MADADI 1-END

MADADI Page 91 to 100

Halisa bata saurareta ba ta tafi tare da daukar alkawarin bashi hakuri dangane da abunda sukayi masa………..

*Littafin na kudi ne….!*

Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya ga yanda abin yake Vip group #600 normal group #300 account… 0542382124…Binta umar gtbank….Idan katin waya zaki tura kiyi min mgn ta whasap da wannan number

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

*BA HARAM BANE!*

73****To alhamdullilahi duk wani abunda ake bukatar ayiwa mai haihuwa Abbah Abbas da iyayensa sunyiwa Naja’atu sun tsaya a kanta sun mata gata fiye da wacce take da miji anyi suna cikin walwala da farin ciki Naja’atu har kuka tayi a ranar sunan ganin yanda kowa yake nuna mata kauna ita da d’anta, a gaskiya kafin samun mutane masu karamci irinsu Alhaji da Hajia sai an bincika, dama kuma barewa ba za tayi gudu danta yayi rarrafe ba, babu shakka Abbah Abbas shine zai zama magajinsu dan gabad’aya shine yake kwatanta hallayar iyayen nasa Abbah Abbas kwata kwata abin duniya bai rufe masa ido ba shi har so yake ma mutum yazo neman abu a gurinsa ya dauka ya bashi, a kasuwa kuwa bai san iya adadin mutanan daya yafewa bashika ba, shiyasa gashinan kullum Allah qara daukaka darajarsa yake yana samun addua ta kowane bangare.

Halisa jiki a sanyaye ta dawo gida tana ta mamakin yanda al’amura suke kasancewa, mijinta ya siyawa mejego raguna biyu manya manya sannan ya siyi wanda akayi miyar suna duk a bakin Ramlatu take jin maganar, hakikanin gaskiya jikinta yayi sanyi da irin qaunar da yakewa yarinyar tana ganin dawo da ita gidansa shine yafi masa alkairi sai kawai ta yanke shawarar watsar da makamanta za ta kuma tunkareshi da maganar Naja’atun taji mai zai sake cewa.

Ranar dama itace take da girki ta fito falo ta sameshi yana abunda ya saba, da kyar ya saurareta dan har yanzu haushin abinda sukai masa yake ji……Yace.”Ai kin bani mamaki Halisa ina tunanin kece ta farkon wacce zata fadawa wani halina, meye a cikin abubuwan da nakewa Najaatu da duk zaku tayar da hankalin ku akai har kuna had’e min kai saboda baku da hankali! to inaso na tuna miki abunda kika manta, Naja’atu bata da wanda ya fini tunda tun tana shekara hudu take a hannuna nine na rainata tana riqe ta tamkar ‘yar dana haifa a cikina ni ta sani duk wani nauyi nata yana kaina, koda iyayenta nada halin daukar d:awainiyarta to bazan bari ba saboda tun farko sun dauke ta sun bani ita, wannan dalilin ya sanya nake kokarin ganin na sauke nauyin amanarta dake kaina, duk ki ture ta wasu abubuwan da suka faru a tsakanina da ita, ni ba mutum ne me riqe abu a cikin ransa ba, da ina da wannan d’abiar to na tabbata ba zan kalli inda take ba, ballantana na ‘batar da kwabona a kanta, sannan idan banda abunku ai Najaatu abar ku tausaya mata ne duba da halin da take ciki menene abin ganin k’yashi da kishi dan na taimaka mata.”?

Halisa tace”Duk naji bayanan ka amma dai kasan kishi halak ne ko.? Shuru yay yana kallonta ta cigaba da cewa”Nifa wallahi idan zaka dafa al’kur’ani ba zan yarda cewar baka son yarinyar nan ba.” ‘Bata fuska yay yana dan harararta Tace”Ai gaskiya ce abunda kakeyi yay yawa haba kowa ya d’ora zarginsa akanka nasan ita kanta yarinyar tana ji a jikinta ko zaka mayar da ita gidanka ne, dan haka nima wallahi nafi sha’awar ka dawo da ita dani da kai da ita Zainab din dukkaninmu sai hankalinmu yafi kwanciya

Ya jima kafin yay magana yace”Na fad’a muku ni ba zan dawo da Najaatu gidana ba amma kun’ki yarda da maganata, magana ce mukeyi a kan cikinta da haihuwarta to tinda Allah yasa ta haihu lafiya ai abunda ake bukata kenan daga haka kuma me zai sake shiga tsakanina da ita idan ba gaisuwa ba, amma tunda na lura zama ku biyu ne bakwaso zan fara neman aure shikkenan sai hankalinku ya kwanta.

Murmushin takaici tayi tace”Ba sabon aure ya kamata kayi ba Najaatu ya kamata ka dawo da ita dan wallahi ko sabon auran kayi ba zaka samun nutsuwar da kake bukata.”

