Uncategorized

MAKAUNIYAR KADDARA 4

 

*_Typing????_*

    *_????MAKAUNIYAR ƘADDARA!!????_*

                *_Bilyn Abdull ce????????_

_ZAFAFA 5 NEXT LEVEL_

Page 4

……………Ƙarfe kusan biyu na rana Zinneerah ta dawo gidan a gajiye. Duk uban riɗi da gyadan data fita da shi kaɗanne ya rage a botikin. Tun a sallamar farko na shigowa gidan dukkanin ɗan guntun farin cikinta ya gushe. Ba komai ya kawo hakanba kuwa sai cin karo da Yaya Kareema datai, wadda ta dawo daga Rimaye wajen yayarsu ta biyu dake bima yaya Gajeje dan ita acan take aure.

        Zaune suke a ƙarƙashin bishiyar tsakar gidan nasu sun baje kaya ita da Sa’a da Tinene. Inna na daga bakin murhu tana talgen tuwon dare. Dariyarsu suke sha cike da nishaɗi dajin daɗi.

     Sa’a ce kawai ta amsa sallamar Zinneerah tare da mata sannu. Ta amsa a ɗarare tana duban Karima data haɗe girar sama data ƙasa. “Yaya Karima ashe kin dawo, sannu da zuwa, yaya kika baro su Yaya Atinen?”.

        “To uwar iya, halan kin aikenine da kike lissaho mani wannan tambayoyin? Kai wagga ɗiya hi’ilinki yayi yawa wallahi, k…….”

        “Haba Yaya Karima, minene laihinta anan kuma? Danta maki barka da dawowa da tambayar su Yaya Atine?”. Sa’a ta faɗa cikin katse ƴar uwar tata rai ɓace.

     A fusace itama karimar ta katseta da fadin, “To kema waya saki a ciki, ALLAH ina ci maki uwa yanzun nan Sa’a. Ita ɗin uwarki ce ko mi?”.

       “Ba uwata bace, amma ƴar uwatace kamar yanda take ƴar uwarku kema. Daga hiɗin gaskiya sai laihi. Ni banga abinda Zinni ta tarema wani a gidan nanba da kuke tsangwama mata, itama fa ɗiyace kamar yanda muke ɗiyan gidan. Duk da baba baya magana akan abinda ake mata na tabbatar yanajin ciwo a rans……..”

          Timmm!! Kake jin saukar dundu a bayan Sa’a. Ta gyantsare saboda azabar zafi tana sosawa. Inna dake tsaye a kanta tana huci tace, “Kaɗanma nai miki dan ubanki. Wa kike hiɗima waɗanan maganar banzar to? Sheɗaniya munahika. Anya kuwa nice uwarki Sa’a? Kodai kema Hauwar ce ta haiheki taimin mucanje ban saniba?”.

         Baki cike da iska Sa’a tace, “Amma inna dan na hiɗi gaskiya sai kimin wannan uban ƙullin a baya?”.

       “Kaɗanma nai miki shegiya ƴal bura’uba bai baki kamar na reza, hita kibar gidan nan kona sauya miki wannan shegiyar huskar da maruka”.

      Fita Sa’a tai tana ƙunƙuni da cigaba da shafa bayanta inda yasha dundun.

     Sum-sum Zinneerah ta wuce ɗakin Inna zata kai botikin tallar tata Karima ta daka mata tsawa. “Munahika dawo a lissahwa sannan”.

       Dawowa Zinneerah tayi jikinta na rawa ta  mikama Karima kuɗin da botikin. Fisgar botikin Tinene tayi, Karima kuma kuɗin ta ƙwata tana buge mata hannu.

      “Innarmu na nawa kika aza mata?”.

    Karima ta faɗa tana fara irga kuɗin.

           Daga inda Inna take ta bata amsa da, “Na jikka sha huɗu ne cir gaba daya, dan na rantse da ALLAH kona hicika ya ɓata ina miki ɓatanci da shegen bugu a gidan nan. Kuma sai ubanki ya biyani kuɗina babu ɗagin ƙahwa”.

