai Najaatu abar ku tausaya mata ne duba da halin da take ciki menene abin ganin k'yashi da kishi dan na taimaka mata."? Halisa tace"Duk naji bayanan ka amma dai kasan kishi halak ne ko.? Shuru yay yana kallonta ta cigaba da cewa"Nifa wallahi idan zaka dafa al'kur'ani ba zan yarda cewar baka son yarinyar nan ba." 'Bata fuska yay yana dan harararta Tace"Ai gaskiya ce abunda kakeyi yay yawa haba kowa ya d'ora zarginsa akanka nasan ita kanta yarinyar tana ji a jikinta ko zaka mayar da ita gidanka ne, dan haka nima wallahi nafi sha'awar ka dawo da ita dani da kai da ita Zainab din dukkaninmu sai hankalinmu yafi kwanciya Ya jima kafin yay magana yace"Na fad'a muku ni ba zan dawo da Najaatu gidana ba amma kun'ki yarda da maganata, magana ce mukeyi a kan cikinta da haihuwarta to tinda Allah yasa ta haihu lafiya ai abunda ake bukata kenan daga haka kuma me zai sake shiga tsakanina da ita idan ba gaisuwa ba, amma tunda na lura zama ku biyu ne bakwaso zan fara neman aure shikkenan sai hankalinku ya kwanta. Murmushin takaici tayi tace"Ba sabon aure ya kamata kayi ba Najaatu ya kamata ka dawo da ita dan wallahi ko sabon auran kayi ba zaka samun nutsuwar da kake bukata." Yace."Haka dai kike gani ni Najaatu bata gabana wallahi kune dai kawai kuke zargina akanta zaku wahalar da kanku ne a banza." Yana gama maganarsa ya cigaba da duba laptop din gabansa.....Halisa takaici yasa ta bar gurin, kwanciya taje tayi tana tunanin maganganunsa itafa ba yarinya bace ballantana ya raina mata hankali. Tunda akayi suna ya daina zuwa gidan da safe, ya dawo zuwa da yamma kamar yanda ya saba kuma babu ruwansa da shiga sabgar Najaatu gaisuwa ce kawai take had'ashi da ita yay abunda ya kawoshi ya tafi, ba Najaatun ba su kansu su hajia sai da suka fuskanci sauyawarsa sai duk jikinsu yayi sanyi kada fa yay musu bazata ya nuna musu abunda suke zargi ba haka bane a gurinsa. *BASH!* Abunda sukeyi dashi da abokansa ya wuce tunanin masu tunani, yanzu harkar siyar da hodar ibilis suke da turawan america, Bash ya had'a kansa da manya manya yahudawa suna ta aikin sa'bo! Yayi masifar kudi irin wanda yake b'ukata gabad'aya idan kun ka ganshi ba zaku ganeshi ba saboda dukkanin kammaninsa sun sanja ya samu duniya sosai duniya tasan da zamansa kuma abokanansa sunaji dashi saboda yana brain sosai yana kawo musu cigaba a cikin harkokin da sukeyi a 'boye............... to hausawa sukace rana dubu ta barawo rana guda ta me kaya Ranar Asabar Allah yay nufi tona musu asiri sun shirya shida abokanasa suka nufi Cameroon domin shigar da musu da kayan sana'ar tasu, lafiya lau suka sauka a filin jirgin garin suka soma saukowa kowa na goye da wata katuwar jaka a bayansa, wani ma'aikaci ya dakatar dasu, yace su ajiye jakkunan dake bayansu, cikin turanci Bash yace idan zaiyi bunkice a kansu yayi su ba zasu ajiye jakarsu ba, mutumin sabon ma'aikaci ne mai aiki domin kishin qasarsa, kawai yace azo a tafi dasu tunda sun sa gaddama sunqi suyi abunda ake bukata suyi......Jin haka da sukayi kawai sai Bash yayi dubarar dauko k'aramar bundiga dake cikin jakar bayansa ya harbi ma'aikacin nan a gwiwa kafin kice kwabo guri ya hautsine! ganin haka yasa da saurin gaske shima ya saita kafafun Bash din ya harbi daya Bash ya zube a gurin yana ihu hade da riqe kafarsa data jiqe da jini, abokansa suka nemi hanyar tserewa Jami'an tsaron da suka iso gurin suka damqe su.........sai da sojoji sukayi bunkice sosai a gurin kafin su bari kowa ya fita daga airport din, tashin hankali su Bash suka raina kansu lokacin da jamian tsaro suka ga abubuwan dake cikin jakkunansu, tun a airport din suka fara jibgarsu kafin su sasu a mota su tafi dasu.......tsayin sati guda suna binkice a kansu kafin su san kasar da kowanne daga cikin su ya fito, jamian tsaro na kasar Cameroon sun samu cikakken bayani akansu Bash cewar mugwayen 'Yan taaddah! ne wanda suka addabi mutane da gomnati dama kullum cikin bukince ake a kansu da abubuwan da suke aikatawa tunda Allah yasa yanzu suna hannu sai a yanke musu hukuncin daya dace.........Koto aka shiga dasu, alqali yaji ya kuma tabbatar da dukkanin abunda ake zarginsu dashi tsabar wahala yasa dukkaninsu basu karyata ba sabida sun riga sun saddaqar da cewa karshensu ne yazo.....A take mai girma mai sharia ya yanke musu hukuncin kisa domin barinsu a doron duniya had'ari ne hukuncin da aka yankewa su Bash babu wanda bai sa farin ciki ba lokacin ne 'yan jarida suka samu aikin yi......suka dinga daukar hotonan su da muryoyinsu Allah Sarki Bash sunkuyar da kansa kawai yake yana hawayen nadama, dan da wani dan Jarida yazo yana masa tambayoyi kasa magana yay ya dago kansa kawai hawaye na zuba a kumatunsa magana biyu kacal ya iya fad'a...."Iyayane sune silar lalacewata babu abunda zance musu sai dai nace zamu hadu a gaban Allah. Magana ta karshe da zanyi a kan wata yarinya ne dana yaudara sunanta Najaatu Ina fatan maganar nan da na keyi tana ji kuma tana kallonta, Najaatu ina rokon ki daki yafe min abunda nayi miki ba ke kadai bama da duk wanda na zalinta ina rokonsa ya yafe min ni tawa takare a duniya." Sai kawai yayi qasa da kansa hawaye na cigaba da zubowa daga idansa Lokacin da labarin abunda ya faru ya isa kunnan iyayen Bash sun shiga tsananin tashin hankali da nadamar abunda suka aikata, dan jin bayanin da Bash yayi yasa jamaar gari sun sake gazgata maganar dama kowa yana tunanin sune suka dorashi a kan hanyar banza gashi yanzu sunzo suna nadama, 'Yan jarida kuwa ai kewaye Alhaji Aminu sukayi wai lallai sai yayi musu qarin bayani dangane da jawabin da Bash din yayi kafin mutuwarsa. Najaatu kuwa al'amarin yayi masifar d'aga mata hankali tayi kuka sosai tayi nadamar rayuwa hajia kasa gane kanta tayi a gidan, sai da ta dinga yi mata nasiha gami da kawo mata misalai sannan ta daina kukan da takeyi ammafa kullum da daddare sai ta rungume 'Danta taci kukanta ta koshi!! sannan take jin sassauci bata ta'ba tunanin zata auri Mutum mai miyagun halaye ba sai gashi ta auri bash wanda ya tara munanan halaye harda albarka haihuwa a tsakaninsu hakika ta tabbata wannan al'amarin da ya faru da rayuwarta qaddarace dan da tasan abinda zai faru kenan da bata bujirewa auran da iyayenta sukayi mata ba, A duk sanda zata kalli fuskar d'anta ji take zuciyarta na karaya ta dinga tunanin halin da zai shiga idan ya girma yaji labarin ta'addacin da ubansa ya aikata kafin a kashe shi, wannan tunanin yasa ta dinga wata iriyar rama kafin tayi ar'bain duk ta fige kullum cikin tunani da nazarin yaya rayuwar d'anta zata tashi take. tunda wanda take tunanin zai tallafeta shima ya daina sakar mata fuska ya nunawa duniya cewa ba zai mayar da ita ba dan yanda yake nuna mata halin ko'in kula yasa kowa ya fahimci munufarsa ita dashi gaisuwa ce kawai ke had'a su watarana har yazo gidan ya tafi bata sani ba, dan zaman daki ta aura yanzu tafi so ta kadaice ita kadai tayi tunanin abinda zai fishsheta.............Allah Sarki Ramlatu itace ke hidima da (Daddy) sunan da suke kiran yaron dashi kenan, Tayi masa wanka ta shiryashi ta goya shi a bayanta mutukar kinga yaron a hannun uwarsa to nono zai sha, Najaatu tana jin dadin yanda Ya Ramlatu da sauran mutan gidan ke nuna kulawarsu a kan yaronta To haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau fari gobe baki Najaatu nata hakuri da halin ko'in kulan da Abbah Abbas ke nuna mata, ita abun sai ya dinga bata mamaki ya damu da d'anta amma ita kallo bata isheshi ba ko gaishe shi tayi baya kallonta yake amsawa amma wani sa'in idan yazo za taji shi suna maganar Daddy da Yaya Ramlatu wani lokacin ma har daukar yaron yake yay masa wasa kafin ya tafi. sai tayi ta mamakin al'amarin wallahi ita ta dauka dukkanin irin kulawar da yake nuna mata a baya yana so ta haihu ne ya mayar da ita sai gashi ya juya mata baya lokaci guda ko kallonta ma baya yi. Yau kwanan ta sittin da uku da haihuwa, hankalinta gabad'aya yana kansu Mmn Sajida dan kullum sai sunyi waya ita Mmn Sajida har fushi tayi saboda dukkaninsu suna lissafe da kwanakin haihuwarta tace saboda taga suna so su ganta da abunda ta haifa shiyasa take ja musu rai shikkenan zasu cireta daga rayuwarsu kamar yanda ta watsar dasu. Wannan maganar da mmn sajida tayi ta tayar mata da hankali sosai taji tana sha'awar zuwa gurinsu, sai ta yanke shawarar sanar da Abbah Abbas din domin taji me zaice akan tafiyar. Lokacin data kira wayarsa yana tare da Zainab da cikinta ya tsufa dan kamar ma naquda take a tsaitsaye dan dai haihuwar fari ce shiyasa basu gane ba amma dai bata da cikakkiyar lafiya.......Zainab ta dauki wayar tana dubawa, My dota ta gani na yawo a fuskar wayar, tasan Najaatu ce sai tace"Abbah Mufida Najaatu na kiran wayarka......Domin ya sake nuna mata babu wata alaqa a tsakaninsa da ita yace "Dauka mana." Da sauri ta daga wayar tana sallama, Najaatu taji rashin dadin jin muryar Zainab sai dai ta daure tace"Dan Allah ki bawa Abbah wayar zanyi magana dashi. Zainab tace"Kada ki damu shine yace na dauka ina sauraranki." Najaatu taji kanta ya sara! da kyar tace"Aa ki dai bashi wayar." Zainab murmushi tayi cikin sigar kuntatawa tace"Wallahi da gaske nake miki gashi ma yana kimtsawa zai fita kuma da umarninsa nake magana dake ki fad'i maganarki dani dashi duk daya ne." Najaatu ta dinga jin kamar ba'a guri guda take ba dan wani irin jiri ne ya shiga d'ibanta, sai kawai ta kashe wayar ta jefar da ita lafiyayyun hawaye suka shiga zobowa a kumatunta, wannan wulakanci dame yay kama? Lallai Abbah Na shirin ya dasa mata ciwo a cikin zuciyarta, ashe bai san yanda take bala'in jin kishin matarsa ba zai ce ta daga mata waya aikuwa ba zata qara kiransa ba, kuma tafiyarta zatayi tunda dama ba zamansa take ba Sai da taci kunanta ta qoshi tukkuna taje ta sanar da hajia maganar zuwa jos din Hajia tace'' Hakan yana da kyau sai ta fara shiri. Bangaransa kuwa koda ya gama shirinsa bai tambayi zainab komai ba tunda hands free wayar take duk yaji komai ya kar'bi wayarsa yayi tafiyarsa harkokinsa, ita kuwa Zainab a ranar yini tayi cikin farin ciki da annushuwa dan duk ciwo ciwon da take ji a jikinta daina ji tayi sabida abunda tayiwa Najaatu na quntatawa kuma taji dadin yanda ya bata goyon baya d'ari bisa d'ari. Bayan kwana uku Naja'atu ta shirya kayanta tsaf hajia ta shirya mata tsaraba mai yawa, tace ta kai musu domin sun cancanci abinda yafi haka, a ranar da zata tafi ta shiga gidan Baba Malam da wurwuri tayi musu sallama itama Baba Talatu ta bata abubuwan tsaraba tace ta kai musu, sannan tayi mata fatan dawowa lafiya. Sai da zata tafi hajia tace"Kinga ikon Allah ko na sha'afa wallahi duk zuwan da Abbansu Saddiqa keyi ban fada masa ba ko kin kirashi a waya ne."