MADADI Page 91 to 100

Lokacin da labarin abunda ya faru ya isa kunnan iyayen Bash sun shiga tsananin tashin hankali da nadamar abunda suka aikata, dan jin bayanin da Bash yayi yasa jamaar gari sun sake gazgata maganar dama kowa yana tunanin sune suka dorashi a kan hanyar banza gashi yanzu sunzo suna nadama, ‘Yan jarida kuwa ai kewaye Alhaji Aminu sukayi wai lallai sai yayi musu qarin bayani dangane da jawabin da Bash din yayi kafin mutuwarsa.
Najaatu kuwa al’amarin yayi masifar d’aga mata hankali tayi kuka sosai tayi nadamar rayuwa hajia kasa gane kanta tayi a gidan, sai da ta dinga yi mata nasiha gami da kawo mata misalai sannan ta daina kukan da takeyi ammafa kullum da daddare sai ta rungume ‘Danta taci kukanta ta koshi!! sannan take jin sassauci bata ta’ba tunanin zata auri Mutum mai miyagun halaye ba sai gashi ta auri bash wanda ya tara munanan halaye harda albarka haihuwa a tsakaninsu hakika ta tabbata wannan al’amarin da ya faru da rayuwarta qaddarace dan da tasan abinda zai faru kenan da bata bujirewa auran da iyayenta sukayi mata ba, A duk sanda zata kalli fuskar d’anta ji take zuciyarta na karaya ta dinga tunanin halin da zai shiga idan ya girma yaji labarin ta’addacin da ubansa ya aikata kafin a kashe shi, wannan tunanin yasa ta dinga wata iriyar rama kafin tayi ar’bain duk ta fige kullum cikin tunani da nazarin yaya rayuwar d’anta zata tashi take. tunda wanda take tunanin zai tallafeta shima ya daina sakar mata fuska ya nunawa duniya cewa ba zai mayar da ita ba dan yanda yake nuna mata halin ko’in kula yasa kowa ya fahimci munufarsa ita dashi gaisuwa ce kawai ke had’a su watarana har yazo gidan ya tafi bata sani ba, dan zaman daki ta aura yanzu tafi so ta kadaice ita kadai tayi tunanin abinda zai fishsheta………….Allah Sarki Ramlatu itace ke hidima da (Daddy) sunan da suke kiran yaron dashi kenan, Tayi masa wanka ta shiryashi ta goya shi a bayanta mutukar kinga yaron a hannun uwarsa to nono zai sha, Najaatu tana jin dadin yanda Ya Ramlatu da sauran mutan gidan ke nuna kulawarsu a kan yaronta
To haka rayuwa ta cigaba da tafiya yau fari gobe baki Najaatu nata hakuri da halin ko’in kulan da Abbah Abbas ke nuna mata, ita abun sai ya dinga bata mamaki ya damu da d’anta amma ita kallo bata isheshi ba ko gaishe shi tayi baya kallonta yake amsawa amma wani sa’in idan yazo za taji shi suna maganar Daddy da Yaya Ramlatu wani lokacin ma har daukar yaron yake yay masa wasa kafin ya tafi. sai tayi ta mamakin al’amarin wallahi ita ta dauka dukkanin irin kulawar da yake nuna mata a baya yana so ta haihu ne ya mayar da ita sai gashi ya juya mata baya lokaci guda ko kallonta ma baya yi.
Yau kwanan ta sittin da uku da haihuwa, hankalinta gabad’aya yana kansu Mmn Sajida dan kullum sai sunyi waya ita Mmn Sajida har fushi tayi saboda dukkaninsu suna lissafe da kwanakin haihuwarta tace saboda taga suna so su ganta da abunda ta haifa shiyasa take ja musu rai shikkenan zasu cireta daga rayuwarsu kamar yanda ta watsar dasu.
Wannan maganar da mmn sajida tayi ta tayar mata da hankali sosai taji tana sha’awar zuwa gurinsu, sai ta yanke shawarar sanar da Abbah Abbas din domin taji me zaice akan tafiyar.
Lokacin data kira wayarsa yana tare da Zainab da cikinta ya tsufa dan kamar ma naquda take a tsaitsaye dan dai haihuwar fari ce shiyasa basu gane ba amma dai bata da cikakkiyar lafiya…….Zainab ta dauki wayar tana dubawa, My dota ta gani na yawo a fuskar wayar, tasan Najaatu ce sai tace”Abbah Mufida Najaatu na kiran wayarka……Domin ya sake nuna mata babu wata alaqa a tsakaninsa da ita yace “Dauka mana.” Da sauri ta daga wayar tana sallama, Najaatu taji rashin dadin jin muryar Zainab sai dai ta daure tace”Dan Allah ki bawa Abbah wayar zanyi magana dashi.
