MADADI Page 91 to 100

Abbah da kyar ya sata tayi shuru a maimakon ta tsaya ta cigaba da sauraran nasihar da yake mata kawai sai ta kwanta ta juya masa baya zafafan hawaye na zubo mata
Yaron ya ajiye mata a kusa da ita ya fita daga dakin yana mamakin al’amarin…..Kafin ya tafi harkokinsa sai ya tsaya ta tambayi hajia ko da akwai abinda ake bukata, hajia ta fad’a masa duk abinda ake bukata yace insha Allahu zai turo yaronsa
Aikuwa wajejan sha biyu na rana Abdulhamid ya kawo uban naman rago gami da kaji gyararru da kayan tea da uban cefane mai yawa………..A take Hajia ta umarci Yaya Ramlatu data taimakwa Jummai mai aiki da suyi wa Naja’atu miya irin ta masu jego.
Sai bayan la’asar iyalin Abbah Abbas suka sauka a gidan dukkaninsu har da yaran tinda washe garin ranar haihuwar jumaa ce sun taso daga makaranta da wuri yaran sai murna sukeyi zasuje suga d’an jinjiri……To bayan sun gaisa da hajia kai tsaye dakin da maijego take suka nufa…Naja’atu da aunty Maryam suna hira sukaji sallamarsu, halisa kamar ba itaba ta karasa cikin dakin da faraa a tare da ita take fadin”Lallai haihuwa da lafiya abar alfahari ce gaskiya na taya ki murna naja’atu Allah ya raya ya baki lafiya.”
Aunty maryam ta amsa da ameen tana miqa mata yaron, Halisa ta karba tana dariya kamar ba itaba suka gaisa da Aunty maryam din cikin sakin fuska, aunty maryam ta dinga mamakin al’amarin, Zainab kuwa sai dauke kai take tana ya mutsa fuska, aunty maryam tace “Sannu uwar biyu kema ai kin kusa Allah dai ya raba lafiya.”
A hankali ta amsa da “Ameen.” Najaatu ta dan kalleta na minti biyu ta kau da kanta ta rasa me yasa gabad’aya Zainab din ke bata haushi iyayinta shine abinda tafi tsana a tare da ita
Halisa ta gama duba yaron ta miqawa Zainab da fad’in ”Gashi ki daukeshi kema kisa albarka.” Zainab ta ya mutsa fuska da fad’in aunt Halisa bana iya daukarsa ni kai dai nasan abunda ke damuna Allah yasa masa albarka.”
Babu wanda yaji dadin abinda tayi ai ko yaya ne ta daukeshi koda kuwa bata jin dadin jikinta…Naja’atu taji haushi sosai sai dai ta bawa zuciyarta hakuri ta cigaba da amsawa Halisa maganar da suke……Su Saddiqa ne suka shigo dakin suna murmushi.
Aunty Maryam tace”Yawwa dama tun dazu ‘kaninku yake neman ku da har yayi fushi na bashi hakuri.” Da sauri mussadiq ya karasa kusa da Halisa yana dariya yana leqa fuskar yaron, Halisa tace zauna nasa maka shi a jikinka.
Ya zauna da sauri tasa masa yaron ya rungumeshi su Saddiqa na leqen fuskarsa! Aunty Maryam ta kalli Mufida da fad’in “Albishirin ku.” Mufida tace”Goro.” Aunty maryam na dariya tace”To dai yaro yaci sunan Abbanku dan sunan da mamansa ta za’ba masa kenan.” Ai gabad’aya sai yaran suka shiga murna da farin ciki Halisa na ‘yar dariya tace”To ikon Allah ashe sunan maigida aka saka masa gaskiya dole na fito da kyau ranar suna.” Aunty Maryam ta dinga dariya tana fad’in “Aikuwa hakan nada kyau.
Zainab kamar ruwa ya cinyeta a dakin tayi d’if bakin ciki kamar ya kasheta jin wai sunan mjinta ta sakawa yaronta yasa ta sake jin wani sabon kishi na taso mata….Gabadaya zaman dakin ne ya gundureta mutukar zata waiwaya ta kalli Naja’atu shar da ita tana dariya da farin ciki to ji take kamar zata mutu saboda bakin ciki….Miqewa kawai tayi ta kama hanya fita, dukkaninsu suka bita da kallo har ta futa babu wanda yayi mata magana a cikinsu…..To aunty maryam dai da Halisa ba yara bane dukkaninsu sun gane abinda ke damun yarinyar itama Naja’atun taso ta fahimci wani abu kawai ta share abun ne dan a zauna lafiya amma zahirin gaskiya irin halin ko in kulan da Zainab ke nuna mata yana yi mata ciwo.