? Da sauri tace"Eh shekaran jiya na fada masa." Hajia tace"To shikkenan dama dan dai kada ya samu labarin tafiyar daga baya ne yasa nayi maganar to Allah ya saukeku lafiya a gaishe mana dasu da kyau. Naja'atu tace zasuji insha Allahu Hajia......Tare suka fito harabar gidan suna tsaye suna kallonta ta shiga mota direba yaja suka fita daga gidan............Abbah Abbas lokacin daya samu labarin tafiyar ranshi yayi masifar 'baci! ya za'ayi saboda rashin hankali ta dauki yaro karami a lokacin sanyi tayi tafiya mai tsayi dashi, shifa gabad'aya garin jos bai masa ba shiyasa bai ta'ba yi mata zancan zuwa ba, ashe jira take ta haihu ta dauki kafa ta tafi ba tare da ta sanar masa ba(Matarka ce ita da zata tsaya fad'a maka????) Hajia ta dinga tausarsa da fadin ita bata san bai sani ba wallahi amma ai ba wani abu bane dan taje ta nunawa mutanan abunda ta haifa saboda sun cancanci hakan......Yace."Hajia ba hana zuwa anyi ba a qalla dai ta bari yaron bayanta yayi kwari ki duba kiga yanda ake busa iska a gari tana iya zuwa da yaron ya samu wata matsalar yanayin gidan da zataje bashi da kyau da tsayin katanga akwai matsala sosai." Hajia ta dinga mamakin maganarsa tace"To ai lalura a ko'ina ma daukarta akeyi kuma ta tafi da kayan sanyi nasan zata kula dashi. Shuru kawai yay ya miqe tare da fadin shi zai tafi.Hajia tace to a sauka lafiya, hanyar futa ya kama ta bishi da kallo tana mamakin son 'ya'yansa. Kasa hakuri yay yana driving ya shiga kiran wayarta, lokacin har ta sauka tana tare dasu Mmn Sajida sai gaishe da juna sukeyi, su Walid da 'Ya'yan Mmn Ladi sun kewayeta tana ta basu tsarabar da taje musu da ita. Koda ta duba wayar taga number sa ce sai ta cigaba da abunda takeyi, taki dauka sai da ya kira sau uku tukkuna ta daga, tana kokarin gaisheshi ya dakatar da ita......"Ashe baki da hankali Najaatu wa kika tambaya wanda ya baki izinin tafiya wani gari? ashe kina nan da halinki na taurin kai ko." Kai tsaye tace"Abbah yi hakuri dan Allah kwana hudu da suka wuce na kira wayarka na tambayaka sai dai idan mantawa kayi." Yace."Ke bana son karya yaushe kika kira ni kika tambaye ni ai saboda kin san bazan bari ba shiyasa kika 'ki sanar dani." (Takwara zo kiga karfin hali????Tace"Wallahi na kira wayarka Zainab ta dauka kuma na fad'a mata maganar sai dai idan itace bata fad'a maka ba." Shuru yay yana tunanin maganar......." To Gobe Dan Azimi zai zo ya dauke ki dan haka duk wanda kika san zaki gaisa dashi a garin kiyi kokarin gaisawa dashi kafin gobe." Yana gama maganarsa ya kashe wayarsa.......... *Littafin na kudi ne...!* Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abun yake Vip group #600 normal group #300 account... 0542382124....Binta umar gtbank...idan katim waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* _Abbah Abbas ka janyo 'yan group yau na caccakar ka????????♀️ Mum Basma tace idan ka tsaya kallon ruwa kwado zaiyi maka kafa, ita kuma Sakina tace" Kana ruwa???? sistar Habiba tace Dantalle ya shigo kawai ayi dashi tunda kai ka tsaya wasa! To nima dai nace ka ajiye makaman ka dan idan ka tsaya jan aji za'ayi maka shigar sauri Najaatu dai a yanzu allura cikin ruwa ce (mai rabo ka dauka)_ *MADADI74* Najaatu shuru kawai tayi tana bin wayar da kallo, mamakin maganarsa take wai zai turo Dan Azimi gobe ya dauketa lallai aikuwa yanda yazo haka zai koma domin kuwa bata tunanin zata bishi to wai nauyin waye a kanta da zaice lallai sai ta dawo gida me za tayi masa bayan baya kulata sannan kullum yana tare da iyalinsa ita kuma sai ya hanata zuwa inda zata ji sassauci zuwanta gidan Mmn Sajida ya saukar mata da nutsuwar zuciya ko babu komai zatai kwana biyu bata saka shi a idonta ba, domin watarana ganinsa yana janyo mata abubuwa da dama hakuri kawai takeyi tana bin rayuwa a yanda tazo mata. Mmn Sajida ta kalleta a sanyaye tace"Najaatu naga jikinki yay sanyi ashe ba'a sani ba kika zo.''? Kallonta tayi tace"Waye ya fad'a miki haka."? Kai tsaye tace"Gashinan mahaifinki ya kira waya yana miki fad'a." Mmn Ladi tace"Eh ai nima shiyasa kika ga jikina yay sanyi wallahi. Najaatu murmushi tayi a nutse tace"Wai ku waye ya fad'a muku Abbah Abbas mahaifina ne."? bude baki sukayi suna kallonta, ta sunkuyar da kanta tana dan murmushi wanda ya tsaya iyakacin lebenta. Mmn Sajida tace ''To idan bashi ya haife ki ba waye shi a cikin rayuwarki."? Tana girgiza kanta tace"Shine mijina na fari wanda na baku labarinsa farkon zuwana garin nan. Suka tsira mata ido suna mamakin maganarta, kwallah ta cika mata ido tace"Kuna mamaki ko? ni kaina ina mamakin kyautayi da tausayi da kyautatawa irin nasa dukkanin irin abubuwan da nayi masa bai sa ya watsar dani da al'amurana ba, yana tsaye a kaina da dukkanin bukatuna." Mmn Sajida tace"Lallai Najaatu kin tafka babban kuskure a baya waye ya fada miki ana samun nagartattun mutane irin wannan mutumin? yanzu dama a kan an aura miki shi kika gudo garin nan yanzu dan Allah meye aibunsa meye kuma abun'ki a tattare dashi."? Tana kuka tace"qaddara Mmn Sajida qaddarar wannan yaron dake hannuna ce ta kawo ni garin nan har na had'u daku....Wallahi har bana so na tuno abubuwan da suka faru a baya Mmn Sajida ni da kaina nasan na tafka kuskure babba! wanda yanzu nake nadamar aikatashi, yanzu gashi inaji ina gani Abbah yafi karfina sai dai na kalleshi da ido Mmn Sajida a yanzu ne nake masifar so nayi zaman aure dashi shi kuma yana nuna baya so, wallahi bansan iya adadain son da nake masa ba a cikin zuciyata saboda mutumin ya cancanci a soshi duk wata sadaukarwa yayi min yana kanyi min babu namijin da zan aura na samu nutsuwar da nake bukata, Mmn Sajida ba zan 'boye muku halin dana ke ciki ba wallahi saboda halin ko in kula da yake nuna min yasa naji zaman garin ya gundureni na tattaro na tawo nan kuma bana tunanin zan koma a kurkusa sai na huta tukkuna." Mmn Ladi ta sauke ajiyar zuciya tace"Gaskiya Najaatu naji miki haushi da takaicin rasa wannan mutumin to amma tunda kin jingina al'amarin a matsayin qaddara muma zamu jingina shi a hakan ammafa wallahi kema da akwai son zuciyarki wanda shine ya kara sanyawa kika kai kanki ga wahala! saboda haka ni dai shawarar da zan baki wallahi ki lalla'ba da wayo da siyasa ya mayar dake dan nima na tabbatar da cewar a gurinsa ne kadai zaki fi samun nutsuwa da kwanciyar hankali saboda yanzu duniya kowa kansa ba kowane namiji ne zai yarda kije masa da d'anki ba. "Mmn Ladi wane dabaru zanyi ya mayar dani ni bazan iya fada masa baki da baki ba, na hakura zan cigaba da rainon yarona har Allah yasa ya girma, shikkenan idan na samu daidai dani sai na aura. Mmn Sajida tace." Ni kuma sai nake ganin kamar yana jira yaron ki yay wayo ya bijiro da maganar kome din kin san fa koda zai mayar dake gidansa ba zai mayar dake kina da d'anyan jego ba, wallahi ko kaffara ba zanyi ba yana sonki dan da baya sonki ba zai dinga yi miki wahala ba, haba ki duba fa ki gani shine yazo ya daukar ki anan sannan lokacin da kika kwanta a asibiti kina kiran wayarsa ko minti ashirin ba'ayi ba ya turo da kudiin da'a ka bukata..........Duk da kin kasance mai laifi a gurinsa hakan bai hanashi kula dake ba, ki kwantar da hankali da kansa zaiyi miki maganar ki koma gidansa amma kema dole ki dan yawaita kwalliya da gyaran jikinki da kowane lokaci ya dinga ganinki tsaf tsaf zaki janyo hankalinsa sannan kina kiransa a waya kina gaisheshi." Najaatu murmushin takaici tayi tace"Mmn Sajida sau nawa zan kira wayarsa yasa matarsa ta dauka! a gabanki ma fa hakan ya ta'ba faruwa Abbah wani irin mutum ne wanda baka gane gabansa da bayansa." Mmn Ladi tace"Kome baud'ewar halinsa mace na iya sanja shi saboda haka idan kika mayar da hankali akan shawarwarin da muke baki zasu taimake ki." Najaartu shuru kawai tayi tana sauraran maganganunsu, tana daukar na dauka tana watsar dana watsarwa bata tunanin zata tunkareshi da maganar ya mayar da ita gidansa idan ya tausaya mata da yaronta ya mayar da ita haka take so idan kuma yana ganin bashi da ra'ayi sai ta hakura ta barwa Allah. Sai bayan taci abinci ta nutsu tukkuna ta shiga fito musu da tsarabar data kawo musu , kowacce turmin atamfa biyu da mayafi da takalmi sai sabulai na wanka dana wanki da kayan kwalliya irin na mata. Sosai suka shiga yi mata godiyar hidimar da tayi musu, ashe da sauran godiya, dan kudinta na haihuwa data samu kimanin dubu saba'in da wani abu a ciki ta dauko dubu hamsin ta kawo musu Mmn Sajida ta miqawa tace su raba....Mmn Sajida ta riqe kudin a hannunta tana kallonta cikin d'umbun mamaki! Murmushi tayi ta kalli Mmn Ladi tace"Mmn Ladi naki kudin sai kiyi kokarin ki fara sanaa dasu kafin naga abunda Allah zaiyi anan gaba insha Allahu idan na samu yanda nake so zan qara miki wasu. Mmn Ladi fashewa tayi da kuka ta rungumeta tana fad'in "Wallahi Najaatu na rasa bakin da zan gode miki ashe ke din alkairi ce a tare damu muna mutukar alfahari da sanin da mukayi miki wallahi Kinyi min abunda d'an uwa na jini baiyi min ba, a cikin 'yan uwana akwai masu hali amma babu wanda yay tunanin dauko kwabonsa ya bani da sunan naja jari nayi sana'a sai ke da Allah ya had'ani dake kin gyara min aurena kuma kin dauki kudi kin bamu, kin kawo min babban zani irin wanda banta'ba daurawa ba, babu abinda zance sai dai nace Allah ya saka miki da alkairi ya biya miki dukkanin bukatunki. Naja'atu tace"Haba Mmn Ladi meye abun kuka wallahi wannan ba komai bane a gurina idan ina da abunda yafi haka zan baku domin kuma kun taimakawa rayuwata a lokacin da nake bukatar taimako saboda haka ki daina kuka kina gode min Allah ne ya had'amu ina fatan zumuncin mu ya d'ore har 'ya'ya da jikoki." Mmn Sajida tace"Insha Allahu Najaatu Allah zai cika mana burin mu kuma kamar yanda muke zumunci insha Allah 'ya'yanmu suma za suyi." Da wannan addua ta Mmn Sajida suka rufe maganar suka shiga hirar Bash da hukuncin da'a ka yanke masa. Laifin Najaatu ya shafi su Halisa a tunzure ya shiga gidan, girkin Halisa ne ganin yanda ya shigo yana shan qamshi yasa bata tunkari inda yake ba gudun wulakanci yasa taje tayi kwanciyar a dakinta tana kallo, har ya gama abinda yake a falo ya shigo yay shirin kwanciya, zama yay gefan gado da wayarsa a hannunsa. Number Najaatu ya nema Lokacin dare yayi dan goma da rabi ta wuce duk sunyi shirin kwanciya Mmn Sajida dalilin zuwan Najaatun yasa bata fita sana'arta ba, suna hira sama sama kiran wayarsa tasa ya shigo. Ta dauka tana dan tunani to me ya kirata yace mata? Shawarar dasu Mmn Sajida suka bata ta tuna, sai kawai ta daga wayar tana wani maqale murya tace"Hello Abbah! barka da dare." Wani irin yarrr! yaji a jikinsa sakamakon jin yanda muryarta ta ratsa jikinsa, tamaza yay yayi gyaran murya as'usul yace."Barka dai ina fatan kin suturta yaron nan da kayan sanyi saboda kin san dai yanda ake sanyi gashi na lura gurin da kike bashi da tsaro da sauransu." Dan murmushi tayi tana kallon Mmn Sajida, ta sake kashe murya tace" Abbah ni baka damu dani ba kenan kana tambayar na suturta Mai sunanka nima ai ina jin sanyi sosai a jikina."