MADADI 1-END

MADADI Page 91 to 100

A sanyaye tace”Abbah ne ya kira wai yanzu haka Dan Azimi nacan kofar gidanki yana jirana yace lallai dole sai na bishi mun koma gida a tare ni kuma wallahi bana jin zan iya binsa sai dai idan ya gaji da zama ya tafi bari ma kawai na kashe wayar ta kada ya sake kira.

Mmn Sajida tace”A’a bada ni za’ayi wannan rashin hankalin ba, Najaatu ba zaki had’a kai dani ki ‘batawa wannan bawan Allahn rai ba, tunda yace ki tafi to gaskiya yana da kyau kibi umarninsa kada ki nuna masa bai isa dake ba, haba keda kike nema ya mayar dake gidansa me zai sanya ki dinga yi masa gaddama akan dukkanin abinda zai umarceki kawai ki tashi mu tafi na tayaki hada kayanki ai mun gaisa kuma insha Allah muma zamu inda kike.

Murya na rawa tace”Mmn Sajida korata kike a gidanki? Wai shin dan Allah idan na koma me zanyi masa zama fa kawai zanyi a gida shi kuma kullum yana gurin iyalinsa to ba gwara na zauna na samu nutsuwa ba.”

Mmn Sajida tace”Lallai ta yaro kyau tace bata qarko wallahi Najaatu baki da wayo har yanzu….Mutumin nan dafa baya sonki ba zai damu dake haka ba, yanzu dama kika samu a hannunki wacce zaki sake janyo hankalinsa kanki ta hanyoyi daban daban, baki da wayo wallahi har yanzu kiyi tunani akan shawarwarin dana baki jiya da daddare wallahi mutukar kin dauki shawara ta baza’a ja dogon lokaci ba zai kawo kansa gurinki.

Najaatu tayi shuru tana nazarin maganar da Mmn Sajida keyi, ” A sanyaye tace.” Shikkenan Mmn Sajida zan gwada Daukar shawararki nagode sosai da kulawarki a kaina.”

Mmn Sajida tace”Babu komai wallahi aike yanzu ‘kanwata ce duk abinda nayi miki ban fadi ba, saboda haka yanzu tashi muje ki shirya kayanki.”

Miqewa sukayi suna gyara mayafi, Mmn Ladi ta fito daga dakin mejego ganin sun miqe tace”Aa ina zakuje naga kun miqe.”? A takaice Mmn Sajida tayi mata bayani…Mmn Ladi tace”Eh lallai haka shine yafi alkairi dake Naja’atu mungode kwarai da ziyara kuma insha Allah muma muna kan hanyar zuwa……Tare suka fita daga gidan Mmn Ladi har bakin titi ta rakasu sai da ta tabbatar sun hau adaidaita sahu sannan ta koma cikin gidanĀ 

Dan Azimi na ganin saukar su Najaatu daga a daidata sahu ya shiga murna dama tun dazu wanda ya turo shi yake ta kiransa a waya yana tambayarsa yanda ake ciki sai bayan sun shiga gidan ne yay saurin kiransa ya fada masa cewa gata nan ta dawo nan ba da jimawa ba zasu dauko hanya.

Abbah Abbas ajiyar zuciya ya sauke kafin yace.”To Alhamdullhi Allah ya kawo ku lafiya.”……Najaatu cikin kunci da damuwa ta fito Mmn Sajida tasa mata jakar kayanta a motar dukkaninsu idan ka gansu za kagane suna cikin alhini na rabuwa da junansu Mmn Sajida sai daure zuciyarta take tana kwantar mata da hankali, sai bayan data shiga motar ne hawayen da take ‘boyewa suka shiga zuba, hannu kawai ta daga mata ta kauda kanta gefe guda…..Dan Azimi na jan motar Mmn Sajida ta juya da sauri ta shiga gidanta tana goge hawayen daya ‘kwace mata, Allah kenan mai had’a mutum da mutum.

Dan Azimi sai hira yake mata ta shareshi haushinsa takeji kamar shine yay mata laifi to shima daya lura bata son hirar sai yaja bakinsa yay shuru kawai ya cigaba da fafara gudu a kan kwalta.

daidai sanda suka shiga zaria Abbah ya sake kiran wayar Dan Azimin yana tambayarsa hanya, Yace.”Gamu a zaria ai mun kusa isowa gida insha Allah.”