Zainab falo ta fito ta zauna ita kadai abun duniya ya isheta, ita kuwa Yaya Ramlatu sai shige da fuce takeyi a tsakanin Dakin maijego da kicin tana sakin habaici ga Zainab din(???? mai hali baya fasa halinsa hausawa suka ce idan ka kwana biyu ba kaga mutum ba to kana ganinsa ka fara tambayarsa halinsa) Zainab muzanta tayi kwarai da gaske sai ta shiga data sanin fitowa falon , sunkuyar da kanta tayi kuka na kokarin kufce mata….Yaya Ramlatu bata qyale Zainab ta sarara ba sai da taga hajia ta sakko tukkuna ta rabu da ita.
Har yamma suna gidan aunty maryam kuwa ganin yamma tayi yasa tayi musu sallama ta tafi gidanta……Halisa da Zainab suka zauna jiran zuwan mijinsu domin haka yace su zauna su jirashi idan yazo sai su tafi tare…..Daf da magariba Abbah da Abbah magaji suka shiga gidan Alhajin Abbah Abbas da kansa ya jagoranci Abokin nasa har dakin da maijegon take ya shiga ya duba yaro da mamansa, Naja’atu kasa hada ido tayi dashi sabida kunya kuma tayi mamakin yanda ya dauki yaron nata yayi masa addua sosai, ta dinga jin wani iri a jikinta tana tuno irin rashin arzikin da dinga yi musu a lokacin auranta da Bash! tana can tunanin abinda ya shud’e suka fita daga dakin ba tare da ta sani ba.
*Littafin na kudi ne…..!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar karantawa ga yanda abin yake….Vip gruop#600 normal group #300 account… 0542382124….Binta umar gtbank… Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
Takwara nima ina bayanki gaskiya abun na Abbah Abbas yayi yawa, haba yace shi ba mayar da ita zaiyi ba to me yasa yake damun kansa a kan al’amuranta hidimar tayi yawa???? kuma Zainab macace dole tayi kishi tunda halak ne! itama Halisa ruwa ne ya daki babban zakara shiyasa tayi sanyi……gaskiya Zainab da Halisa suna da hakuri☺️………..Nafisat maganarki haka take Najaatu dawa ta dogara da har takewa wata al’kawarin zata bata jari???? Kawai ta samu mutum sai tatikeshi take koda yake ai yace saboda Allah da Annabi yake mata hidima! hummm! to maji ma gani dai wai an bunne tsuhowa da ranta????
*MADADI*
72*****Naja’atu sai wajajen tara na dare da samu sukunin kiran wayar su Mmn Sajida ta fad’a musu ta haihu! Mmn Sajida kamar ta fasa wayar dan murna a gurguje ta shiga gidan Mmn Ladi ta sheda mata, Mmn Ladi na murna da farin ciki ta kar’bi wayar tana mata barka tare da fatan Allah ya raya abunda aka samu…..Sun juma suna hira da juna kafin tayi musu sallama cike da jin kaunarsu a cikin ranta. To a takaice dai
Sai da Naja’atu ta kwana uku da haihuwa tukkuna Baba Talatu tazo ta duba taga abinda ta haifa daukar yaron tayi tai masa addua daidai gwargwado tabbas komai qinka da abu idan Allah ya qaddara faruwarsa babu yanda za’akayi, babu shakka rabon wannan yaro ne ya raba auran *MADADIN* da suka daura amma suna fatan Allah ya mayar dashi da alkairi……………Bayan ta gama zancan zucci da take sai ta kalli Naja’atun a nutse tace” ‘Dazu Magaji yake fad’a min cewar wai kin za’bawa yaro suna hakane ko.”? A sanyaye tace”Eh Baba nace ayi masa hud’uba da sunan Abbah Abbas dan ganin yanda yake hidima nasan babu abinda zanyi na biya shi dawainiyar da yake dani amma hausawa na cewa yaba kyauta tukwici a ganina sunansa yafi cancanta a sakawa yaron.”
Baba Talatu tace”Lallai kinyi tunani mai kyau Naja’atu kuma nayi farin ciki sosai da wannan yaro yaci sunan Alhaji Abbas ina rokon Allah yasa ya gaji irin halinsa.” Kanta a ‘kasa ta amsa da ameen ya Allah.” Baba malam ma da yaji sunan da Naja’atu ta za’bawa yaron yaji dadi sosai saboda haka