! Cikin shagwaba ta k'arasa maganar. Shuru yay na minti biyu kafin yace."Ke ai kin girma sanyi ba zai miki lahani ba kamar shi so sabida shi na kira wayarki sannan kuma na sake tunasar miki da abinda na fad'a miki d'azu! gobe da wurwuri Dan Azimi zai zo ya daukeki." Kamar za tayi kuka tace"Allah ni bazan dawo gobe ba, Abbah wa na'ajiye a garin kano da zan takurawa kaina dawowa ni dai dan Allah ka bari na kwana biyu a gari jos dan ina jin dadin garin sosai da sosai.'' A hasale yace."Ke! ashe baki da hankali wannan garin duk babu mutunin arziki a cikinsa ashe kina so ki sake haduwa da wani mara tarbiya kenan( Afuwa mazauna wannan garin banyi da niyyar naci muku fuska ba labari ne yazo a haka a gafarce ni garin jos akwai masu tarbiya sosai ga misalin irinsu Mmn Sajida nan nayi)......Tace"Haba dai Abbah ba duka a ka zama d'aya ba Wallahi su Mmn Sajida suna da kirki da tarbiya kuma ni da naje ziyara mai zai had'a ni da wani saurayi ko bazawari babu ruwana dasu. Yace."Ni dai na fad'a miki gobe ki zauna cikin shiri domin hankalina bai yarda da zamanki a wannan gari ba." Kashe wayar yay bai saurari ta bakinta ba.......Halisa ta miqe zaune tana hararar bayansa ji take kamar ta makeshi! saboda haushi yana yaudarar kansa yana yaudararsu to meye nasa na damuwa dan ta tafi jos da har zai ce zai tura a daukota. tsaki taja a zuciyarta kafin tace"To wai kai meye na damuwa dan ta tafi wannan gari? babu fa nauyin kowa a kanta da kake cewa ta dawo haba ai ka kyaleta ta huta su gaisa sosai da wannan mutanan da sukayi mata hallaci." Yana jinta yay shuru sai ma ya fara kokarin kwanciya yana kokarin rufe kafafunsa, Halisa bata san sanda taja tsaki ba tace"Abban Mufida kenan ka tsaya wasa wallahi sai dai kaji anayi dan Najaatu a yanzu allura cikin ruwa ce da d'anyan jegon da take dashi ba zata rasa me auranta ba......Fad'in wannan magana da Halisa tayi sai ya fusata! ya miqe zaune ya dinga zazzaga mata masifa da fad'in "mahaukacin Namiji ne zai auri mace da d'anyan jego saboda haka kada ta kuskura ta sake yi masa irin wannan magana. Halisa itama ta fusata tace" To itama kada ya sake zuwa gabanta yayi waya da Najaatu tunda abun nasa ya zama rainin hankali, haka suka dinga cacar baki tana fad'a yana fad'a dan gabanyansu a tunzure suke kowa yana ganin ba'ayi masa daidai ba.......Gabad'ayansu Haka suka kwanta suna jin haushin juna..... *Infaction* _Ko wace mace kaji tace miki tana fama da infaction wai shin ya zamuyi mu kare kanmu daga wannan laluran mai wahalar magani? Idan kina da sanyi koda mijinki bai dashi sai ya samu....Ko kuma ke baki dashi mijinki nada shi to sai kin samu, idan ya kasance duk kuna dauke da lalurar sai ku durfafi shan magani a tare! dan idan daya yasha daya bai shaba to akin banza kukayi ciwon yana nan babu inda zaije..........Kina budurwa kina kyaikayin gaba da zubar da farin ruwa gashi an kusa bikin ki kinja bakinki kinyi shuru baki fadawa mamanki ba, to zaki haifarwa da kanki matsala babba dan idan kikaje gidan mijinki da wannan ciwo kika shafa masa zai miki mummunar fahinta ya dunga yi miki wani irin kallo na daban......... saboda haka mutukar kina da matsala irin wannan maza ki sanar da mahaifiyarki kafin ki sanar dani mahaifiyarki itace mafi kusa dake kuma ita ta haifeki babu kunya a tsakaninku! Ki fada mata komai zata kaiki gurin mai magani....Ni shawara ce kawai a tsakaninmu._ *Idan da tsumma kike using a lokacin da kike jin al'ada to ya kasance kullum kina sanjawa sau uku ko sau hudu, sannan idan kin wanke tsumman ki dinga sashi a rana ya bushe kwayoyin cutar zasu mutu.......mutukar kina barin matuncin ki da danshin ruwa to ba zaki rabu da kyaikyayin gaba ba, wannan guri an fiso kullum ya kasance a bushe.......Idan da pad kike using lokacin haila yana da kyau kina sanjawa a kai kai kada kisa tun safe ki barshi sai dare dole gabanki yayi miki kyaikyayi daga haka kuma kwayoyin cuta su shiga jikinki, wannan kyakiyayin masifa ne, saboda haka dan Allah muyi hattara????????♀️* Vip group #600 normal group #300 accont...0542382124....Binta umat gtbank...WhatsApp number... 07084653262 _Yau mura ta hana ni nayi muku post akan lokaci duk naga adduoin ku dana pravite dana group ????????♀️ Nagode sosai Binta tana tare daku insha Allah????_ *BHRMBN 74_75* Da maganar Halisa ya kwanta bacci ya kuma tashi da maganar a cikin ransa, ya jima yana nazarin maganar da tunanin abinda zai biyo baya a jos din mutukar an san ita din bazawara ce to tabbas maganar Halisa na iya kasacancewa a samu wanda zai ce yana sonta duk da jegon da take dashi, dan haka yana dawowa daga masallaci ya nemi number wayar Dan Azimi suka gaisa da juna yace."Ina fatan dai ka shirya ka tafi da wuri bana so kuyi shigowar dare. Dan Azimi yace."Eh gani nama fito Insha Allahu yanzu zan tafi, Yace." to Allah ya kiyaye hanya inda ka sauka sai ka kira ni ka sanar dani ." Dan Azimi yace."Insha Allah ranka ya dade." Sallama sukayi ya kashe wayar ya miqe ya fita falo....zama yay kan kujera yana jiyo motsin Halisa a kicin, tsabar 'bacin rai Halisa ko gaisheshi ba tayi ba, yana kallonta ta fito daga kicin ta nufi dakinta ko kallonsa ba tayi ba, miqewa yay yana girgiza kansa ya nufi gurin Zainab, babu kowa a falon lokacin da shiga sai ya nufi dakin yaran sa domin duba su, suna tare da Baba Larai tana taimaka musu da shirin makaranta, a nutse yaran suka gaishe shi ya amsa cikin kulawa shima ya gaishe da Baba larai ya tsaya suka danyi maganar yaran da ita kafin ya fita daga dakin. Zainab tana zaune kan dadduma tunda tayi sallah ta kasa motsawa daga inda take marar ta ce take wani irin ciwo....Cikin mawuyacin hali ya sameta, hankalinsa ya tashi ya taimaka mata ta miqe tsaye, yana tambayarta abinda ke damunta, cikin halin ciwo ta fada masa cewar mararta ke ciwo, zaunar da ita yay gefan gado yace."Bari na kira Baba Larai ta dubaki ko haihuwa za kayi....Fita yay daga dakin sauri, koda baba larai taga yanayin Zainab a take ta fahimci cewa haihuwa za tayi, tace"Alhaji haihuwa yarinyar nan za tayi amma yana da kyau aje asibiti domin a sake tabbatarwa, Yace."Okey bari na sanar da Halisa....Halisa jin cewa zainab zata haihu yasa ta biyo bayansa halin da taga Zainab a ciki yasa jikinta sanyi, kayan haihuwa kawai suka hada suka nufi asibiti Zainab duk ta rikice da ihu! gabadaya ta manta da addua sai ihu take tana kiran a taimaka mata gabadaya hankalinsu ya tashi harshi Abbah Abbas din dake driving hankali a tashe ya kara karfin motar suka isa asibitin nasarawa. Zainab bata dade tana doguwar naquda ba Allah ya sauketa lafiya inda ta haifi 'ya mace mai kama da ita sai dai ta dauko hasken fatar babanta, Abbah yayi farin ciki sosai ganin yanda Allah ya raba lafiya maijego da babynta lafiyarsu lau.........Kafin su bar asibitin Abbah ya sanar da duk wanda ya dace ya san haihuwa, awa biyu kacal sukayi a asibitin aka sallamesu....Suna koma gidan suka tarar da 'yan uwan Zainab sun cika gidan, Abbah ya tsaya suka gaisa a gurguje ya fita ya basu guri Bangaran Halisa ya koma domin ya kimtsa jikinsa. Allah sarki Halisa ganin yanda yake ta murna da haihuwar zainab din yasa itama taji tana sha'awar haihuwa tunda ta haihu sau biyu bata sake haihuwa ba, mufida yanzu shekaranta goma sha uku amma ko 'batan wata ta sake ba, zama tayi ta zabga tagumi abin duniya ya isheta. Ganin ya shigo dakin ne yasa ta miqe ta fita ta basa guri gabad'aya duniya tayi mata zafi tana ta nadamar cutar da kanta da tayi tana tunanin ko magungunan turawan data dinga d'ubga ne ya toshe mata mahaifa gaskiya dole ma taje asibiti a dubata tunda ba wuce haihuwa tayi ba. Zainab na tsakiyar 'yan uwanta suna ta zugata ita kuma ta saki baki sai fad'a musu karya da gaskiya takeyi...Wata yayarta tace"To yanzu ai duk wani abu da kika san kina bukata ki rubuta masa kuma kada ki sake kiyi amfani da kyan babyn nan ya sake siya miki wasu, sannan kice kina so ya siya miki set gold zakiyi fitar bikin suna dashi. Zainab tace"Duk abinda nake so yana kaina ke har mota nima sai ya siya min tunda na tabbatar wacce aunty Halisa take hawa shi ya siya mata. Yayar tata tace"Ato idan kika tsaya wasa sai ki zama koma baya tunda kin haihu dashi ai kin zama kujera a gidansa....Zainab murmushin jin dadi tayi ta juya ta kalli babynta dake kwance a gefanta. Yaya Ramlatu da Hajia Rabi da Baba Talatu ne sukayi sallama a dakin. Da sauri Yayar zainab ta miqe tana musu barka da zuwa ta basu guri suka zauna suna gaisawa, Babyn ta dauko ta miqawa baba talatu da fadin "Ga bakuwar duniya mai kama da babanta." Baba Talatu ta karbi yarinyar tana murmushi cikin nutsuwa tace"Masha Allah Allah yayi mata albarka babu shakka yarinya ta dauko gida Allah y raya mana ita. suka amsa da amin. Baba talatu ta miqawa Hajia Rabi itama ta karbe ta tayi mata addua sannan ta miqawa Yaya Ramlatu. Yaya Ramlatu tayi murmushi idonta a kan babyn tace"Yarinya dai ta dauko hasken fatar gida amma kuma kammaninta sak na uwarta." Zainab tayi saurin kallonta tana mamakin maganarta, ita kuwa yayarta cikin ya'ke tace"Aikuwa baki ji bahaushe yana cewa kyawun d'a ya gaji uwarsa ba." Ya Ramlatu tayi dariya cikin sigar kuntatawa tace" Kyawun d'a ya gaji ubansa ake cewa yarinya ta gaji ubanta gurin haske fata kammani kuma na uwarta ne Allah yasa kada ta dauko halinta." Hajia rabi tace"Wace irin magana ce wannan."? cikin takaici Ramlatu tace"Hajia duk sanda zan kalli yarinyar nan sai na tuna sanda ta wanke ni da mari ni kam a tarihin rayuwata ba zan taba mancewa da ita ba." Jin wannan magana yasa 'yan uwan Zainab jikinsu yay sanyi kunya duk ta dabaibayesu, Zainab kuwa tuni ta fashe da kuka gabanta sai faduwa yake Ramlatu tazo ta tona mata asiri a gurin 'yan uwanta Yayar Zainab tace"Dan Allah kiyi hakuri 'yar uwa maganar tone tone duk bata taso ba alheri da farin ciki ne ya kawo muku gidan nan saboda haka idan zainab tayi miki wani wanda bakiji dadinsa ba ki gafarce ta akwai kuruciya a tare da ita Ramlatu tace"Iskanci dai ba kuruciya ba, ai magana ni ta wuce a gurina wallahi kawai dai idan na tuna al'amarin raina yake baci." Cikin fusata! Yayar zainab din tace" Ashe dama abunda kike yi kenan yanzu kamar wannan matar tana a matsayin yayar mijinki ki fitar da hannu ki mareta to Sai ki bata hakuri tunda ke baki da mutunci." Zainab na kuka tace"Yaya Ramlatu ki gafarce ni wallahi tsautsayi ne." Cike da takaici tace "Dena kuka ai na yafe miki tuntuni saura kuma idan ya dawo ki fada masa ga abinda nazo nayi miki kisa shi ya kawo min rundunar sojoji." Zainab tace"Wallahi ko wancan karan ma bani nasa shi ba kiyi hakuri." Baba Talatu tace"Ke kam Ramlatu abu baya wuce wa a gurinki ne? yarinyar nan ta baki hakuri magana ta kare dan Allah. Yaya Ramlatu tace"Magana ta wuce baba insha Allah bazan sake tada ita ba." Karfe uku saura na rana Dan Azimi yayi parking din mota a kofar gidan Mmn Sajida, sai dai me? yana fitowa yaga katon kwado kulle da kyauran gidan.....Ya jima yana mamaki kafin ya bude motar ya zauna ya shiga kiran wanda ya aikoshi, ya sheda masa abunda yake faruwa. Abbah jin abinda dan Azimi yake fad'a masa yasa ko gama sauraransa baiyi ba ya kashe wayar da sauri ya nemi number ta......Lokacin suna gidan bikin sunan k'anwar Mmn Ladi, dan da zasu tafi cewa tayi ba zata zauna ita kadai a gida ba sai ta shirya tsaf sukayi tafiyarsu bayan tasan da maganar zuwan Dan Azimi. Hayaniyar jama'a ya hanata taji abinda yake cewa sai kawai ta kashe wayar ta ta ajiye tasan dai maganar zuwan Dan Azimi zaiyi mata ita kuwa ba taga dalilin da zai sanya ta koma gida a yanzu ba. Abbah ya shiga mamaki mai tsananin gaske yau shi Najaatu ta kashewa waya! to wai shin ma ina ta tafi a garin da bata da kowa hakika yarinyar nan na nema ta d'ora masa ciwon zuciya. Wayar ya sake kira sai ta miqe daga cikin mutane ta samu gurin da babu hayaniya sosai ta daga a sanyaye tace"Abbah ina kwana wallahi ina cikin jamaa ne shiyasa bana jinka sosai." Yace."Kina ina Dan Azimi tuntuni yazo daukar ki bakya nan to har in dai na isa dake duk inda kike kiyi maza ki koma yana zaman jiran ki." Abbah dan......Katse ta yay da sauri yace."Kina so ki 'bata min rai ko? na fad'a miki bana son zamanki a wannan garin nasan dai daga jiya zuwa yau duk wanda kika sani a garin kin gaisa dashi to zaman me za kiyi kuma gashi nan kwana d'aya kacal da zuwanki kin fita yawo shin me kike so ki zama? saboda haka na gama magana idan na isa na fad'a miki kiji to ki tabbatar kin biyo Dan Azimi kun n dawo gida a tare." Kashe wayarsa yay bayan ya gama maganarsa. Tun kafin ta zauna Mmn Sajida ke kallonta, tace"Najaatu yana ga jikinki a sanyaye ina fata ba wata matsala bace." A sanyaye tace"Abbah ne ya kira wai yanzu haka Dan Azimi nacan kofar gidanki yana jirana yace lallai dole sai na bishi mun koma gida a tare ni kuma wallahi bana jin zan iya binsa sai dai idan ya gaji da zama ya tafi bari ma kawai na kashe wayar ta kada ya sake kira. Mmn Sajida tace"A'a bada ni za'ayi wannan rashin hankalin ba, Najaatu ba zaki had'a kai dani ki 'batawa wannan bawan Allahn rai ba, tunda yace ki tafi to gaskiya yana da kyau kibi umarninsa kada ki nuna masa bai isa dake ba, haba keda kike nema ya mayar dake gidansa me zai sanya ki dinga yi masa gaddama akan dukkanin abinda zai umarceki kawai ki tashi mu tafi na tayaki hada kayanki ai mun gaisa kuma insha Allah muma zamu inda kike. Murya na rawa tace"Mmn Sajida korata kike a gidanki? Wai shin dan Allah idan na koma me zanyi masa zama fa kawai zanyi a gida shi kuma kullum yana gurin iyalinsa to ba gwara na zauna na samu nutsuwa ba." Mmn Sajida tace"Lallai ta yaro kyau tace bata qarko wallahi Najaatu baki da wayo har yanzu....Mutumin nan dafa baya sonki ba zai damu dake haka ba, yanzu dama kika samu a hannunki wacce zaki sake janyo hankalinsa kanki ta hanyoyi daban daban, baki da wayo wallahi har yanzu kiyi tunani akan shawarwarin dana baki jiya da daddare wallahi mutukar kin dauki shawara ta baza'a ja dogon lokaci ba zai kawo kansa gurinki. Najaatu tayi shuru tana nazarin maganar da Mmn Sajida keyi, " A sanyaye tace." Shikkenan Mmn Sajida zan gwada Daukar shawararki nagode sosai da kulawarki a kaina." Mmn Sajida tace"Babu komai wallahi aike yanzu 'kanwata ce duk abinda nayi miki ban fadi ba, saboda haka yanzu tashi muje ki shirya kayanki." Miqewa sukayi suna gyara mayafi, Mmn Ladi ta fito daga dakin mejego ganin sun miqe tace"Aa ina zakuje naga kun miqe."