MADADI Page 91 to 100

Koda ta duba wayar taga number sa ce sai ta cigaba da abunda takeyi, taki dauka sai da ya kira sau uku tukkuna ta daga, tana kokarin gaisheshi ya dakatar da ita……”Ashe baki da hankali Najaatu wa kika tambaya wanda ya baki izinin tafiya wani gari? ashe kina nan da halinki na taurin kai ko.”
Kai tsaye tace”Abbah yi hakuri dan Allah kwana hudu da suka wuce na kira wayarka na tambayaka sai dai idan mantawa kayi.”
Yace.”Ke bana son karya yaushe kika kira ni kika tambaye ni ai saboda kin san bazan bari ba shiyasa kika ‘ki sanar dani.” (Takwara zo kiga karfin hali????Tace”Wallahi na kira wayarka Zainab ta dauka kuma na fad’a mata maganar sai dai idan itace bata fad’a maka ba.”
Shuru yay yana tunanin maganar…….” To Gobe Dan Azimi zai zo ya dauke ki dan haka duk wanda kika san zaki gaisa dashi a garin kiyi kokarin gaisawa dashi kafin gobe.” Yana gama maganarsa ya kashe wayarsa……….
*Littafin na kudi ne…!*
Koda zaki ganshi a groups na sata ne idan kina bukatar ki biya kudin karatu ga yanda abun yake Vip group #600 normal group #300 account… 0542382124….Binta umar gtbank…idan katim waya zaki tura kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
_Abbah Abbas ka janyo ‘yan group yau na caccakar ka????????♀️ Mum Basma tace idan ka tsaya kallon ruwa kwado zaiyi maka kafa, ita kuma Sakina tace” Kana ruwa???? sistar Habiba tace Dantalle ya shigo kawai ayi dashi tunda kai ka tsaya wasa! To nima dai nace ka ajiye makaman ka dan idan ka tsaya jan aji za’ayi maka shigar sauri Najaatu dai a yanzu allura cikin ruwa ce (mai rabo ka dauka)_
*MADADI74*
Najaatu shuru kawai tayi tana bin wayar da kallo, mamakin maganarsa take wai zai turo Dan Azimi gobe ya dauketa lallai aikuwa yanda yazo haka zai koma domin kuwa bata tunanin zata bishi to wai nauyin waye a kanta da zaice lallai sai ta dawo gida me za tayi masa bayan baya kulata sannan kullum yana tare da iyalinsa ita kuma sai ya hanata zuwa inda zata ji sassauci zuwanta gidan Mmn Sajida ya saukar mata da nutsuwar zuciya ko babu komai zatai kwana biyu bata saka shi a idonta ba, domin watarana ganinsa yana janyo mata abubuwa da dama hakuri kawai takeyi tana bin rayuwa a yanda tazo mata.
Mmn Sajida ta kalleta a sanyaye tace”Najaatu naga jikinki yay sanyi ashe ba’a sani ba kika zo.”? Kallonta tayi tace”Waye ya fad’a miki haka.”? Kai tsaye tace”Gashinan mahaifinki ya kira waya yana miki fad’a.” Mmn Ladi tace”Eh ai nima shiyasa kika ga jikina yay sanyi wallahi.
Najaatu murmushi tayi a nutse tace”Wai ku waye ya fad’a muku Abbah Abbas mahaifina ne.”? bude baki sukayi suna kallonta, ta sunkuyar da kanta tana dan murmushi wanda ya tsaya iyakacin lebenta.
Mmn Sajida tace ”To idan bashi ya haife ki ba waye shi a cikin rayuwarki.”? Tana girgiza kanta tace”Shine mijina na fari wanda na baku labarinsa farkon zuwana garin nan.
