MADADI Page 91 to 100

Zainab tana zaune kan dadduma tunda tayi sallah ta kasa motsawa daga inda take marar ta ce take wani irin ciwo….Cikin mawuyacin hali ya sameta, hankalinsa ya tashi ya taimaka mata ta miqe tsaye, yana tambayarta abinda ke damunta, cikin halin ciwo ta fada masa cewar mararta ke ciwo, zaunar da ita yay gefan gado yace.”Bari na kira Baba Larai ta dubaki ko haihuwa za kayi….Fita yay daga dakin sauri, koda baba larai taga yanayin Zainab a take ta fahimci cewa haihuwa za tayi, tace”Alhaji haihuwa yarinyar nan za tayi amma yana da kyau aje asibiti domin a sake tabbatarwa, Yace.”Okey bari na sanar da Halisa….Halisa jin cewa zainab zata haihu yasa ta biyo bayansa halin da taga Zainab a ciki yasa jikinta sanyi, kayan haihuwa kawai suka hada suka nufi asibiti Zainab duk ta rikice da ihu! gabadaya ta manta da addua sai ihu take tana kiran a taimaka mata gabadaya hankalinsu ya tashi harshi Abbah Abbas din dake driving hankali a tashe ya kara karfin motar suka isa asibitin nasarawa.
Zainab bata dade tana doguwar naquda ba Allah ya sauketa lafiya inda ta haifi ‘ya mace mai kama da ita sai dai ta dauko hasken fatar babanta, Abbah yayi farin ciki sosai ganin yanda Allah ya raba lafiya maijego da babynta lafiyarsu lau………Kafin su bar asibitin Abbah ya sanar da duk wanda ya dace ya san haihuwa, awa biyu kacal sukayi a asibitin aka sallamesu….Suna koma gidan suka tarar da ‘yan uwan Zainab sun cika gidan, Abbah ya tsaya suka gaisa a gurguje ya fita ya basu guri
Bangaran Halisa ya koma domin ya kimtsa jikinsa. Allah sarki Halisa ganin yanda yake ta murna da haihuwar zainab din yasa itama taji tana sha’awar haihuwa tunda ta haihu sau biyu bata sake haihuwa ba, mufida yanzu shekaranta goma sha uku amma ko ‘batan wata ta sake ba, zama tayi ta zabga tagumi abin duniya ya isheta.
Ganin ya shigo dakin ne yasa ta miqe ta fita ta basa guri gabad’aya duniya tayi mata zafi tana ta nadamar cutar da kanta da tayi tana tunanin ko magungunan turawan data dinga d’ubga ne ya toshe mata mahaifa gaskiya dole ma taje asibiti a dubata tunda ba wuce haihuwa tayi ba.
Zainab na tsakiyar ‘yan uwanta suna ta zugata ita kuma ta saki baki sai fad’a musu karya da gaskiya takeyi…Wata yayarta tace”To yanzu ai duk wani abu da kika san kina bukata ki rubuta masa kuma kada ki sake kiyi amfani da kyan babyn nan ya sake siya miki wasu, sannan kice kina so ya siya miki set gold zakiyi fitar bikin suna dashi.
Zainab tace”Duk abinda nake so yana kaina ke har mota nima sai ya siya min tunda na tabbatar wacce aunty Halisa take hawa shi ya siya mata.
Yayar tata tace”Ato idan kika tsaya wasa sai ki zama koma baya tunda kin haihu dashi ai kin zama kujera a gidansa….Zainab murmushin jin dadi tayi ta juya ta kalli babynta dake kwance a gefanta.
Yaya Ramlatu da Hajia Rabi da Baba Talatu ne sukayi sallama a dakin.
Da sauri Yayar zainab ta miqe tana musu barka da zuwa ta basu guri suka zauna suna gaisawa, Babyn ta dauko ta miqawa baba talatu da fadin “Ga bakuwar duniya mai kama da babanta.” Baba Talatu ta karbi yarinyar tana murmushi cikin nutsuwa tace”Masha Allah Allah yayi mata albarka babu shakka yarinya ta dauko gida Allah y raya mana ita.
suka amsa da amin. Baba talatu ta miqawa Hajia Rabi itama ta karbe ta tayi mata addua sannan ta miqawa Yaya Ramlatu.
Yaya Ramlatu tayi murmushi idonta a kan babyn tace”Yarinya dai ta dauko hasken fatar gida amma kuma kammaninta sak na uwarta.” Zainab tayi saurin kallonta tana mamakin maganarta, ita kuwa yayarta cikin ya’ke tace”Aikuwa baki ji bahaushe yana cewa kyawun d’a ya gaji uwarsa ba.” Ya Ramlatu tayi dariya cikin sigar kuntatawa tace” Kyawun d’a ya gaji ubansa ake cewa yarinya ta gaji ubanta gurin haske fata kammani kuma na uwarta ne Allah yasa kada ta dauko halinta.”