Zainab tace”Kada ki damu shine yace na dauka ina sauraranki.” Najaatu taji kanta ya sara! da kyar tace”Aa ki dai bashi wayar.” Zainab murmushi tayi cikin sigar kuntatawa tace”Wallahi da gaske nake miki gashi ma yana kimtsawa zai fita kuma da umarninsa nake magana dake ki fad’i maganarki dani dashi duk daya ne.” Najaatu ta dinga jin kamar ba’a guri guda take ba dan wani irin jiri ne ya shiga d’ibanta, sai kawai ta kashe wayar ta jefar da ita lafiyayyun hawaye suka shiga zobowa a kumatunta, wannan wulakanci dame yay kama? Lallai Abbah Na shirin ya dasa mata ciwo a cikin zuciyarta, ashe bai san yanda take bala’in jin kishin matarsa ba zai ce ta daga mata waya aikuwa ba zata qara kiransa ba, kuma tafiyarta zatayi tunda dama ba zamansa take ba
Sai da taci kunanta ta qoshi tukkuna taje ta sanar da hajia maganar zuwa jos din Hajia tace” Hakan yana da kyau sai ta fara shiri.
Bangaransa kuwa koda ya gama shirinsa bai tambayi zainab komai ba tunda hands free wayar take duk yaji komai ya kar’bi wayarsa yayi tafiyarsa harkokinsa, ita kuwa Zainab a ranar yini tayi cikin farin ciki da annushuwa dan duk ciwo ciwon da take ji a jikinta daina ji tayi sabida abunda tayiwa Najaatu na quntatawa kuma taji dadin yanda ya bata goyon baya d’ari bisa d’ari.
Bayan kwana uku Naja’atu ta shirya kayanta tsaf hajia ta shirya mata tsaraba mai yawa, tace ta kai musu domin sun cancanci abinda yafi haka, a ranar da zata tafi ta shiga gidan Baba Malam da wurwuri tayi musu sallama itama Baba Talatu ta bata abubuwan tsaraba tace ta kai musu, sannan tayi mata fatan dawowa lafiya.
Sai da zata tafi hajia tace”Kinga ikon Allah ko na sha’afa wallahi duk zuwan da Abbansu Saddiqa keyi ban fada masa ba ko kin kirashi a waya ne.”? Da sauri tace”Eh shekaran jiya na fada masa.” Hajia tace”To shikkenan dama dan dai kada ya samu labarin tafiyar daga baya ne yasa nayi maganar to Allah ya saukeku lafiya a gaishe mana dasu da kyau.
Naja’atu tace zasuji insha Allahu Hajia……Tare suka fito harabar gidan suna tsaye suna kallonta ta shiga mota direba yaja suka fita daga gidan…………Abbah Abbas lokacin daya samu labarin tafiyar ranshi yayi masifar ‘baci! ya za’ayi saboda rashin hankali ta dauki yaro karami a lokacin sanyi tayi tafiya mai tsayi dashi, shifa gabad’aya garin jos bai masa ba shiyasa bai ta’ba yi mata zancan zuwa ba, ashe jira take ta haihu ta dauki kafa ta tafi ba tare da ta sanar masa ba(Matarka ce ita da zata tsaya fad’a maka????) Hajia ta dinga tausarsa da fadin ita bata san bai sani ba wallahi amma ai ba wani abu bane dan taje ta nunawa mutanan abunda ta haifa saboda sun cancanci hakan……Yace.”Hajia ba hana zuwa anyi ba a qalla dai ta bari yaron bayanta yayi kwari ki duba kiga yanda ake busa iska a gari tana iya zuwa da yaron ya samu wata matsalar yanayin gidan da zataje bashi da kyau da tsayin katanga akwai matsala sosai.” Hajia ta dinga mamakin maganarsa tace”To ai lalura a ko’ina ma daukarta akeyi kuma ta tafi da kayan sanyi nasan zata kula dashi.
Shuru kawai yay ya miqe tare da fadin shi zai tafi.Hajia tace to a sauka lafiya, hanyar futa ya kama ta bishi da kallo tana mamakin son ‘ya’yansa.
Kasa hakuri yay yana driving ya shiga kiran wayarta, lokacin har ta sauka tana tare dasu Mmn Sajida sai gaishe da juna sukeyi, su Walid da ‘Ya’yan Mmn Ladi sun kewayeta tana ta basu tsarabar da taje musu da ita.