? A takaice Mmn Sajida tayi mata bayani...Mmn Ladi tace"Eh lallai haka shine yafi alkairi dake Naja'atu mungode kwarai da ziyara kuma insha Allah muma muna kan hanyar zuwa......Tare suka fita daga gidan Mmn Ladi har bakin titi ta rakasu sai da ta tabbatar sun hau adaidaita sahu sannan ta koma cikin gidan Dan Azimi na ganin saukar su Najaatu daga a daidata sahu ya shiga murna dama tun dazu wanda ya turo shi yake ta kiransa a waya yana tambayarsa yanda ake ciki sai bayan sun shiga gidan ne yay saurin kiransa ya fada masa cewa gata nan ta dawo nan ba da jimawa ba zasu dauko hanya. Abbah Abbas ajiyar zuciya ya sauke kafin yace.''To Alhamdullhi Allah ya kawo ku lafiya."......Najaatu cikin kunci da damuwa ta fito Mmn Sajida tasa mata jakar kayanta a motar dukkaninsu idan ka gansu za kagane suna cikin alhini na rabuwa da junansu Mmn Sajida sai daure zuciyarta take tana kwantar mata da hankali, sai bayan data shiga motar ne hawayen da take 'boyewa suka shiga zuba, hannu kawai ta daga mata ta kauda kanta gefe guda.....Dan Azimi na jan motar Mmn Sajida ta juya da sauri ta shiga gidanta tana goge hawayen daya 'kwace mata, Allah kenan mai had'a mutum da mutum. Dan Azimi sai hira yake mata ta shareshi haushinsa takeji kamar shine yay mata laifi to shima daya lura bata son hirar sai yaja bakinsa yay shuru kawai ya cigaba da fafara gudu a kan kwalta. daidai sanda suka shiga zaria Abbah ya sake kiran wayar Dan Azimin yana tambayarsa hanya, Yace."Gamu a zaria ai mun kusa isowa gida insha Allah." Abbah ajiyar zuciya ya sauke tare da fad'in "Allah ya saukeku lafiya.'' ya kashe wayar yana jin tamkar wanda aka yayewa dukkanin damuwar dake damunsa tabbas Tafiyar Najaatu garin jos ta daga masa hankali sosai dan gani yake kamar zata sake had'uwa da wani dan ta'addahn! ya yaudareta, shi da kansa a yanzu ya gazgata abinda ke damunsa a kan yarinyar ya daina wahalar da kansa da yaudarar kansa a kan cewar shi ba son aure yake mata ba so yake mata irin na uba da 'yarsa! Gaskiya da yayi nazari sosai ya gane ba irin wannan son yake mata ba, yarinyar ita da d'anta sunyi masifar tsaya masa a rai! kuma ya yarda da maganar Halisa inda take cewa samun nutsuwar sa Najaatu na kusa dashi, hakane tunda tun jiya yake cikin tararrabi gami da rashin kwanciyar hankali saboda tayi nesa daga inda yake, gabadaya haihuwar Zainab bata dameshi ba akan yanda ya damu da lallai sai Najaatu ta dawo gida. Sai wajejen tara da rabi na dare suka sauka.....Dama tuntuni ya gayawa Hajia cewa ya tura Dan Azimi ya daukota hajia ta dinga mamakinsa, sai dai tayi shuru kawai tana binsa da dukkanin abinda yake tsara mata akan tafiyar....Najaatu kukan takaici ta zauna ta nayi Hajia ta zauna tana ta rarrashinta da bata hakuri ita kuwa Yaya Ramlatu d'an ta dauka ta goya tana taya hajian rarrashin da take.........A ranar dai Najaatu bakin ciki da takaici tayi bacci dan taji bala'in haushin abun dan dai babu yanda za tayi ne. Sai da safe take jin labarin haihuwar Zainab a bakin Ramlatu tace Allah Ya raya abunda aka samu, Hajia tace"Idan anyi la'asar sai muje nima banje naga 'yar ba. Tace"To shikkenan Hajia Allah ya kaimu lafiya. To kamar yanda hajia ta fada hakane ya kasance bayan sunyi sallar la'asar a gida suka shirya tsaf suka nufi gidan masu jegon......Gate din Zainab cike yake da 'yan uwanta tamkar ma ranar ne suna Zainab famliy nasu suna da yawa shiyasa tunda akayi haihuwar suke shige da fice a gidan, mutum uku ma a gidan suka kwana kuma duk da auransu kawai daular gidan Zainab din ce take d'ibarsu suka zauna suna d'orawa da saukewa, 'Ya'yan sheik Nazifi 'Ya'yan malam kaqi halin malam ne yawanci su basu da hali mai kyau mazajensu na hakuri dasu mutuka, kuma mafi akasari almajiransa suke aure shiyasa suke rashin mutuncinsu iya san ransu sabida mazajen nasu najin kunya da nauyin tunkarar shehin malamin da wata magana, a cikinsu Zainab ce karama kuma itace ke auran Alhaji (mai kudi) shiyasa tunda suka zo suke zugata ga yanda za tayi ta gina kanta a gidan.......Harabar gurin Zainab yayi kaca kaca da kayan miya gefe katon kasko ne akan murhu wuta sai ci take anata soya nama tamkar ranar sallah. Ganin shigowarsu Hajian gidan yasa suka dan shiga nutsuwarsu cikin girmamawa suke shiga yi mata barka da zuwa, Babbar yayar su zainab din itace ta jagorance su har inda maijego take.....Zainab taci kwalliya tamkar wata amarya da babynta a hannu tana shayar da ita cike da murna takewa hajian barka da zuwa. Hajia Abu ta samu guri ta zauna a nutse Najaatu ma ta zauna kusa da ita tana kokarin kwance Daddy dake motsi a bayanta. Zainab ta miqawa Hajia yarinyar kana cikin neman gindin zama ta tsuguna har qasa tana gaishe ta....Hajia cike da farin cikin ganin Zainab da 'yarta kalau ta amsa tana fad'in "Sannu Zainab Allah ya qara miki lafiya tare da abunda kika haifa naji dadin ganinki kalau keda yarinyarki Allah ya rayata tafarkin addinin musulunci." Zainab na dan murmushi ta amsa tare da komawa ta zauna a gefan gado. Dakin ne yay shuru Zainab 'Yar rainin hankali wai jira take Najaatu ta gaisheta tayi mata barka......Najaatu kuwa tunda tayi mata kallo daya ta dauke kanta,babyn kawai ta kar'ba hannun hajia tana dubata gami da sa mata albarka, a tsakaninsu babu wacce ta kulawa kowa....Hajia tayi mamakin al'amarin kwarai da gaske kuma ta fahimci abinda yake da akwai sai tayi shuru da bakinta ba wai dan bata da abincewa ba sai dan ganin kamar shuru din da tayi shi yafi alkairi. Sun kai kimanin Mintina ashirin a dakin Zainab din kafi su miqe Hajia tace zasu shiga gurin halisa su gaisa." Zainab tace"To hajia nagode sosai Allah ya qara girma." Hajia ta amsa da ameeen sannan suka fita daga dakin. Yanayin yanda suka samu Halisa cikin damuwa yasa daga hajian har Najaatun suka tausaya mata, Halisa bata 'boyewa hajia abinda ke damunta ba sai da fad'a mata komai Hajia tace"Kada ta damu insha Allahu ita da kanta za tai masa maganar zuwa asibitin insha Allahu kuma za'a dace idan anje dan haka ta daina damuwa." Halisa taji dadin zuwan hajian sosai da sosai kuma tasan tunda tace zatayi masa magana to zai dauki al'amarin da muhimanci........Hajia da Najaatu basu jima sosai ba sukayi mata sallama suka fito, Halisa har bakin mota ta rakasu sai da direba yaja motar sannan ta koma gurinta tana jin sassauci a cikin zuciyarta amma hakika abinda 'Yan uwan Zainab sukeyi a gidan ya fara bata haushi 'barna da samun gurin da sukayi yayi yawa basu da hankali ko kadan kuma sun fito da kwadayinsu a fili kamar ba 'ya'yan fitaccen malami ba. To har dai yanzu abinda ke faruwa a tsakaninta dashi shike faruwa tunda ta dawo gaisuwa ce kawai a tsakaninsu daga ita babu wata magana sai dai kallo, watarana idan yazo tana zaune a falo barin falon takeyi bayan sun gaisa dan ta tsani munafikin kallon da yake mata wanda daga zarar yaga zasu had'a ido sai yay sauri ya dauke kansa, haushin hakan yasa take barin gurin inda shi kuma yake jin haushin hakan yafi so ta zauna yana dan kallonta ko yafi fahintar abunda suke tattaunawa da mahaifiyarsa. Ranar kwana biyar da haihuwa yasa Abdulhamid ya kai kayan barka gidan Alhajin kamar yanda hajia ta umarceshi....akwati uku manya shaqe da kaya sai kace amarya, akwatin babyn ma guda daya ce amma na Zainab har uku....ita kanta hajian sai da tayi mamakin abun harda set din gold masu nauyi da tsada!....Ya Ramlatu ta dinga masifa da fad'in "Wannan kayan sunyi yawa kuma basu dace da yarinyar ba haba sai kace hauka bayan lefan da akayi mata saboda ta haihu sai a sake yi mata wani. Hajia ta katseta da fad'in " Ke bana son ganin ido dan Allah ko wace haihuwa da goshinta meye dan anyi mata ai haihuwar fari ce saboda haka kada na sake jin wannan magana duk abinda zainab ta samu rabonta ne. Ramlatu tace"Hajia duba fa kiga wannan uwar sarqa ki daga kiji nauyinta anya Abbas yana sane yake 'barnatar da dukiyarsa bayan ga 'ya'ya ya fara tarawa abun yay yawa." Hajia tace"Ni dai nace ki bar maganar nan kome zainab ta samu rabonta ne saboda haka ki hada komai a inda yake anjima da yamma sai kuje ku kai musu." Ramlatu shuru kawai tayi tana mamakin al'amarin.....To itama Najaatu nata 'bangaran sai da taji wani iri daurewa kawai tayi tana kokarin cire kanta daga abinda be shafeta ba amma ita kanta wannan set din gold din ya bata sha'awa sosai.... *Littafin na kudi ne....!* Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya ga yanda abun yake.....Vip gruop#600 normal group #300 account... 0542382124...Binta umar gtbabk WhatsApp number *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* *MADADI 76_77* Abinda su hajia basu sani ba shine tun ranar kwana biyu da haihuwar Zainab ta tisa shi a gaba ta dinga lissafa masa abubuwan da take so, Allah sarki Abbah sarkin adalci sai yace to ta fada masa iya adadin kudin da take bukata, bata fada masa a ranar ba sai ta bari babbar yarta tazo ta fad'a mata inda ita kuma kai tsaye tace"ki fada masa dubu dari biyar zai baki. Zainab tayi shuru tana mamakin uban kudin da yayartata ta tsuga! tace."Anya aunty kudin basuyi yawa ba."