Hajia rabi tace”Wace irin magana ce wannan.”? cikin takaici Ramlatu tace”Hajia duk sanda zan kalli yarinyar nan sai na tuna sanda ta wanke ni da mari ni kam a tarihin rayuwata ba zan taba mancewa da ita ba.”
Jin wannan magana yasa ‘yan uwan Zainab jikinsu yay sanyi kunya duk ta dabaibayesu, Zainab kuwa tuni ta fashe da kuka gabanta sai faduwa yake Ramlatu tazo ta tona mata asiri a gurin ‘yan uwanta
Yayar Zainab tace”Dan Allah kiyi hakuri ‘yar uwa maganar tone tone duk bata taso ba alheri da farin ciki ne ya kawo muku gidan nan saboda haka idan zainab tayi miki wani wanda bakiji dadinsa ba ki gafarce ta akwai kuruciya a tare da ita
Ramlatu tace”Iskanci dai ba kuruciya ba, ai magana ni ta wuce a gurina wallahi kawai dai idan na tuna al’amarin raina yake baci.”
Cikin fusata! Yayar zainab din tace” Ashe dama abunda kike yi kenan yanzu kamar wannan matar tana a matsayin yayar mijinki ki fitar da hannu ki mareta to Sai ki bata hakuri tunda ke baki da mutunci.”
Zainab na kuka tace”Yaya Ramlatu ki gafarce ni wallahi tsautsayi ne.” Cike da takaici tace “Dena kuka ai na yafe miki tuntuni saura kuma idan ya dawo ki fada masa ga abinda nazo nayi miki kisa shi ya kawo min rundunar sojoji.” Zainab tace”Wallahi ko wancan karan ma bani nasa shi ba kiyi hakuri.”
Baba Talatu tace”Ke kam Ramlatu abu baya wuce wa a gurinki ne? yarinyar nan ta baki hakuri magana ta kare dan Allah.
Yaya Ramlatu tace”Magana ta wuce baba insha Allah bazan sake tada ita ba.”
Karfe uku saura na rana Dan Azimi yayi parking din mota a kofar gidan Mmn Sajida, sai dai me? yana fitowa yaga katon kwado kulle da kyauran gidan…..Ya jima yana mamaki kafin ya bude motar ya zauna ya shiga kiran wanda ya aikoshi, ya sheda masa abunda yake faruwa.
Abbah jin abinda dan Azimi yake fad’a masa yasa ko gama sauraransa baiyi ba ya kashe wayar da sauri ya nemi number ta……Lokacin suna gidan bikin sunan k’anwar Mmn Ladi, dan da zasu tafi cewa tayi ba zata zauna ita kadai a gida ba sai ta shirya tsaf sukayi tafiyarsu bayan tasan da maganar zuwan Dan Azimi.
Hayaniyar jama’a ya hanata taji abinda yake cewa sai kawai ta kashe wayar ta ta ajiye tasan dai maganar zuwan Dan Azimi zaiyi mata ita kuwa ba taga dalilin da zai sanya ta koma gida a yanzu ba.
Abbah ya shiga mamaki mai tsananin gaske yau shi Najaatu ta kashewa waya! to wai shin ma ina ta tafi a garin da bata da kowa hakika yarinyar nan na nema ta d’ora masa ciwon zuciya.
Wayar ya sake kira sai ta miqe daga cikin mutane ta samu gurin da babu hayaniya sosai ta daga a sanyaye tace”Abbah ina kwana wallahi ina cikin jamaa ne shiyasa bana jinka sosai.”
Yace.”Kina ina Dan Azimi tuntuni yazo daukar ki bakya nan to har in dai na isa dake duk inda kike kiyi maza ki koma yana zaman jiran ki.” Abbah dan……Katse ta yay da sauri yace.”Kina so ki ‘bata min rai ko? na fad’a miki bana son zamanki a wannan garin nasan dai daga jiya zuwa yau duk wanda kika sani a garin kin gaisa dashi to zaman me za kiyi kuma gashi nan kwana d’aya kacal da zuwanki kin fita yawo shin me kike so ki zama? saboda haka na gama magana idan na isa na fad’a miki kiji to ki tabbatar kin biyo Dan Azimi kun
n dawo gida a tare.” Kashe wayarsa yay bayan ya gama maganarsa.
Tun kafin ta zauna Mmn Sajida ke kallonta, tace”Najaatu yana ga jikinki a sanyaye ina fata ba wata matsala bace.”