MADADI 1-END

MADADI Page 91 to 100

A daran ranar da Baba Talatu ta fad’a masa maganar ya aika aka dauko masa yaron yayi masa hud’uba da sunan Abbas kamar yanda Naja’atun ta buqata..

‘Bangaran Abbah Abbas kuwa koda ya samu labarin anyiwa yaro huduba da sunansa beyi mamaki ba saboda dama kafin hakan ta kasance sunyi maganar da ita kawai sai yayi fatan alkairi tare da yiwa yaron adduar shiriya maidaiciya……..Washe garin ranar yana zuwa Kasuwa ya kira Abdulhamid ya umarce shi daya shiga kasuwa ya had’o kayan baby duk wani abu da yasan masu haihuwa na bukata ya siyo idan ma bai gane ba yayi tambaya a gurin yace a hada masa set biyu, yana nufin dana Naja’atu dana Zainab duk da ita bata haihu ba yana ganin idan ya siya ya huta tunda itama a kan hanya take cikinta yanzu yana wata bakwai.

Abudulhamid ya nufi kasuwar wambai dama dan wajejen ne, kai tsaye gurin masu siyar da kayan bebis ya nufa, yace a had’a masa kayan jarirai. Mutumin ya tambayashi namiji ko mace.” 

Da sauri ya dauko wayarsa ya kira Abbah Abbas din ya tambayeshi, yace A had’a na maza duka duk da bawai amincewa yayi da scanning din Zainab ba yasan hasashe ne abun bai zama lallai ta haifi Namiji ba kamar yanda suka fad’a! ya dai siya kawai idan mace ta haifa ya sake siyan wasu.

Sannan yace masa ya wuce da kayan gida ya kai b’angaran Zainab zai kirata a waya ya fad’a mata.

Tsaf aka had’a kaya saiti biyu iri daya Abdulhamid ya shiryasu a mota ya nufi gidan Ubangidan nasa 

Abbah na gama waya da Abdulhamid ya kira Zainab ya fada mata cewar Abdulhamid zai zo da kayan jarirai sai ta za’bi wanda take so ta barwa Naja’atu nata….Zainab ta rasa inda maganarsa ta dosa sai kawai ta amsa da to sukayi sallama.

Abdulhamid yazo ya jibge mata kaya a bakin gate din gurinta bayan fitarsa ta tsirawa kayan ido ikon Allah komai iri d’aya komai biyu sai kace kayan tagwaye sai ta shiga zargin anya kuwa ba shine uban yaron ba, to idan ba hakaba ya za’ayi ya dinga daidaitashi da d’ansa.

Kamar za tayi kuka ta nufi gurin Halisa, taje ta tattagota suka zo suka tsaya a gaban kayan suna kallo….Halisa ta sauke ajiyar zuciya tana dudduba kayan tace” Saura ragon suna shine kawai abunda ya rage amma wannan hidima tayi yawa, ni kam banta’ba ganin mutum mara zuciya irin Abban Mufida ba wallahi.” Yanda ta fadi maganar zaka fahimci a fusace take, dan duk abinda yake akan Naja’atun bai ta’ba qular da ita irin yau ba, haka kawai saboda rashin zuciya ya dinga daukar yaro yana daidaitashi da nasa gaskiya abunda yake yayi yawa wallahi

 Zainab kuwa fashewa tayi da kuka da fad’in “Kin san Allah aunty Halisa hakuri na ya kusa ‘karewa nifa ba zan iya jurar wannan wulakancin ba wallahi!…Yama za’ayi ya dinga daidaita ta damu muna a matsayin matayensa komai zaiyi mana sai yayi mata ke wata hidimar ma da yake mata bayayi mana, ba dole muyi zargin akwai wani abu qasa ba ni wallahi bana son namiji munafiki ki duba kiga kwanaki yanda ya fitittuke yana kokarin ci mana mutunci a kanta ina dalili wallahi bazan zauna hawan jini ya kama ni ba.” Zainab na kuka ta qarashe maganarta.

Halisa tace”A’a Zainab kibi hankali kusan wata takwas kina zaune da mutumin nan amma har yanzu kin kasa gane halinsa Abbahn Mufida idan yasa kansa abu babu wanda ya isa ya hanashi, kuma wallahi ki iya bakinki rashin kunya babu inda zata kai ki ki kyaleshi kawai muga iya gudun ruwansa ai shi dai da bakinsa yace ba dawo da ita zaiyi ba to duk ranar da yazo mana da maganar zai dawo da ita mu kuma a ranar zamu mayar masa da martani…..Sannan ki daina sakar masa fuska nima zai daina ganin walwalata kwana biyu haba abun ya wuce gona da iri kawai saboda yaga munyi masa shuru sai ya dinga yi mana abunda yaga dama.”