? Murmushi tayi tace"Idan miliyan kikace kina bukata yana da ikon da zai baki mijinki fa yana da kudi ne wanda be san a dadinsu ba meye a ciki dan ya baki dubu dari biyar 'ya guda fa kika haifar masa darajar dan mutum yafi komai." Zainab tace"To zan gwada nagani anty bana so yaga rashin hankalina wallahi. Tace"Baki da wayo zainab na fada miki fa yanzu ne lokacin ki amma tunda kina ganin kamar wani abu shikkenn kanki zaki cuta ba wani ba, yanzu idan ya baki kudin nan sun isa ki siyi komai na qawa da kece raini ke har sai sunyi miki saura sai ki ajiye a account dinki kyayi wata bukatar dasu Zainab tace"To shikkenan bari ya shigo da daddare zan fada masa." Zainab tayi mamaki lokacin data fada masa a dadin kudin da take bukata yace babu matsala zai saka mata a account dinta in yaso duk abunda take bukata baby ke bukata sai tasa 'yan uwanta su cire kudin su siya mata.......Zainab yana fita ta dinga murna da farin ciki kanta na sake girma tana tunkaho da cewar ita din 'yar gaban goshi ce wannan zunzurutun kudin da ya bata tayi hidimar haihuwarta yasa ta daina jin haushin abubuwan da yayi wa Najaatu a lokacin data haihu, ta tabbata kyauta da hannun bayarwa a jinin jikinsa yake......koda yan uwanta suka zo ta nuna musu shedar kudin a wayarta sai suka dinga mamaki! wasu daga cikinsu har sai da hassadar su ta fito fili, babbar yarsu aunty Hauwa tace"To sai ki bani Atm din ki naje da kaina zan had'o miki kaya na alfarma wanda zaki fita kunya dashi ranar suna." haka kuwa akayi aunty Hauwa yayar Zainab itace duk ta had'o kayan barka saboda tsabar rashin hankali duk ta qarar da kudin gurin siyawa 'yar uwarta kayan banza da wofi amma baby ta tashi da akwati daya itama ba wasu kayan kirki ne a ciki ba. Ita kanta Halisa da aka kai kayan ta shiga ta gansu sai da tayi mamaki! daurewa kawai tayi ta dudduba tasa albarka ta nufi gurinta, aikuwa tana fita 'yan uwan Zainab suka shiga dariya kowa na fadin albarkacin bakinsa akanta wai 'yar bakin ciki ce hassada tasa ta kasa zama ta duba kayan a tsanake, ita kuwa zainab sai wani figala take tana fad'in ita waye yasan abunda akayi mata a baya saboda haka taje tayi ta hassadarta idan ma mutuwa za tayi ta mutu babu ruwanta.'' Babu wanda yay mata fadan arziki sai ma qara zugata da suke idan tayi arbain tace ya siya mata mota. kai tsaye tace"Dama ai yanzu abinda yake gabana kenan naga ina hawa babbar mota wacce tafi ta Halisan kudi da girma." Halisa kuwa sa masa ido kawai tayi taga iya gudun ruwansa, shin ita da yara me ya tanadar musu na fitar suna ai ko turaman atamfofi ya kawo musu suma su sanya, tun ranar da sukayi cacar baki akan Najaatu suke sama sama da juna dan haka ana ya gobe suna ta same shi yana shiryawa zai fita tace"Naga kayan barka na Zainab sai nace to mu ina namu kayan fitar suna ni da yara." Ba tare da ya kalleta ba yace."Kinyi magana kina bukata ne? Tace"Sai nayi magana zaka san abinda ya dace a qallah dai ai muma ka kawo mana namu ba sai nayi magana ba tunda muna da hakki. Yace."Itama bani naje nayi mata siyayya ba dan bani da lokaci kudi na bata kuma kin san dole ayi mata hidima tunda haihuwa tayi." Tace"Ina ruwana da haihuwa tayi ni ina maka maganar akan hakkina da yara na." Afusace! yace."Ke! Halisa ba zanyi ba! uwata ce ke zaki sani a gaba kina nuna min abunda ya dace to ba zanyi ba nace! kusa wanda kuke dashi." Yana gama maganarsa ya buge rigarsa tare da daukar wayoyinsa ya qara gaba....Halisa ta jima tana mamakin wannan al'amarin ta dinga tunanin hukuncin da zata dauka a kansa, miqewa tayi a guruguje tayi wanka ta fito ta shirya key din motarta ta dauka ta kama hanyar fita Daidai kofar gate din Zainab ta dinga jiyo hayaniyarsu sai shewa sukeyi da fad'in gobe har d'an asharrale zasu dauko su cashe! Motar ta kawai ta shiga ta fita daga gidan, kai tsaye kofar na'isa ta nufa. Lokacin data isa gidan Hajia da Ramlatu na zaune a palo suna hira Najaatu na daki tana bacci....Halisa ta samu guri ta zauna fuskarta a ba'ce! Hajia tace"Halisa Allah yasa dai lafiya na ganki da tsakar rana ina fata dai ba wata matsala bace.....Halisa kasa magana tayi sabida tunda take bata ta'ba kawo kararsa gurin iyayensa ba ba dan bayayi mata laifi ba kawai tana hakuri ne amma hakika yau ya kaita bangon makura....Ta gaida hajian murya na rawa ta shiga sheda mata abunda yake faruwa, Tace"Saboda nace ya mayar da Najaatu gidansa yake jin haushina kullum babu kalma mai dadi to yau dan nayi masa magana akan hakkina dana yara ya farfad'a min magana iya son ransa Hajia wallahi ina hakuri da halin Abban mufida ina ganin zan tafi gida kawai na bashi guri." Hajia tayi shuru tana nazarin maganar Ramlatu kuwa hasala tayi tace"Ai wannan yarinya fitinanniya ce wallahi watakila ma ita ta hanashi yay muku komai aini tunda ta zugashi ya dauko min police ta fita daga raina, kuma haka kawai saboda kin bashi shawarar arziki sai ya dinga jin haushinki to meye da Najaatun da yake gudunta." Najaatu jin hayaniya a falo yasa ta fito daga daki ta samu guri ta zauna tana kallonsu da so ta fahimci inda maganar ta dosa.....Halisa tace"Wallahi kuwa Yaya Ramlatu Abban Mufida wani iri ne yana son abu amma sai ya dinga nunawa baya so saboda nace idan ya tsaya wasa wani zai aureta duk da jegonta shine fa yake Jin haushina." Hajia tace"Duk dai yanzu magana ta kare kiyi hakuri ki koma gida kada ki tafi gidanku idan yazo da yamma zanji dalilinsa na danne miki hakki maganar zuwa asibiti dama munyi dashi kancewar sai bayan suna hankali ya kwanta zai kaiki yace watakila ma dubai zakuje a dubaki sosai." Jin wannan magana da hajia tayi yasa Halisa taji sassaucin akan bacin ran dake zuciyarta sai ta miqe tana gyara mayafinta da fadin ita zata tafi." Hajia da Yaya Ramlatu suka sake tausarta akan kada tace fa zata je gida ta koma dakinta, nan ta tabbatar musu da cewar gidan zan ta koma insha Allah....Bayan fitar Halisa Najaatu tunani ta shigayi ta fahimci maganganun da Halisa takeyi a kanta wato saboda tace masa ya mayar da ita yake gaba da ita to ita kuwa wace iriyar kiyayya yake mata da har zai dinga gaba da wani a kanta.....Allah sarki Halisa ashe yanzu tana kaunarta tunda gashi har tana cewa mijinta ya dawo da ita. jin hawaye na kokarin su zubo mata ne yasa ta miqe da sauri ta bar gurin. Hawaye na sauka a kan kumatun ta ta zaune gefan gado tana tunanin abinda zai taimake ta, gabadaya ji tayi zaman gidan Alhajin ya fita daga ranta, ba dan komai sai dan tayi nesa dashi da duk abinda ya shafe shi tana ganin idan ya daina ganinta sai tafi martaba da daraja a idonsa, me yay zafi da har zai dauki fushi da gaba akanta ashe dama haka kiyayyar ta tayi girma a zuciyarsa........... yanzu idan tace zata koma gidan Malam su hajia hankalinsu zai tashi kuma ba zasuji dadi ba sannan zasu dinga tunanin ko wani abun suke mata na rashin kyautawa yasa take gudun zama dasu, amma da badan hakaba da wallahi barin gidan za tayi domin ba taga amfanin zamanta a ciki ba Tana wanka tana tunanin maganarsu da Mmn Sajida....Itafa gani take dukkanin wani abu na jan hankali da za tayi masa bai zama lallai ya kalleta da qima da daraja ba , amma dai tana ganin zata kwatanta yin wasu abubuwan ko Allah zai sa a dace. Shiryawa tayi tsaf! ta fito ta samesu har yanzu suna falon suna tattauna maganar, sai ta nuna tamkar ba taji abinda suke magana a kai ba.....Hajia tace"Ya na ganki da hijabi ko gidan Malam zaki shiga."? Tace"Eh inaso na shiga mu gaisa bayan na dawo daga gidan Lalle ('Kunshi) inaso nayi kwalliyar suna." Hajia tace"Aikuwa yana da kyau hakan to da akwai kudi a gurinki ne." Tace"Eh akwai wanda zasu ishe ni." Yaya Ramlatu tace"To ko zaki bar Daddy a gida kyafi samun nutsuwa gurin zaman kunshin." kokarin kwanto yaron take daga bayanta tana fadin " Aikuwa kin kawo shawara mai kyau Yaya Ramlatu dan yana iya rikice min da rigima ya hana lalle na yayi kyau. Yaya Ramlatu ta kar'be shi da zanin goyonsa ta miqe tana kokarin goya shi a baya tace"Ai har kyaje ki dawo yana baya idan ya tashi a bacci sai a dama masa madara." Hajia tace"Duk da haka dai kada ki zauna kada a shiga hakkinsa." Tana kokarin fita tace"Insha Allah bazan jima ba zan dawo. Gidan Lallen kabuga ne kuma lokacin da taje akwai mutane dan ma mai lallen kawar Salimat ce budurwar Salim wacce a lokacin auranta da Bash yasa ta gane gidan.....Dalilin wannan sanayyar yasa Bilki mai kunshi ta tsallake mutanan dake gabanta ta kama kafafun Najaatu tana yi mata, aikuwa jamaar dake gurin suka dinga surutu kowa na ganin an shiga hakkinsa....Tace" Dan Allah kuyi hakuri na bar karamin yaro ne a gida kuyi min uziri.'' jin haka yasa wasu suka daina magana wasu kuwa fushi sukayi suka tafi.....Bilki ta dauki lalle mai tsayi da ado da yawa, Najaatu tace"Bilki da kinyi min takaitacce tunda kinga akwai jamaa a gabanki." tace"na riga na dauki mai ado dole kema sai kin jure zama.'' shuru kawai tayi ta zubawa kafafunta ido wanda bilki ke zane su da jan lalle. Kafafuwa da hannuwa akayi mata jan lalle mai kyau da burgewa sosai kunshin ya dauki hankulan jamaar dake gurin suka dinga so ayi musu irinsa. Sai bayan biyar da Rabi na yamma sannan ta cire lallen ya wani fito rad'au a kafafunta na hannun ma yayi abun burgewa, Najaatu sosai tayi farin ciki da yanda Bilki ta fito da ita kamar wata amarya.....Dubu biyar ta bata saboda jin dadin abinda tayi mata bayan haka kuma zuwanta yasa wasu costoms din sun tafi shiyasa ta bata wannan kudin...............Ta jima a bakin titi tana neman abun hawa bata samu ba, da yake yamma tayi duk 'yan kasuwa sun tashi tun daga mandawari ake fama da goslow har titin kabuga gurin ya had'e sosai masu motocin gida dana haya kowa na kokarin wuce wa, da kyar ta samu a daidaita sahu wanda zaije kofar na'isa amma kuma duk maza ne a ciki su biyu.....Ganin bata da mafita yasa kawai tayi kundubala ta shiga, aikuwa samarin nan suka dameta da hira da yake aboki da aboki ne duk a tunaninsu sun dauka budurwa ce wai dan Allah ta basu number wayarta, Najaatu shuru tayi musu tayi bala'in shan kunu! na kusa da ita ne ya kalli hannunta data dora a jikin k'arfen adaidata sahun yace"Baby wannan lallen yay kyau nawa ne kudinsa na biya gaskiya kina da kyau gaki da aji wallahi kin burgeni kuma ina shaawar auranki." Tace"Kai dan Allah ku kyaleni da surutu lalura ce ta fito dani kuma ni ba budurwa bace matar aurece. Dariya kawai sukayi suna fadin"Aikwai 'yan mata irinki da yawa masu kiran kansu da matan aure amma basu bane matar aure ta fita daban baby....Takaici yasa tayi musu shuru tana Allah Allah ta sauka.....kawai sai taji suna cewa mai adaidata sahun kada ya saukesu a inda zasu sauka suna so su rakata gida....Gabanta ya fadi ta kallesu rai a bace tace"Wallahi zaku janyowa kan ku wato na fada muku ni matar aure ce kuna gaddama ko okey." Daga haka sai kawai taja bakinta tayi shuru ta kyalesu tana jinsu suna ta dariya da surutai a kan maganarta. Ana kokarin shiga massalaci domin sallar magariba adaidaita sahu ta tsaya a kofar gidan alhaji.....Motar Abbah Abbas da taga ni a fake a inda ya saba ajiyewa yasa gabanta ya tsananta faduwa. Tana kokarin dauko kudi a jakarta ya fito daga gidan Alhajin fuskarsa tamkar hadarin dake dab da zubar da ruwa, tunda yazo gidan ya samu yaro na kuka da neman uwarsa ransa ya 'baci ya tambayi Yaya Ramlatu ina take? tace Ta tafi gidan kunshi.....Ai sai ya shiga surfa mata masifa kamar ubanta harda cewa rashin hankali ne da zata kama d'aukar yaro ta rabashi da uwarsa yini guda saboda haka ai sai ta daukeshi ta kaiwa uwarsa kada su kashe shi." Ya Ramlatu ta dinga mamakin tsawar da yake buga mata sai so take ta fahimtar dashi yaki fahinta wai itama ta mayar da kanta karamar yarinya mara tunani, Hajiya da taga abun nasa naso ya wuce gona da iri tace"To wai kai ina ruwanka ne? ko auran yarinyar nan kake da zaka takura mata kunshi ta tafi domin ta gyara kanta kuma bamu dauka yaron nan zai tashi ya dinga rigima irin hakaba itama watakila rashin abun hawa ne ya tsayar da ita dan haka abar maganar haka uwar yaron itama nasan tana can hankalinta a tashe.......Cikin wannan 'bacin ran ya fito daga gidan sai kuma yaci karo da wani dan samarin nan sun kewaye ta sun hanata wucewa wai sai ta basu number.... Ganinsa yasa ta kid'ime! pose dinta ta fad'i ta sunkuya dauka saurayin shima ya tsuguna hannunwansu ya hadu guri daya. tana dagowa ta wanka masa mari jiki na kyarma ta dauki pose dinta ta barsu a gurin....Komai a kan idonsa ya faru yana kallonta tana tawowa yana ji kamar idan ta karaso yayi wurgi da ita saboda jin wani mahaukacin kishi dake taso masa, gifta shi tayi da sauri ta tura karamar kofar gidan ta shiga gabanta sai wani irin bugawa yake......matasan samarin nan kuwa adaidata sahun suka shiga takaici kamar ya kashe su su basu samu number ba gashi sun sha mari amma babu komai tunda sunga inda ta shiga watarana zasu kawo mata ziyara dansu basu yarda matar aure ce....Abbah sai da yaga Adaidata sahun ya bar gurin sannan ya wuce cikin massalaci yana jin wani irin zafi a cikin zuciyarsa. Najaatu na shiga gidan taji yo muryar daddy nata zabga ihu! da sauri ta shiga falon ta tarar dasu sunyi cirko cirko hajia rabi na rike da waya a hannunta tana kokarin nemo number.....Sallamarta yasa duk suka kalli bakin kofar shigowa Ya Ramlatu ta karasa gurinta da sauri ta miqa mata yaron da fadin"Kar'beshi kada azo a tafi dani yanzu yanzu aka gama cin mutuncina." Hajia Rabi tasa dariya da fad'in "Wallahi Ramlatu baki da dama waye zai tafi dake."