Yace.”Haka dai kike gani ni Najaatu bata gabana wallahi kune dai kawai kuke zargina akanta zaku wahalar da kanku ne a banza.” Yana gama maganarsa ya cigaba da duba laptop din gabansa…..Halisa takaici yasa ta bar gurin, kwanciya taje tayi tana tunanin maganganunsa itafa ba yarinya bace ballantana ya raina mata hankali.

Tunda akayi suna ya daina zuwa gidan da safe, ya dawo zuwa da yamma kamar yanda ya saba kuma babu ruwansa da shiga sabgar Najaatu gaisuwa ce kawai take had’ashi da ita yay abunda ya kawoshi ya tafi, ba Najaatun ba su kansu su hajia sai da suka fuskanci sauyawarsa sai duk jikinsu yayi sanyi kada fa yay musu bazata ya nuna musu abunda suke zargi ba haka bane a gurinsa.

*BASH!*

Abunda sukeyi dashi da abokansa ya wuce tunanin masu tunani, yanzu harkar siyar da hodar ibilis suke da turawan america, Bash ya had’a kansa da manya manya yahudawa suna ta aikin sa’bo! Yayi masifar kudi irin wanda yake b’ukata gabad’aya idan kun ka ganshi ba zaku ganeshi ba saboda dukkanin kammaninsa sun sanja ya samu duniya sosai duniya tasan da zamansa kuma abokanansa sunaji dashi saboda yana brain sosai yana kawo musu cigaba a cikin harkokin da sukeyi a ‘boye…………… to hausawa sukace rana dubu ta barawo rana guda ta me kaya Ranar Asabar Allah yay nufi tona musu asiri sun shirya shida abokanasa suka nufi Cameroon domin shigar da musu da kayan sana’ar tasu, lafiya lau suka sauka a filin jirgin garin suka soma saukowa kowa na goye da wata katuwar jaka a bayansa, wani ma’aikaci ya dakatar dasu, yace su ajiye jakkunan dake bayansu, cikin turanci Bash yace idan zaiyi bunkice a kansu yayi su ba zasu ajiye jakarsu ba, mutumin sabon ma’aikaci ne mai aiki domin kishin qasarsa, kawai yace azo a tafi dasu tunda sun sa gaddama sunqi suyi abunda ake bukata suyi……Jin haka da sukayi kawai sai Bash yayi dubarar dauko k’aramar bundiga dake cikin jakar bayansa ya harbi ma’aikacin nan a gwiwa kafin kice kwabo guri ya hautsine! ganin haka yasa da saurin gaske shima ya saita kafafun Bash din ya harbi daya Bash ya zube a gurin yana ihu hade da riqe kafarsa data jiqe da jini,

abokansa suka nemi hanyar tserewa Jami’an tsaron da suka iso gurin suka damqe su………sai da sojoji sukayi bunkice sosai a gurin kafin su bari kowa ya fita daga airport din, tashin hankali su Bash suka raina kansu lokacin da jamian tsaro suka ga abubuwan dake cikin jakkunansu, tun a airport din suka fara jibgarsu kafin su sasu a mota su tafi dasu…….tsayin sati guda suna binkice a kansu kafin su san kasar da kowanne daga cikin su ya fito, jamian tsaro na kasar Cameroon sun samu cikakken bayani akansu Bash cewar mugwayen ‘Yan taaddah! ne wanda suka addabi mutane da gomnati dama kullum cikin bukince ake a kansu da abubuwan da suke aikatawa tunda Allah yasa yanzu suna hannu sai a yanke musu hukuncin daya dace………Koto aka shiga dasu, alqali yaji ya kuma tabbatar da dukkanin abunda ake zarginsu dashi tsabar wahala yasa dukkaninsu basu karyata ba sabida sun riga sun saddaqar da cewa karshensu ne yazo…..A take mai girma mai sharia ya yanke musu hukuncin kisa domin barinsu a doron duniya had’ari ne hukuncin da aka yankewa su Bash babu wanda bai sa farin ciki ba lokacin ne ‘yan jarida suka samu aikin yi……suka dinga daukar hotonan su da muryoyinsu Allah Sarki Bash sunkuyar da kansa kawai yake yana hawayen nadama, dan da wani dan Jarida yazo yana masa tambayoyi kasa magana yay ya dago kansa kawai hawaye na zuba a kumatunsa magana biyu kacal ya iya fad’a….”Iyayane sune silar lalacewata babu abunda zance musu sai dai nace zamu hadu a gaban Allah. Magana ta karshe da zanyi a kan wata yarinya ne dana yaudara sunanta Najaatu Ina fatan maganar nan da na keyi tana ji kuma tana kallonta, Najaatu ina rokon ki daki yafe min abunda nayi miki ba ke kadai bama da duk wanda na zalinta ina rokonsa ya yafe min ni tawa takare a duniya.” Sai kawai yayi qasa da kansa hawaye na cigaba da zubowa daga idansa

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button