Zainab tace”Nifa aunty Halisa ban iya ‘boye abu a raina ba shiyasa ko gidanmu sukeyi min kallon mara kunya a gaskiya idan ba’a nan din ba to babu a inda za’a dinga cimin fuska na haqura ki duba kiga wannan aikin dan Allah kawai an kama an siyo min kayan haihuwa da wata mtssw!.” takarashe maganar tare da jan tsaki.

Halisa ta’be bakinta tayi tace”Allah y kyauta na fad’a miki ba tsayayya zakiyi masa ba ki ‘bullo masa ta bayan gida idan kika ce zakiyi masa rashin kunya duk abin arzikin da yake da mahaifinki bai hanashi ya kora ki gida ba.”

Zainab jikinta yayi sanyi jin maganar da Halisa tayi, gaskiya tana jin tsoron faruwar hakan saboda tasan halin mahaifinta bashi da wasa idan ma yaji kan abinda take rigima a kai zai iya hukuntata, tana ganin zata ‘bullo masa ta bayan gida kamar yanda Halisa ta bata shawara. Wuce wa tayi ta bar gurin ba tare data ta’ba komai a cikin kayan ba…………Hasken solar daya haske harabar gidan nasa baisa ya lura da kayan dake gibge a guri guda ba, kasancewar girkin Halisa ne sai ya nufi gurin zainab din ya gurguje domin ya dubata.

.A kwance ya sameta a dakinta yara suna falo su kadai….Yayi mamakin hakan kasance duk dare tana zama tare da yaran a falo har sai ya shigo gidan

ita kuwa Zainab tana jin shigowarsa dakin sai ta shiga baccin karya yayi ta kiran sunanta tana ji taqi magana, kawai sai ya qyaleta da tunanin anjima kafin ya kwanta ya sake shigowa ya dubata watakila lokacin ta tashi.

To koda ya shiga gurin Halisan ma bai samu tar’ba mai kyau ba, ta bashi abinci amma bata zauna ta bari ya gama ci ba ta bar gurin…Zuwa tayi ta kwanta ta bacci ya dauketa….Abbah bai kawo komai a ranshi ba, daya gama dube dubensa a loptop kamar yanda ya saba sai ya sake komawa gurin Zainab din nan ya tarar har ta kulle kofar falon daga ciki kamar tasan zai dawo, kasa hakuri yayi yana tsaye a gurun ya kira wayarta lokacin bata kwanta ba kuma bata kashe wayar ba amma tana kallo yana kira bata daga ba.” Girgiza kansa yay ya kama hanya da niyyar barin gurin yana nazarin wani abu a cikin zuciyarsa…….Cin karo yayi da abu yayi saurin kuna hasken wayarsa yana dubawa……Ya kai minti biyar yana nazarin kayan kafin ya gane kayan daya sa Abdulhamid ya kawo ne! to meye amfanin barinsu a waje? tambayar kansa yake! wannan ya nuna masa cewar Zainab duk abinda tayi masa a yanzu tana da manufa! takaici al’amarin yasa shi jan karamin tsaki ya bar gurin tare da tunanin halin quruciyar yarinyar yasan dai duk abunda takeyi akan Naja’atu take yinsa.

To al’amarin su Halisa fa ya tsananta kwana biyu sun had’e masa kai babu wacce ke sakar masa fuska, tun abun na bashi dariya da mamaki har ya dawo bashi haushi! daya gaji da bibiyarsu sai shima ya dauke musu wuta ya shiga sabgarsa da yaran sa idan ya dawo gida yayi abinda zaiyi ya shige dakinsa ya kwanta ba wacce yake cin abincinta, kayan jirajirai kuwa daya fahimci akansu suke jin haushi, sai ya sake qudurtar kuntata musu bai dauki kayan ya kai gidan Alhajin ba sai da yasa aka kawo masa manya manya atampopi guda uku da legos less masu tsada biyu sai wani boyel mai uban kyau da tsada da saitin takalmi da jakarsa, a falon Zainab ya ajiye kayan sabida yasan dole zata kira Halisa ta gani, aikuwa a ranar kasa komai sukayi a gidan kowacce al’amarin yafi karfinta! wato fushin da suke yi ma kamar tunzurashi suke……Zainab cutar karya ta kirkira ta dinga kuka tana lanjarewa darajar abinda yake cikinta ya kulata..Ita kuwa Halisa shareta yayi ya daina shiga sabgarta……Ranar suna da sassafe ya dauki yaransa ya kaisu gidan yayi tafiyarsa sabgarsa, Halisa taga al’amarin na nema ya zama babba sai ta shirya tsaf da turaman atamfofinta guda biyu ta nufi gidan Alhajin…Ita kuwa Zainab cewa tayi babu inda za taje bata da lafiya.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button