? Rike baki tayi tace" Haba Hajia kina kallonsa fa ya dinga zazzaga kamar zai doke ni ke kyace shine yake gaba dani wallahi Abbas ya raina ni sosai amma babu komai. Najaatu taji tausayinta ya kamata tace"Dan Allah Yaya Ramlatu kiyi hakuri wallahi dana san zan dade gurin k'unshin nan da na tafi da yaron nan yau goslow akayi sosai da kyar ma na samu abun hawa." Hajia tace"Nima sai da na zargi haka wallahi to me yasa baki kira Dan Azimi yazo ya daukeki ba." Tace"Gabadaya hankalina bai kai nayi tunanin hakaba wallahi. Hajia Rabi tace gashinan kuwa kwalliya ta biya kudin sabulu kunshin yayi kyau sosai da sosai." Najaatu ta nemi guri ta zauna tana kokarin ciro nono tasawa yaron a baki tace"Wai ma duk da haka akwai wanda suka rigani darajar Salimat budurwar Salim naci akayi min da wuri." Hajia Rabi tace" lallai zuwa gidan 'kunshin sai mutum yayi da gaske...Hajia tace"Aikuwa dai kafin ayi kwalliya sai an ji jiki mu lokacin mu idan muka daure kafafun mu da lalle shikkenan bukata ta biya mu wayi gari rad'au damu amma zamani yanzu komai ya sanja Allah ya kyauta." tana ta gama maganarta miqe da niyyar zuwa tayi sallah Yaya Ramlatu da hajia Rabi ma tafiya sukayi sallah suka barta ita kadai a falon tana shayar da d'anta tare da tunanin irin kallon da taga Abbah Abbas nayi mata a d'azu! yanda taga fuskarsa a murtuke yasa dik hankalinta ya tashi tana tsoron ya shigo yay mata fad'a. Tana kokarin barin falon ya shigo....Tayi saurin sunkuyar da kanta gabanta na fad'uwa. Nasa 'bangaran ganin nonota guda a bayyane yasa hankalinsa ya tashi sai yaji gabadaya ma yana nema ya rasa karsashinsa....Najaatu sam ta manta tana shayar da d'anta nono shiyasa bata gyara ba, Da kyar ya karasa shigowa yana ta bin ta da kallo 'kunshin dake kafafunta da hannayenta ya tsirawa ido, yayi masa kyau a ido, dauke kansa yay daga kallon kafafunta yay gyaran murya kamar koda yaushe Yace."Najaatu wane irin rashin hankali da rashin imani ne yasa zaki tafi yawon banza ki bar yaro karami irin wannan a gida yay ta kuka kin san hakkin d'an adam kuwa."? A kausashe yay maganar....Ta dan kalleshi tana zum'bura baki tace"Abbah ba yawo naje ba naje gurun 'kunshi ne." Da sauri yace."Wa kika ajiye da zakiyi wa kwalliya ko kina da miji ne."? Gabanta ya fadi ta kalleshi tace"Sai ina da miji zanyi kwalliya ai mace da ado aka santa." Yace." Sam Ban san da wannan maganar ba kawai dai kin fita ke kad'ai ne dan ki samu samari kuma na gani kin samo to mutukar yawo zaki dinga fita kina barin yaro zan samu Baba malam na sheda masa abinda kikeyi nasan shi zakiji maganarsa tunda ni kin raina tawa maganar saboda kina samun daurin gindi a gurinsu hajia! dan haka wannan itace maganata ta karshe da zanyi miki kada ki kuskura ki kara barin yaro a gida ki fita yawon zagayen samun zawarawa." Kuka take sosai tace"Wai dan Allah Abbah wannan wace irin magana kake kana kallon 'kunshi fa a kafafuna amma kake cewa ina tafiya yawon samo zawarawa ashe har sai na fita zagaye bazawari zai biyo ni ni ba'irin wannan zawarawan bace ko yanzu nayi niyyar aure sai nayi saboda inada wanda zan aura a hannu." Ta fadi wannan maganar ne danta tunzura shi, aikuwa ya tunzuru ya dinga zazzaga mata fad'a da fad'in "kamar shi zata sashi a gaba tana yi masa rashin kunya to zai fita harkar ta tunda ta zama 'yar kanta, fad'a yake mata sosai harda miqewa tsaye kishi na nema yasa ya fad'i a gurin. Hajia ta sauko daga sama da sauri tana fad'in "me yake faruwa ne wannan fad'a da kake yi kwana biyu ya isa fad'a a gida fad'a a inda bai dace ba to ita kuma Najaatu mai tayi maka."? Zama yay kan kujera yana numfarfashi, ya cire hularsa ya ajiye kawai ya shiga girgiza kafafunsa....Najaatu daukar d'anta tayi ta bar gurin tun kafin zuciyarta tayi bundiga.....Hajia ta kalleshi tana so ya samu sassauci ta fad'a masa hukuncin data yanke dan ta gaji da wannan hargagin da yake....... 78***Hajia sai da ta tabbatar da cewar ya dawo cikin hayyacinsa sannan ta fara magana kamar haka." 'Dazu da safe Halisa tazo gidan nan cikin 'bacin rai tare da qudirin tafiya gidansu akan abubuwan da kake a gidanka na rashin kyautawa to naji ta banki ta kuma na rarrasheta tayi hakuri ta koma gida inaso kai ma yanzu naji ta bakinka kan abunda ke faruwa a tsakaninka da ita." Shuru yayi yana mamakin maganar Halisa ta kawo shi qara gurin mahaifiyarsa akan wani dalili me yay mata mai zafi da zata kawo kararsa gaban mahaifiyarsa, Hajia ganin yay shiru yasa tace"Kai nake saurare." Ajiyar zuciya ya sauke kafin yace."Hajia a zahirin gaskiya ni ban san abinda nayi mata wanda ya sanya har ta kawo miki ka'ra ta wannan shine dalilin da yasa kika ga nayi shuru ina mamakin maganar saboda d'azu da safe lafiya lau muka rabu na tafi kasuwa. Hajia tace"To ita kuma tace min akan tace ka mayar da Najaatu gidanka ne kake jin haushinta wanda dalilin wannan maganar da tayi maka yasa kake gaba da ita sannan baka siya mata abin futar suna ba." Shuru yay bakinsa ya mutu lallai Halisa bata da kirki shi zata tonawa asiri baiyi tsammanin zata iya kawo kararsa akan wannan dalilin ba, tabbas daya san abinda zata aikata kenan toda ya tsaya ya saurareta sun rabu lafiya, duk sanda zai tunu da furucinta a kan Najaatu sai yaji wani irin mugun haushinta ya rufeshi shiyasa ya watsar da lamarinta ya'ki siya mata komai ya kuma ki bata kudi duk da yasan zata bukace su domin tayi hidimar haihuwar Zainab dasu. Hajia ta cigaba da cewa''Yanzu meye laifin Najaatu da har zaka dinga gudunta haba kai kuwa! wallahi mu duk mun dauka kana da qudirin mayar da ita dakinta dan ganin irin hidimar da kake mata ashe kai ba haka abun yake a zuciyarka ba, menene abun gudu a tare da yarinyar kayi hakuri ka tausaya mata ita da d'anta ka mayar da ita dakinta komai ya wuce ni a matsayina na wacce ta haifeka nake baka umarni akan haka Najaatu matar arziki ce sannan dukkanin abunda ya faru tsakaninka da ita qaddara ce da rabon wannan yaro da take goye dashi, dukkaninmu idan yarinyar nan ta koma dakinta sai munfi farin ciki akan ta sake wani auran.......Sannan sai magana akan Halisa inaso itama kayi mata abunda ya dace duk da ba itace ta haihu ba yana da kyau kayi mata wani abun wanda zai faranta zuciyarta haka akasan adalin namiji." Abbah Abbas kasa cewa komai yayi dan gabadaya Hajia ta gama kashe masa jikinsa da maganganunta tabbas bashi da yanda zaiyi ya bijirewa umarninta dole ne ya mayar da Najaatu dakinta tinda ta riga ta umarce shi....Hularsa ya dauka yasa yace."Shikkenan Hajia tunda kin bukaci da ayi hakan za'ayi insha Allah ina rokon Allah yasa hakan shine alkairi maganar Halisa kuma idan na koma gida zan zauna da ita insha Allah. Hajia tayi murmushin jin dadi tace"To nagode sosai da wannan alfarmar da kayi min baka bijirewa umarnina ba naji dadi kwarai da gaske ina maka fatan alkairi tare da samu farin ciki har karshen rayuwarka. Ya amsa da ameen ya rabbi hajia babu wani abu da zaki nema a gurina na kasa yi miki saboda nasan kome na zama a duniya ta dalilinki ne da tasirin aduoin da kike min saboda haka insha Allah Najaatu zata koma dakinta kamar yanda kika bukata amma inaso yaron yay wayo tukkuna sai ayi maganar daurin aure." Hajia tayi shuru tana nazarin maganarsa Eh hakan kamar shine maslaha amma kamar za'a ja dogon lokaci....Tace."To shikkenan hakan yayi Allah ya nuna mana lokacin da zata yaye yaron sai a d'aura auren ko kuma dai za'a daura auran kawai sai tayi zamanta a gida idan ta yaye yaron sai ta tare." Yace."A'a bari dai ta yaye shi tukkuna ina ganin hakan kamar sai yafi.'' Baya so taje ta dauki ciki ga k'aramin goyo yaron zai iya lalacewa shiyasa yace haka....To itama hajian ta fahimci abinda yake nufi sai tace"To Allah ya nuna mana....Miqewa yay tare yi mata sallama, a sauka lafiya tayi masa tare da bada sakon gaisuwarta gasu Saddaqa........lokacin daya shiga gidan samun Halisa yay a qame a kujera tayi kici kici da fuska, tsaf ta shirya masa da duk wani tashin hankalin da zai shigo dashi Ganinta cikin shirin ko ta kwana yasa ya sassauta fuskarsa domin baya neman wani bala'i yaji ma da wanda ya shigo dashi gidan, sai kawai ya shige dakinsa ba tare da ya tanka mata ba. K'wafa tayi tana girgiza kanta ta dauka zai shigo da bala'i sai taga akasin hakan tayi murmushi cikin zuciyarta tace"Ashe abun rainin hankali ne da samun sake to daga yanzu idan kayi min abunda be gamsar dani ba xan tunkari mahaifiyarka na fada mata magana ta qare...'Kin tashi tayi tabi bayansa har ya gama abunda yake ya fito cikin jallabiya ruwan toka....Kusa da ita ya zauna yana kallonta yace." Abunda kikayi kin kyauta kenan? abunda ba kiyi da kuruciya ba shine yanzu saboda shashanci zakiyi gabadaya kishi ya rufe miki ido kin manta ke irin abubuwan da nayi miki a baya sabida kawai kinga kayan haihuwar Zainab kin tashi hankalinki harda zuwa ki fad'awa hajia laifina bana muamular arzki dake saboda kince na mayar da Najaatu naqi shine nake gaba dake ko? Kallonsa tayi tace"Ai ba qarya nayi ba baka kulani baka cin abincina" Yace "cikin nida dake waye gaba da wani? wa ya cancanci ya d'urkusuwa dan uwansa". Murmushi tayi tace" Abinda yake faruwa kenan tsakanin ma'aurata wai dan Allah Abban mufida me yasa kuke da iko ne sau nawa ina maka magana ina girki ina ajiye maka baka ko saurarata ballantana kaci abincina akan kawai na baka shawarar arziki ashe kai so kake nai ta binka ina baka hakuri alhalin ni na nayi maka alkairi ka mayar min da sharri wallahi banga laifin da nayi maka ba wanda zai sanya nayi ta baka hakuri ba." Yace."Ya isa haka! maganar dawo da Najaatu ce dai duk ta janyo wannan abu to sai hankalinki ya kwanta hajia ta bani umarni na dawo da ita shikkenan magana sai ta qare.Tace"Abbahn mufida kenan koda hajia bata baka umarni ba to kai zaka bawa kanka umarni dan haka kamar yanda kace a bar maganar an barta kai da Najaatun ina muku fatan alkairi tare da zaman lafiya mai d'orewa.....Cikin ransa ya amsa da ameen kafin gurin yay shuru na minti uku...Gyaran murya yay yace."Yanzu me kike bukata." Tace"Yanzu kuma lokaci ya qure ai gobe suna mai zanyi da kudi." Yace duk da haka hakkinki ne ai ko bayan suna zaki iya amfani dasu ta wata hanyar sabida haka kema zan sa miki kudi a account d'inki shikkenan na fita kada ki sake zuwa kice ina tauye miki hakkinki dan ni duk neman da nake akan iyalina nake banga abunda zai hanani na faranta muku rai ba." Halisa akayi murmushi ana wani girgiza jiki "To nagode sosai Allah ya qara budi na alkairi." Amsawa yay da amin ya miqe tare da fad'in zai shiga gurin Zainab ya dubata. Ba tace masa komai ba har ya fita daga dakin, lallai zuwa gurin hajia yayi mata amfani tunda gashi nan ya zauna suna maganar arziki babu hayaniyar daya saba. Zainab maijego tayi shar shar da ita, mai kitso da lalle ('kunshi) har gida tazo tayi mata kitson attaccement mai