Suka tsira mata ido suna mamakin maganarta, kwallah ta cika mata ido tace”Kuna mamaki ko? ni kaina ina mamakin kyautayi da tausayi da kyautatawa irin nasa dukkanin irin abubuwan da nayi masa bai sa ya watsar dani da al’amurana ba, yana tsaye a kaina da dukkanin bukatuna.” Mmn Sajida tace”Lallai Najaatu kin tafka babban kuskure a baya waye ya fada miki ana samun nagartattun mutane irin wannan mutumin? yanzu dama a kan an aura miki shi kika gudo garin nan yanzu dan Allah meye aibunsa meye kuma abun’ki a tattare dashi.”? Tana kuka tace”qaddara Mmn Sajida qaddarar wannan yaron dake hannuna ce ta kawo ni garin nan har na had’u daku….Wallahi har bana so na tuno abubuwan da suka faru a baya Mmn Sajida ni da kaina nasan na tafka kuskure babba! wanda yanzu nake nadamar aikatashi, yanzu gashi inaji ina gani Abbah yafi karfina sai dai na kalleshi da ido Mmn Sajida a yanzu ne nake masifar so nayi zaman aure dashi shi kuma yana nuna baya so, wallahi bansan iya adadain son da nake masa ba a cikin zuciyata saboda mutumin ya cancanci a soshi duk wata sadaukarwa yayi min yana kanyi min babu namijin da zan aura na samu nutsuwar da nake bukata, Mmn Sajida ba zan ‘boye muku halin dana ke ciki ba wallahi saboda halin ko in kula da yake nuna min yasa naji zaman garin ya gundureni na tattaro na tawo nan kuma bana tunanin zan koma a kurkusa sai na huta tukkuna.”
Mmn Ladi ta sauke ajiyar zuciya tace”Gaskiya Najaatu naji miki haushi da takaicin rasa wannan mutumin to amma tunda kin jingina al’amarin a matsayin qaddara muma zamu jingina shi a hakan ammafa wallahi kema da akwai son zuciyarki wanda shine ya kara sanyawa kika kai kanki ga wahala! saboda haka ni dai shawarar da zan baki wallahi ki lalla’ba da wayo da siyasa ya mayar dake dan nima na tabbatar da cewar a gurinsa ne kadai zaki fi samun nutsuwa da kwanciyar hankali saboda yanzu duniya kowa kansa ba kowane namiji ne zai yarda kije masa da d’anki ba.
“Mmn Ladi wane dabaru zanyi ya mayar dani ni bazan iya fada masa baki da baki ba, na hakura zan cigaba da rainon yarona har Allah yasa ya girma, shikkenan idan na samu daidai dani sai na aura.
Mmn Sajida tace.” Ni kuma sai nake ganin kamar yana jira yaron ki yay wayo ya bijiro da maganar kome din kin san fa koda zai mayar dake gidansa ba zai mayar dake kina da d’anyan jego ba, wallahi ko kaffara ba zanyi ba yana sonki dan da baya sonki ba zai dinga yi miki wahala ba, haba ki duba fa ki gani shine yazo ya daukar ki anan sannan lokacin da kika kwanta a asibiti kina kiran wayarsa ko minti ashirin ba’ayi ba ya turo da kudiin da’a ka bukata……….Duk da kin kasance mai laifi a gurinsa hakan bai hanashi kula dake ba, ki kwantar da hankali da kansa zaiyi miki maganar ki koma gidansa amma kema dole ki dan yawaita kwalliya da gyaran jikinki da kowane lokaci ya dinga ganinki tsaf tsaf zaki janyo hankalinsa sannan kina kiransa a waya kina gaisheshi.”
Najaatu murmushin takaici tayi tace”Mmn Sajida sau nawa zan kira wayarsa yasa matarsa ta dauka! a gabanki ma fa hakan ya ta’ba faruwa Abbah wani irin mutum ne wanda baka gane gabansa da bayansa.”
Mmn Ladi tace”Kome baud’ewar halinsa mace na iya sanja shi saboda haka idan kika mayar da hankali akan shawarwarin da muke baki zasu taimake ki.”
Najaartu shuru kawai tayi tana sauraran maganganunsu, tana daukar na dauka tana watsar dana watsarwa bata tunanin zata tunkareshi da maganar ya mayar da ita gidansa idan ya tausaya mata da yaronta ya mayar da ita haka take so idan kuma yana ganin bashi da ra’ayi sai ta hakura ta barwa Allah.
Sai bayan taci abinci ta nutsu tukkuna ta shiga fito musu da tsarabar data kawo musu , kowacce turmin atamfa biyu da mayafi da takalmi sai sabulai na wanka dana wanki da kayan kwalliya irin na mata.
Sosai suka shiga yi mata godiyar hidimar da tayi musu, ashe da sauran godiya, dan kudinta na haihuwa data samu kimanin dubu saba’in da wani abu a ciki ta dauko dubu hamsin ta kawo musu
Mmn Sajida ta miqawa tace su raba….Mmn Sajida ta riqe kudin a hannunta tana kallonta cikin d’umbun mamaki! Murmushi tayi ta kalli Mmn Ladi tace”Mmn Ladi naki kudin sai kiyi kokarin ki fara sanaa dasu kafin naga abunda Allah zaiyi anan gaba insha Allahu idan na samu yanda nake so zan qara miki wasu.