Abbah ajiyar zuciya ya sauke tare da fad’in “Allah ya saukeku lafiya.” ya kashe wayar yana jin tamkar wanda aka yayewa dukkanin damuwar dake damunsa tabbas Tafiyar Najaatu garin jos ta daga masa hankali sosai dan gani yake kamar zata sake had’uwa da wani dan ta’addahn! ya yaudareta, shi da kansa a yanzu ya gazgata abinda ke damunsa a kan yarinyar ya daina wahalar da kansa da yaudarar kansa a kan cewar shi ba son aure yake mata ba so yake mata irin na uba da ‘yarsa! Gaskiya da yayi nazari sosai ya gane ba irin wannan son yake mata ba, yarinyar ita da d’anta sunyi masifar tsaya masa a rai! kuma ya yarda da maganar Halisa inda take cewa samun nutsuwar sa Najaatu na kusa dashi, hakane tunda tun jiya yake cikin tararrabi gami da rashin kwanciyar hankali saboda tayi nesa daga inda yake, gabadaya haihuwar Zainab bata dameshi ba akan yanda ya damu da lallai sai Najaatu ta dawo gida.

Sai wajejen tara da rabi na dare suka sauka…..Dama tuntuni ya gayawa Hajia cewa ya tura Dan Azimi ya daukota hajia ta dinga mamakinsa, sai dai tayi shuru kawai tana binsa da dukkanin abinda yake tsara mata akan tafiyar….Najaatu kukan takaici ta zauna ta nayi Hajia ta zauna tana ta rarrashinta da bata hakuri ita kuwa Yaya Ramlatu d’an ta dauka ta goya tana taya hajian rarrashin da take………A ranar dai Najaatu bakin ciki da takaici tayi bacci dan taji bala’in haushin abun dan dai babu yanda za tayi ne.

Sai da safe take jin labarin haihuwar Zainab a bakin Ramlatu tace Allah Ya raya abunda aka samu, Hajia tace”Idan anyi la’asar sai muje nima banje naga ‘yar ba.

Tace”To shikkenan Hajia Allah ya kaimu lafiya.

To kamar yanda hajia ta fada hakane ya kasance bayan sunyi sallar la’asar a gida suka shirya tsaf suka nufi gidan masu jegon……Gate din Zainab cike yake da ‘yan uwanta tamkar ma ranar ne suna Zainab famliy nasu suna da yawa shiyasa tunda akayi haihuwar suke shige da fice a gidan, mutum uku ma a gidan suka kwana kuma duk da auransu kawai daular gidan Zainab din ce take d’ibarsu suka zauna suna d’orawa da saukewa, ‘Ya’yan sheik Nazifi ‘Ya’yan malam kaqi halin malam ne yawanci su basu da hali mai kyau mazajensu na hakuri dasu mutuka, kuma mafi akasari almajiransa suke aure shiyasa suke rashin mutuncinsu iya san ransu sabida mazajen nasu najin kunya da nauyin tunkarar shehin malamin da wata magana, a cikinsu Zainab ce karama kuma itace ke auran Alhaji (mai kudi) shiyasa tunda suka zo suke zugata ga yanda za tayi ta gina kanta a gidan…….Harabar gurin Zainab yayi kaca kaca da kayan miya gefe katon kasko ne akan murhu wuta sai ci take anata soya nama tamkar ranar sallah.

Ganin shigowarsu Hajian gidan yasa suka dan shiga nutsuwarsu cikin girmamawa suke shiga yi mata barka da zuwa, Babbar yayar su zainab din itace ta jagorance su har inda maijego take…..Zainab taci kwalliya tamkar wata amarya da babynta a hannu tana shayar da ita cike da murna takewa hajian barka da zuwa.

Hajia Abu ta samu guri ta zauna a nutse Najaatu ma ta zauna kusa da ita tana kokarin kwance Daddy dake motsi a bayanta.

Zainab ta miqawa Hajia yarinyar kana cikin neman gindin zama ta tsuguna har qasa tana gaishe ta….Hajia cike da farin cikin ganin Zainab da ‘yarta kalau ta amsa tana fad’in “Sannu Zainab Allah ya qara miki lafiya tare da abunda kika haifa naji dadin ganinki kalau keda yarinyarki Allah ya rayata tafarkin addinin musulunci.” Zainab na dan murmushi ta amsa tare da komawa ta zauna a gefan gado.

Dakin ne yay shuru Zainab ‘Yar rainin hankali wai jira take Najaatu ta gaisheta tayi mata barka……Najaatu kuwa tunda tayi mata kallo daya ta dauke kanta,babyn kawai ta kar’ba hannun hajia tana dubata gami da sa mata albarka, a tsakaninsu babu wacce ta kulawa kowa….Hajia tayi mamakin al’amarin kwarai da gaske kuma ta fahimci abinda yake da akwai sai tayi shuru da bakinta ba wai dan bata da abincewa ba sai dan ganin kamar shuru din da tayi shi yafi alkairi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button