uban yawa sannan akayi mata jan lalle da baki gabadaya faratan ta tasa musu (jan farce) sai kace wata inyamura dan gabadaya kammanin ta sun sanja......Tana zaune ita da masu taya ta zaman jego sai hira suke tare da shirye shiryen yanda shagalin bikin suna zai kasance dan har sun biya mai d'an Asharrale (DJ) kudi zai zo da yamma ya baje kolinsa, abunda sukeyi tamkar ba 'Ya'yan shehin malami ba. Ganin ya shigo dakin yasa suka shiga gaisheshi suka fita daga dakin da sauri. Zama yay kusa da ita yana kallonta cike da mamaki yace."Wannan wane irin kitso ne akanki irin na arna shin nauyin abinda akayi miki kitson dashi baya damunki sannan kin saka wani abu a faratanki ko kyau ba suyi miki ba, dan Allah idan za kuyi kwalliya kusan irin wacce zaku dinga yi. Zainab jikinta yay sanyi jin yanda ya gwale mata kwalliyarta sam bata dauka zai ga rashin kyawunta ba kasancewar ta sanshi shi ma'abocin san ado ne. A sanyaye tace"Ai sabida nasan bana sallah yasa nayi kitson attachment sannan nayi ado da jan farce. Yace."Duk da haka zaki gayyato shedanu jikinki wannan kwalliyar da kuke ita kesa sanyawa abubuwa da yawa su faru daku ina laifi ma da kikayi 'kunshi amma meye na rufe farcenki da wani jan abu." Zainab tayi shuru yace."Gobe da safe ki kankareshi dan baiyi miki kyau ba sannan wannan uban gashin dokin da kika sa a kanki ana gama taron suna ki kwance shi bazan lamunci shigowar shed'anu gidana ba. Tace"Abbah Mufida kitson nan ansha wuya kafin ayi kuma dubu kusan ashirin na biya akayi min ya za'ayi kace na tsefe! Yace."Babu ruwana da kudin da kika biya ni dai umarni na baki." Zainab ta shiga halin damuwa, babyn dake kwance a kusa da ita ya dauka ya dubata sosai ya ajiye ta tare da miqewa hanyar futa ya nufa....Tace."Abbah Mufida dama ina so na fad'a maka cewar su aunt Hauwa sun gayyato mai DJ zai zo yay mana da yamma." Yace."Waye me DJ. "? Kai tsaye tace" Ina nufin mai Dan Asharrale inaso ka bani kudin li...... katse ta yay da sauri yace"A gidan nawa za'a buga min DJ."? Dawo yay ya tsaya a kanta ya wani tamke fuska yace"Wai shin Zainab kin manta daga inda kika fito ne na lura gabadaya dake da 'yan uwanki duk shagalallu ne kun fito daga tsatso mai kyau amma kuna neman ku shagala wannan abubuwan da kuke na tabbata Ya sheik bai sani ba to ni da kaina zan sanar masa dan ni ba irin shashashan mazan da 'yan uwanki ke aura bane in banda rashin hankali har ki dube ni kice zaki kawo min 'Dan Asharrale yazo yay me? To kada ki kuskura wallahi tun wuri su da suka gayyoto shi su dakatar dashi dan mutukar yazo min gida sai na daureshi sannan kema na baki mamaki." Zainab ta dinga kuka tana bashi hakuri tsabar 'bacin rai yasa ko sauraranta baiyi ba ya kada kansa ya fita da dakin yana mamakin al'amarin ashe da yarinyar nan bata fad'a masa ba da sai dai ya samu labarin zuwan Dan Asharrale gidansa. da kuwa ya dauki tsatstsauran mataki a kanta dan ba zata kawo masa bidia a gida ba. Washe gari ranar suna yarinya taci sunan kakarta Hajia Zainab (Abu) sai ya kasance Yarinyar ta amsa sunan mamanta da kakarta amma dai shi uban 'yar sunan babarsa yasa kai tsaye kuma yace a dinga kiranta da Ummi Hajia taji dadin samun takawara ta dinga murna tare da adduar Allah ya raya mai sunanta..........Bangaran Najaatu kuwa da tayi alkawari kan cewa babu inda za taje, sai kuma daga baya tayi wani tunani tayi sauri tayi shiri na mussaman ado da kwalliya tayi mai k'ayatarwa ta fito falo tana zabga kamshi turarruka masu kamshi da daukar hankali... Nan ta samu Ya Ramlatu da wasu daga cikin Family din Hajia suna zaune ta gaisa dasu a mutunce! Ta kalli Ramlatu da fad'in." Ba yanzu zamu tafi bane."? Ya Ramlatu tace"ko kawai kibi hajia Rabi ku tafi kada rana tayi ni zan jira zuwansu Hajia Rakiya sai mu had'u gabadayanmu mu biyo bayanku. Tace"To shikkenan, sama ta hau tayi sallama da hajia ta sauko Ya Ramlatu tace" Daddy tunda yay bacci a bayana to ki barshi kawai na tawo dashi. Tace"Kada fa ya tashi yayi miki rigima irin na jiya. Dariya ta d'anyi tace"Ba zai tashi ba insha Allah ai su Hajia Rakiyan suna hanya muma ba zamu dade ba zamu biyo bayanku. Tace to shikkenan sai kin tawo. Naja'atu tana sane ta yafa qaramin mayafi mara sirri ga yanayin dinki jikinta riga da siket sun matseta swiss les ne mai tsada amma tasa anyi mata matsatstsan d'inki! tana sane tasa kayan saboda tasan baya son suyi irin shigar su fita da ita.. Taji dadin ganin dukk motocinsa a harabar gidan da alama bai futa ba, kai tsaye bangaran maijego suka nufa.....'Yan uwanta ne duk a gurin suka gaisa a tsaitsaye suka wuce ciki. Zainab tayi kyau har ta gaji kana ganinta kaga matar Alhaji gold yaji a ko'ina ga wata uwar shadda tasa wacce taji uban surfani irin na manyan mata...Najaatu kallo daya tayi mata ta dauke kanta, kishi ne yake taso mata tana danneshi...To itama Zainab din nata bangaran ganin zahirin Najaatun ya firgitata jikinta yay sanyi dan bata ta'ba tsammanin cika da kasaitarta ya kai hakaba ashe cikakkiyar macace abar alfaharin ko wane da namiji lallai hijabi ba karamin sururta mace yake ba. Ta dinga satar kallon Najaatun tana jin wata shakkarta gabad'aya bata so ta had'u da mijinta dan kada ya 'kyasa (Maman Hanan kinga mutuniyar ki ko ???? sai kace tsinken sakace sai iyayin tsiya) Najaatu na hankalce da irin kallon da take mata sai kawai ta miqe da fad'n "Hajia bari na shiga gurin Aunty Halisa mu gaisa. Hajia Rabi tace" To shikkenan nima zan shigo yanzu insha Allah." Najaatu ta juya tana wata iyar tafiya ta taqama! Zainab kasa dauke idonta tayi daga kanta har ta fita daga dakin. Da sallama a bakinta ta tura kofar falon ta shiga, Abbah Abbas na tsaye a tsakiyar falon yana magana da Saddiqa Halisa kuma na zaune a kan kujera tayi ado daidai misali Mussadiq da Mufida na kusa da ita a zaune. Ganin shigowarta yasa yaran suka ruga a guje suka rungumeta suna murna...Halisa na murmushi tace"Najaatu ke kika fara zuwa kenan sannu da zuwa karaso ki zauna. A nutse ta riqe hannun Mussadiq suka karasa falon ta samu guri ta zauna a nutse ta kalleshi yana tsaye a inda yake yana mata wani irin kallo mai kama da harara ita tasan ko kallon menene sai ta basar tace"Abbah ina kwana? 'kin amsawa yay ya kalli Saddiqa da fad'in ta tashi maza taje gurin Zainab tace ta duba masa gilas d'insa a dakinta, Saddiqa tayi saurin miqewa domin tafiya aiken da yayi mata, Najaatu ba tayi zuciya ba ta sake gaishe shi, a dakile ya amsa ya bar gurin... murmushi kawai tayi ta juya suka cigaba da magana da Halisa...... *Littafin na kudi ne.....!* Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abun yake Vip gruop#600 normal group #300 account..... 0542382124...Binta umar gtbabk...Idan kati zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number. *07084653262* *BINTA UMAR ABBALE* 79******Halisa na murmushi tace" Ya kuma naganki a haka ina kika baro maigidan nawa."? Tace"Yana goye a bayan Yaya Ramlatu lokacin da zamu tawo yana bacci shine tace na kyaleshi kawai ta tawo dashi." Halisa tace" Ayya amma kin shiga gurin maijegon ko."? "Eh Hajia Rabi ma can na baro ta." Shuru falon yayi kowa yana tunani a cikin ransa......Kamshin turaransa ne ya sanya dukkaninsu suka dago kai suna kallonsa, Najaatu kallon sharia kawai tayi masa tayi kasa da kanta tana jin wani irin yanayi a jikinta, a duk lokacin da zata kalleshi sai sonsa da kaunarsa sun sake karuwa a cikin zuciyarta, Abbah Abbas kwata kwata baya tsufa kullum kara masa kuruciya ake babu wanda zai kalleshi yace yayi shekara hamsin a duniya saboda shi mutum ne dan gayu mai kula da kansa, Yanzu ma yayi ado cikin wani had'addan filtex irin na maza dark blue abinka da farin mutum sai yayi masa wani irin kyau, hula mai farin zanen zare yay amfani da ita, kafarsa sanye da takalmi sau ciki baki sai shaninig yake, farin gilashin da yake sakaye a idonsa yayi masa masifar kyau, Najaatu ta dinga jin wani irin sanyi na ziyartar jikinta sha'awarsa ce take taso mata a jikinta sai ta shiga tunawa da irin zazzafar soyayyar da ya dinga nuna mata a lokacin da suke tare.......Muryarsa taji yana magana..."Yau ma kin bar yaron nan a gida ko ashe ke ba'a isa a fad'a miki magana guda kiji ba? yanzu meye amfanin saka wannan mayafin na jikinki da kin sani kin yar dashi a hanya dan bashi da wani amfani tunda gashinan a zahiri komai na jikinki ana gani. Shuru tayi ta kasa magana ba wai dan bata da abinda cewa ba kawai tana ganin kamar shurun shi yafi amfani saboda gudun kada ta fada masa wata maganar yace tayi masa rashin kunya. Halisa tace" Ni sai nake ganin ai ba wani abu bane dan ta bar yaron a gurin Yaya Ramlatu tunda yanzu zasu zo maganar hijabi kuma ka ajiyeshi a gefe yau daya dan tasa mayafi ai ba laifi bane tunda bata da nauyin kowa a kanta kuma ni wallahi banga abunda mayafinta ya nuna ba. tana yar dariya ta karashe maganar. Yace." Ni na gani ai tunda ke baki gani ba, sannan ni nasan tana da wata munufa ta yafa mayafin tunda keda ita duk kun san bana son irin wannan mayafan marasa sirri saboda haka idan zaku tafi ki kar'bi hijabi gurin Halisa ki suturta jikinki baki burgeni ba idan dani kikayi.......Halisa tace"Ikon Allah shikkenan sai tayi kwalliya dan kai kad'ai bazawara ce fa kuma kowa yasan zawarawa da 'yan mata gurin ado da kwalliya me zai sanya ka damu kanka.....Yace."Ai shine abinda nake so ki fahinta ta bud'e tsaraicinta ne dan ni ko wani a waje ya gani yaji sha'awa to ni duk irin wannan basa burgeni." Jin abinda yake cewa ne yasa tace"Haba Abbah yanzu dan Allah ina tsaraici anan."? Tafada tana cire mayafin jikinta tare da gyara zamanta a kan kujerar. Saurin dauke kansa yay sakamakon ganin tudun nonowanta da suka fito ta saman riga.....Aunty Halisa tace"To nima dai haka na gani wallahi." Najaatu ta cigaba da cewa"Wallahi ni banyi kwalliyata dan kowa ba dan kaina nayi kuma Aunty Halisa ni bazan fitar da tsaraicina saboda na samu mijin aure ba saboda nasan ko yanzu na bukaci aure zanyi tunda ni nasan kaina ba k'aramar mace bace." Halisa ta dinga dariya tana kallonsa yana tsaye yana kallonsu, kowa dai yay zagi a kasuwa yasan da wanda yake, shuru kawai yay musu ya zauna kan kujera mai cin mutum daya, agogon hannunsa ya duba, ya kalli Mussadiq dake fama da game yace"Jeka gurun Zainab kace tazo amma tazo da baby Ummi." Yaron ya ajiye game din da sauri ya tafi aiken da akai masa. Abbah shuru yay yana jin Halisa na fad'in "Najaatu kin birgeni wallahi ai dama nace ke ba k'aramar mace bace koda baki sa mayafi ba ya kasance kullum a cikin hijabi kike na tabbata ba zaki rasa miji ba haba ai ido ba mudu ba yasan 'kima." Shiru yay bai tanka ba dan ya lura Halisa naso ta tona masa asiri a gurin yarinyar shiyasa yaja bakinsa yay shuru ya shiga girgiza kafafunsa....Halisa kallonsa take a fakaice tana 'boye dariyarta ita wallahi idan yana muzurai a kan rashin gaskiya dariya yake bata wai shi lallai ba zai fito fili ya nuna cewar ya damu da yarinyar ba alhalin duk gashinan ya nuna alama a zahiri kowa ya gani. Zainab ta shigo falon rugume da 'yarta ganin Halisa da Najaatu na hira cikin fahimtar juna yasa taji haushin hakan, dauke kanta tayi ta nufi gurun mijinta....Baby Ummi ya kar'ba daga hannuta ya rungumeta a gefan hannunsa na hagu sai ya janyo zainab din ya d'ora a cinyarsa, ya rike kungunta da hannunsa na dama wayarsa ya bata yace tayi musu hoto.......Wannan al'amari ya duguzunma zuciyar Najaatu da Halisa ba kamar najaatu da taji gurin na juyawa da ita, Ita kuwa Halisa d'aga murya tayi tace"Me yasa ba kaje can gurinta kunyi hoton ba ai ina ganin kamar hakan sai yafi armashi." Yace."Akwai