MADADI 1-END

MADADI Page 91 to 100

Mmn Ladi fashewa tayi da kuka ta rungumeta tana fad’in “Wallahi Najaatu na rasa bakin da zan gode miki ashe ke din alkairi ce a tare damu muna mutukar alfahari da sanin da mukayi miki wallahi Kinyi min abunda d’an uwa na jini baiyi min ba, a cikin ‘yan uwana akwai masu hali amma babu wanda yay tunanin dauko kwabonsa ya bani da sunan naja jari nayi sana’a sai ke da Allah ya had’ani dake kin gyara min aurena kuma kin dauki kudi kin bamu, kin kawo min babban zani irin wanda banta’ba daurawa ba, babu abinda zance sai dai nace Allah ya saka miki da alkairi ya biya miki dukkanin bukatunki.

 Naja’atu tace”Haba Mmn Ladi meye abun kuka wallahi wannan ba komai bane a gurina idan ina da abunda yafi haka zan baku domin kuma kun taimakawa rayuwata a lokacin da nake bukatar taimako saboda haka ki daina kuka kina gode min Allah ne ya had’amu ina fatan zumuncin mu ya d’ore har ‘ya’ya da jikoki.” Mmn Sajida tace”Insha Allahu Najaatu Allah zai cika mana burin mu kuma kamar yanda muke zumunci insha Allah ‘ya’yanmu suma za suyi.”

Da wannan addua ta Mmn Sajida suka rufe maganar suka shiga hirar Bash da hukuncin da’a ka yanke masa.

Laifin Najaatu ya shafi su Halisa a tunzure ya shiga gidan, girkin Halisa ne ganin yanda ya shigo yana shan qamshi yasa bata tunkari inda yake ba gudun wulakanci yasa taje tayi kwanciyar a dakinta tana kallo, har ya gama abinda yake a falo ya shigo yay shirin kwanciya, zama yay gefan gado da wayarsa a hannunsa. Number Najaatu ya nema

Lokacin dare yayi dan goma da rabi ta wuce duk sunyi shirin kwanciya Mmn Sajida dalilin zuwan Najaatun yasa bata fita sana’arta ba, suna hira sama sama kiran wayarsa tasa ya shigo.

Ta dauka tana dan tunani to me ya kirata yace mata? Shawarar dasu Mmn Sajida suka bata ta tuna, sai kawai ta daga wayar tana wani maqale murya tace”Hello Abbah! barka da dare.” Wani irin yarrr! yaji a jikinsa sakamakon jin yanda muryarta ta ratsa jikinsa, tamaza yay yayi gyaran murya as’usul yace.”Barka dai ina fatan kin suturta yaron nan da kayan sanyi saboda kin san dai yanda ake sanyi gashi na lura gurin da kike bashi da tsaro da sauransu.”

Dan murmushi tayi tana kallon Mmn Sajida, ta sake kashe murya tace” Abbah ni baka damu dani ba kenan kana tambayar na suturta Mai sunanka nima ai ina jin sanyi sosai a jikina.”! Cikin shagwaba ta k’arasa maganar.

Shuru yay na minti biyu kafin yace.”Ke ai kin girma sanyi ba zai miki lahani ba kamar shi so sabida shi na kira wayarki sannan kuma na sake tunasar miki da abinda na fad’a miki d’azu! gobe da wurwuri Dan Azimi zai zo ya daukeki.”

Kamar za tayi kuka tace”Allah ni bazan dawo gobe ba, Abbah wa na’ajiye a garin kano da zan takurawa kaina dawowa ni dai dan Allah ka bari na kwana biyu a gari jos dan ina jin dadin garin sosai da sosai.”

A hasale yace.”Ke! ashe baki da hankali wannan garin duk babu mutunin arziki a cikinsa ashe kina so ki sake haduwa da wani mara tarbiya kenan( Afuwa mazauna wannan garin banyi da niyyar naci muku fuska ba labari ne yazo a haka a gafarce ni garin jos akwai masu tarbiya sosai ga misalin irinsu Mmn Sajida nan nayi)……Tace”Haba dai Abbah ba duka a ka zama d’aya ba Wallahi su Mmn Sajida suna da kirki da tarbiya kuma ni da naje ziyara mai zai had’a ni da wani saurayi ko bazawari babu ruwana dasu.

Yace.”Ni dai na fad’a miki gobe ki zauna cikin shiri domin hankalina bai yarda da zamanki a wannan gari ba.” Kashe wayar yay bai saurari ta bakinta ba…….Halisa ta miqe zaune tana hararar bayansa ji take kamar ta makeshi! saboda haushi yana yaudarar kansa yana yaudararsu to meye nasa na damuwa dan ta tafi jos da har zai ce zai tura a daukota. tsaki taja a zuciyarta kafin tace”To wai kai meye na damuwa dan ta tafi wannan gari? babu fa nauyin kowa a kanta da kake cewa ta dawo haba ai ka kyaleta ta huta su gaisa sosai da wannan mutanan da sukayi mata hallaci.” 

Yana jinta yay shuru sai ma ya fara kokarin kwanciya yana kokarin rufe kafafunsa, Halisa bata san sanda taja tsaki ba tace”Abban Mufida kenan ka tsaya wasa wallahi sai dai kaji anayi dan Najaatu a yanzu allura cikin ruwa ce da d’anyan jegon da take dashi ba zata rasa me auranta ba……Fad’in wannan magana da Halisa tayi sai ya fusata! ya miqe zaune ya dinga zazzaga mata masifa da fad’in “mahaukacin Namiji ne zai auri mace da d’anyan jego saboda haka kada ta kuskura ta sake yi masa irin wannan magana.

Halisa itama ta fusata tace” To itama kada ya sake zuwa gabanta yayi waya da Najaatu tunda abun nasa ya zama rainin hankali, haka suka dinga cacar baki tana fad’a yana fad’a dan gabanyansu a tunzure suke kowa yana ganin ba’ayi masa daidai ba…….Gabad’ayansu Haka suka kwanta suna jin haushin juna…..

*Infaction*

_Ko wace mace kaji tace miki tana fama da infaction wai shin ya zamuyi mu kare kanmu daga wannan laluran mai wahalar magani? Idan kina da sanyi koda mijinki bai dashi sai ya samu….Ko kuma ke baki dashi mijinki nada shi to sai kin samu, idan ya kasance duk kuna dauke da lalurar sai ku durfafi shan magani a tare! dan idan daya yasha daya bai shaba to akin banza kukayi ciwon yana nan babu inda zaije……….Kina budurwa kina kyaikayin gaba da zubar da farin ruwa gashi an kusa bikin ki kinja bakinki kinyi shuru baki fadawa mamanki ba, to zaki haifarwa da kanki matsala babba dan idan kikaje gidan mijinki da wannan ciwo kika shafa masa zai miki mummunar fahinta ya dunga yi miki wani irin kallo na daban……… saboda haka mutukar kina da matsala irin wannan maza ki sanar da mahaifiyarki kafin ki sanar dani mahaifiyarki itace mafi kusa dake kuma ita ta haifeki babu kunya a tsakaninku! Ki fada mata komai zata kaiki gurin mai magani….Ni shawara ce kawai a tsakaninmu._

*Idan da tsumma kike using a lokacin da kike jin al’ada to ya kasance kullum kina sanjawa sau uku ko sau hudu, sannan idan kin wanke tsumman ki dinga sashi a rana ya bushe kwayoyin cutar zasu mutu…….mutukar kina barin matuncin ki da danshin ruwa to ba zaki rabu da kyaikyayin gaba ba, wannan guri an fiso kullum ya kasance a bushe…….Idan da pad kike using lokacin haila yana da kyau kina sanjawa a kai kai kada kisa tun safe ki barshi sai dare dole gabanki yayi miki kyaikyayi daga haka kuma kwayoyin cuta su shiga jikinki, wannan kyakiyayin masifa ne, saboda haka dan Allah muyi hattara????????‍♀️*

Vip group #600 normal group #300 accont…0542382124….Binta umat gtbank…WhatsApp number… 07084653262

_Yau mura ta hana ni nayi muku post akan lokaci duk naga adduoin ku dana pravite dana group ????????‍♀️ Nagode sosai Binta tana tare daku insha Allah????_

*BHRMBN 74_75*

Da maganar Halisa ya kwanta bacci ya kuma tashi da maganar a cikin ransa, ya jima yana nazarin maganar da tunanin abinda zai biyo baya a jos din mutukar an san ita din bazawara ce to tabbas maganar Halisa na iya kasacancewa a samu wanda zai ce yana sonta duk da jegon da take dashi, dan haka yana dawowa daga masallaci ya nemi number wayar Dan Azimi suka gaisa da juna yace.”Ina fatan dai ka shirya ka tafi da wuri bana so kuyi shigowar dare.

Dan Azimi yace.”Eh gani nama fito Insha Allahu yanzu zan tafi, Yace.” to Allah ya kiyaye hanya inda ka sauka sai ka kira ni ka sanar dani .” Dan Azimi yace.”Insha Allah ranka ya dade.” Sallama sukayi ya kashe wayar ya miqe ya fita falo….zama yay kan kujera yana jiyo motsin Halisa a kicin, tsabar ‘bacin rai Halisa ko gaisheshi ba tayi ba, yana kallonta ta fito daga kicin ta nufi dakinta ko kallonsa ba tayi ba, miqewa yay yana girgiza kansa ya nufi gurin Zainab, babu kowa a falon lokacin da shiga sai ya nufi dakin yaran sa domin duba su, suna tare da Baba Larai tana taimaka musu da shirin makaranta, a nutse yaran suka gaishe shi ya amsa cikin kulawa shima ya gaishe da Baba larai ya tsaya suka danyi maganar yaran da ita kafin ya fita daga dakin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button