jamaa a gurun ne ko banda ikon nayi abinda nake so a inda na gada dama." Ta'be bakinta tayi tace"Aa kayi komai babu damuwa ai." Ya kalli su Saddiqa da fad'in su taso suzo gurinsa, yaran suka kewaye shi Zainab na zaune daram! a cinyarsa tana ta daukarsu a hoto farin ciki kamar ya kasheta hakika tayi farin ciki da yanda ya nuna musu cewa ita mai muhimanci ce a rayuwarsa, in da shi kuma anasa bangaran da biyu yake haka duk dan ya cuzguna musu, aikuwa ya hango tsantsar kishi da tashin hankali a idanun Najaatu dan har ja idanunta sukayi saboda tsabar bacin rai da takaici......Sai da suka gama dauke dauke hotonsu sannan yazo inda suke zaune da yake duguwar kujera ce sai ya shiga tsakaninsu, Najaatu kamar ta miqe ta bar gurin haka taji sai dai ta daure ta matsa gefe saboda jin yanda ya takureta....Baby Ummi ya kar'ba ya riqe yasa su Saddiqa suka shigo kowa ya tsaya, sannan ya umarci Zainab din ta daukesu, hakan be mata ciwo ba saboda tasan ita ya fara nunawa muhimanci.....Zainab tayi musu kusan biyar ta miqa masa wayar, tare da fad'in "Zata koma gurin 'yan uwanta! Babyn ya miqa mata tare da fatan a tashi taro lafiya.....Ta 'karbi 'yarta ta tafi ba tare da ta kula kowa a gurin ba.....Shima tana fita ya miqe daga tsakiyarsu ya kama hanyar futa, babu wanda ya kulashi sai yaransa sune sukayi masa adawo lafiya. Ya amsa cike da walwala da farin ciki yasan yau da Halisa Da Najaatu dukkaninsu ba zasu yini cikin farin ciki ba, wato harshi zasu sa a gaba sunawa dariya sun mayar dashi sakarai shiyasa yay musu haka. bayan fitarsa Najaatu mamaki take sosai da yanda Halisa tayi sanyi yanzu gabadaya ta mayar da rayuwa ba wani abuba, idan da lokacin baya ne ai bai isa yayi mata irin wannan rashin kyautawa a falonta ba gaskiya kamar da akwai cin fuska a ciki sai taga kamar ma ita ta fita jin haushin al'amarin amma dai yanda ta dauke kanta daga kan abunda yayi yasa taji ta burgeta mutuka Taron sunan Zainab yayi kyau ya kuma k'ayatar anci ansha maijego ta fito sosai dan sai da tayi shigar kaya kala goma cikinsu duk babu na yarwa abunda yay musu cikas kawai rashin Dan Asharrale amma dai duk da haka ba suyi bikin Lami ba sai da suka saka (Mp) mai kid'an tsiya suka dinga jin wakokin *Gwanja* suna cashewa sai rawa suke suna murguda mazaunai maijego dadi ya isheta ta dinga yi musu liki.....Gabadaya d'abi'un 'yan uwan Zainab na banza ne 'ya'yan malam ne amma kuma sunqi halin malam rashin arziki kawai suke yanda ransu yake so. *BAYAN SATI BIYU* Al'amura suna ta gudanawa yanda ya kamata, ta bangaran Najaatu ta bude wuta sosai da ado da kwalliya da ta daidaici lokacin zuwansa gidan zata fito ta zauna kan kujera tana baza kamshi tururuka...Ita kanta hajia sai da taji dad'in salon da yarinyar ta tsiro dashi tasan tabbas yin hakan zai sake janyo hankalinsa kanta, aikuwa dai a tsakankanin kwanakin daurewa kawai yake yi amma yarinyar na mutukar galabaitar da zuciyarsa dan dai kawai mutum ne mai dauriya da dauke kansa a kan abu shiyasa baya bari kowa ya gane halin da yake ciki, duk sanda zai shiga gidan yakan sakaye idanunsa da gilashi gudun kada kwayoyin idonsa su nuna abinda yake zuciyarsa.....Najaatu halin ko'in kulan da yake nuna mata bai dameta ba kwalliya da sauran abubuwa ba zata daina ba tunda ta fahimci suna tasiri a tare dashi..... Da yake tana da yawan gashi mai kitso har gida take zuwa ta 'bata lokaci gurin tsantsara mata kunshi kuwa da ya goge zatayi wani........Al'amarin daya sanya shi tunanin sanja shawara akan wacce sukayi da hajia yana ganin kamar d'aura auran a kurkusa shine kwanciyar hankalinsa idan yace zai cigaba da zama tsayin watanni yana ganin yarinyar hankalinsa na tashi to babu shakka zai iya shiga halin ni 'yasu dalilin daya sa ya yanke shawarar tunkarar abokinsa da maganar.....Abbah Magaji yace"To tunda kana ganin hakan yayi maka shikkenan sai kawai ka sanya a ranar da kakeso a daura auran." Yace."Yau insha Allah idan na shiga unguwar zan zauna da Malam da Alhaji a kan maganar." Abbah Magaji yace."To shikkenan Allah ya sanya alkairi yasa anyi kenan." Ya amsa da ameen ameen. Najaatu duk wani abu da ake bata da labarinsa dan tunda aka tsayar da maganar daurin aure shi bai kirata ya fada mata ba kuma har yanzu babu wata kyakkyawar alaka a tsakaninsu, tana dai jin maganar sama sama a gurun hajia da Yaya Ramlatu suma kuma babu wacce tace mata komai a kan al'amarin.......Ranar Lahadi da safe yazo gidan, Hajia na sama tana sallar walha Yaya Ramlatu da Hajia Rabi sun tafi asibiti duba Salim ashe tun ranar da Naburago ya watsa masa kudin auransa ya kwanta ciwo kamar ba zaiyi rai ba, sai da aka kwantar dashi a asibiti sannan Sakina ta aiko aka sanar da mahaifiyarsa shine fa Alhaji yace maza maza suje su duba jikin nasa ai hannunka baya ru'bewa ka yanke ka yar........Tana daki tana gyara jakar kayanta yay sallama a dakin, gabanta ya fadi dajin miryarsa, daidaita nutsuwarta tayi ta dan juya tana amsawa .....Idonsa kuri kan gashinta wanda akayi mata wani irin kitso mai kyau jelolin gashin sun dan sauka bayanta, Najaatu nada gashi daidai gwargwado gashi baki mai daukar ido......Ganin yana mata wani irin kallo ne yasa ta lalubi dankwalinta ta daura, a sanyaye tace"Abbah sannu da zuwa." Da sassauci a tare dashi ya amsa tare da neman guri ya zauna yana kallonta, gaishe tayi ta dan gyara zamanta tana jira taji da abinda yazo dashi. Gyaran mirya yay as'usul yace."Naji gidan shuru tunda na shigo banji motsin mutum ba ina fata dai lafiya."? Tace"Wallahi tun safe Alhaji da Hajia Rabi yaya Ramlatu suka tafi asibitin gadon kaya wai ashe Salim ne bai da lafiya yana can a kwance, ita kuma hajia na sama tana sallar walha." shuru yay na minti biyu kafin yace."Tun yaushe ne baida lafiyar.''? Tace"Wallahi ban sani ba jiya Matar babansa ta aiko aka fad'a." Allah ya sawwake." yafada yana me tsurawa yatsun hannunta ido....Dakin yay shuru kowa na tunani, Abbah tunanin ta inda zai fara yake, da kyar ya iya kiran sunanta. Ta daga kanta ta kalleshi kafin ta mayar dashi kasa "Kina da labarin maganar daurin auramu ranar jumaa mai zuwa kuwa."? Gabanta ya fadi tayi saurin kallonsa, girarsa ya daga mata ya lumshe idonsa, a hankali yace." Naso na bari yaronki ya kara kwari amma na kasa saboda ni kadai nasan yanda nake jinki a cikin zuciyata, Halisa tace ba zan ta'ba samun nutsuwa ba sai dake sai nake kokarin k'aryata maganarta saboda ina ganin ke baki isa ki tauyemin rayuwata ta kowane fanni ba, ashe so ba haka yake ba, dalilin yin hakan da nayi yasa ya mayar dani sakarai mara nutsuwa gami da saninan muhumacinsa, hakika a cikin 'yan kwanakin nan ni kadai nasan irin azabtuwar da nake a kanki Najaatu zan sake auranki a karo na biyu inaso ki bani hankalinki da nutsuwarki da dukkanin kulawarki bana so a yanzu dani dake muyi auran Madadi inaso muyi aure naso da kauna wanda zamu rayu a cikinsa cikin farin ciki da walwala har karshen rayuwarmu." Wani irin farin ciki ya ciki mata zuciyarta hawayen farin ciki ya shiga sauka akan kumatunta, mirya na rawa tace"Abbah ka daina kokwanto akaina a yanzu zan aureka na zauna da kai tsakani na da Allah, Wallahi ban ta'ba kaunar wani namiji ba kamar ka, Abbah bani da za'bi sai naka bani da bakin godiya a gareka kayi min dukkanin sadaukarwa a rayuwata inaso yau na fad'a maka da bakina cewar ina sonka wanda ban san iya adadinsa ba, ina rokonka daka yafe min abubuwan da suka faru a baya kuruciya ce da kuma qaddara yanzu zan zauna zaman aure da kai tsakani da Allah da kuma so da kauna insha Allah." Ya dinga wani murmushin farin ciki da jin dadi yana wani lumshe idanunsa a kanta, mirmushi tayi ta sunkuyar da kanta k'asa tana wasa da hannayenta yace."Nayi farin cikin jin wannan magana taki Najaatu ashe yanzu ina da babban matsayi a cikin zuciyarki ban sani ba, a gaskiya dole wannan karon nayi shiri mai kyau inaso na nuna miki ni daban nake da sauran maza sai kin kasance a matsayin matata zaki gazgata hakan." Yakare maganar yana jifanta da wani shu'umin kallo...Kunya ce ta rufe ta da sauri ta rufe fuskarta tana dariya. *ALHAMDULLILAHI FAD'AN MASOYA HUTU NE INJI BAHAUSHE* Salim zazza'bi typoid ne yaci karfinsa inda har ya ta'ba masa hanjin jikinsa,wannan bayanin likitan dake kula dashi yayiwa Alhaji hankalinsa ya tashi Yaya Ramlatu kuwa kuka kawai take tana fad'in ''Yanzu wata da wattani d'anta yana kwance yana ciwo a kasa fada mata wato da sai dai taji labarin mutuwarsa kenan, babu shakka abunda Sakina tayi mata bata kyauta ba Ita dai Sakina hakuri kawai take bata dan gabadayan su Hankalinsu ya tashi jin cewar hanjin cikinsa ya 'bule dole sai anyi masa aiki. Abbah Abbas ma da yazo dubashi sai da hankalinsa ya tashi, a take yasa hannu ya kuma biya zunzurutun kud'aden da asibitin ke bukata yace maza a shiga dashi teater , Allah sarki Yaya Ramlatu kuka kawai take dan gani take tamkar gawarsa za'a fito mata da ita, sai dai kuma ba a nan take ita cuta ba mutuwa bace mai lafiya ma yana iya mutuwa ya bar wanda yake da shekara goma yana jinya.......Lafiya lau aka fito da Salim anyi aiki cikin nasara yanzu abinda yay saura kula da shan magani akan 'ka'ida. ***** Alhaji Aminu Dan jarida da kyar ya samu gurin zama bayan fitowarsu daga prison sai kowa ya gudunsu dalilin daya sa kenan ya harhada 'yan kudaden da suka rage masa ya gudu k'yauyen zaria shida iyalinsa ya samu ya siyi wani lalataccen gida, sauran kudin suka siyi kayan abinci....Mommy ta fara sanar sai da gwanjo a cikin kyauyen sai ta shiga cikin gari ta siyo tazo ta baza a kofar gidan jama'ar garin na siya da wannan sanaa suke rufawa kansu asiri. A lokacin Munira ta dade da haihuwa inda ta haifi Da namiji a hannun kanwar Momynta Laila.......'Kaskanci da wulakanci babu irin wanda Munira bata gani ba, taci wuya sosai wanda sai da ta kai ta kawo ta daina fitowa waje dan da ta fito za'a soma yi mata waka mai cikin shega babanta karto d'an uwanta 'barawo wasu yaran ma har jifanta suke wannan dalilin yasa take zama a gida taci kukanta ta koshi Lailah ta ta cigaba da azabtar da ita....Tunda ta samu labarin dawowar iyayenta ta gudu ta koma gurinsu, dan gwara tayi rayuwa a cikin kyauyen da suke a kan azabar da Laila take gana mata. *RANAR JUMA'A* Ranar aka daura auran Abbah Abbas da Najaatu a karo na biyu daurin auran yayi albarka sosai dan ya samu halartar manya manyan mutane daga bangaran Alhaji Abbas mai girma governor dashi da mukarrabansa ma sun samu hallatar daurin auran Abbah Abbas ranar kasa rufe bakinsa yay sai murmushi yake yana gaisawa da jamaa cikin walwala da farin ciki.........Najaatu ta sake zama matarsa a karo na biyu ai dole ya nunawa Ubangiji farin cikinsa.. *'Kawata kada kiyi wasa da wanke bakin ki domun ana saurin gane tsabtar mutum ta ha'koransa.....Akwai damuwa ace wai idan kikayi brush da safe ba zaki sakeyin wani ba sai wata safiyar???? to idan kuna marking lov da oga yana muradin ya sha bakinki yaji wari ko datti abinci kina tunanin zai sake marmarin kusantar bakin ki????????♀️ tsotsar bakin juna gurin mu'amula ta aure na qarawa ma'aurata amarshi da son kasantuwa da junansu, duk wata macen da mijinta baya had'a baki da ita ta bunkici kanta,????rashin gyara da kula da kanki zai janyo miki babbar matsala k'awata.......Idan kinyi bursh da asubah da safe kafin ki karya ki sake yin wani, da daddare kafin ki kwanta kiyi wani ki dauki kaninfari guda biyu kisa a bakinki kina tsotsa, kaninfari yana da mutukar sirri a tare dake kada kiyi wasa dayin amfanin dashi, dan Allah kada kiyi saken da zai sanya mijinki ya dinga gudun had'a baki dake????* Share this [ad_2]