     Zinneerah dai batace komaiba. Sai su Tinene ne suka kwashe da dariya. Karima ta gama irga kuɗin tana jijjigasu da faɗin, “ALLAH ya sota Inna sun cika. Kuɗin anan jikka goma sha ɗaya da murtala uku, sai kayan daya rage na jikka uku ba murtala uku”.

      “Ta taimaki kanta. Ga tuwo can kije ki ci idan kina so, dan nasan dai abokan iskancinki sun gama cika maki ciki da shinkahwar tasha”.

      “To” kawai Zinneerah ta ce ta nufi hanyar ɗakinsu. Dan wani irin jiri takeji yana neman kwasarta. Tana shiga ɗakinsu ta zube a katifar su Tinene tana sauke numfashi. A hankali barci ya fara rinjayar idanunta mai daɗi. 

       “Baƙo na sallama da Zinneerah a waje”.

     Ta tsinkayo muryar yaro sama-sama da ga tsakar gida. Tsawar da inna ta dakama yaron ce ta sakata buɗe idanunta gaba ɗaya babu shiri. Sai kuma ta jiyo Sa’a na faɗin,

         “Inna bafa wani bane ba, malam badamasi ne malaminsu”.

     Tsaki Inna taja batare data tankaba. Yayinda Sa’a ta ɗaga labulen ɗakin tana kiran sunanta. “Zinni ki tashi ga Malam Bade yazo nemanki”.

      Yinƙurawa tai ta tashi zaune tana gyara hijjab ɗin jikinta. Cikin sanyinta dana barcin data fara tace, “To Yaya Sa’a”. Daga haka ta miƙe ta fiti cike da dauriya.

    

        Matashin saurayine, dan gaba ɗaya shekarun nasa bazasu wuce talatin da ɗoriya ba. Zinneerah data fito a ɗarare saboda tsoron Inna ta rissina tana murmushi. “Sannu da zuwa malam. Ina yini?”.

     Shima tashi fuskar faɗaɗe da murmushi ya amsa yana kallonta. “Zinneerah Sulaiman ashe kin dawo gida babu labari? Sai ɗazu ina bisa mashin na hangeki da botikin gyaɗa da riɗi a bakin yara”.

      Har yanzu tana a duƙe kai a ƙasa tana murmushi, cikin ƴar muryarta tace, “Na dawo Malam, dama naje wajen mamana ne gaisheta”.

       Yanzu kam da mamaki yake dubanta. Cikin kasa haɗiye abinda ke a ransa yace, “Amma a gari aketa hiɗin guduwa kikai bama asan ina kika nuhwaba? Kai mutane sai dai a barsu da halinsu. ALLAH ya ƙyauta to, kin baro maman naki lahiya ko?”.

       “Lahiya lau suke Malam”.

“To Alhmdllh, Yanzu ni bama wannan ba, nazone dama akan jarabawarku ta jsce. Ina hwata dai baki manta nanda kwanaki takwas zaku hwara ba ko?”.

      Karan farko ta ɗago taɗan kallesa ta sake maida kanta ƙasa. Kafin tace wani abu Inna ta banko ƙyauran langa-langar ƙofar gidan nasu ta fito.

            “Uhyimm! Kaji farkar taka ta dawo kazo kenan? To billahillazi bari kaji yanzu bazan ɗauki wannan sheɗancinba. Kaji da ƙyau karna sake ganinka ƙohwar gidan nan. Idan son ganinta kake ta bika can mahaɗar taku man……”

      “K dalla malama saurara, tsohuwar banza da bakinta bai hiɗin alkairi sai sheri wa ɗiyan mutane. Na rantse da ALLAH kika ƙara hiɗin wani kalmar ɓatanci garemu yau sai kin kwana ofishin ƴan sanda. Ni nazo ne akan maganar jarabawa da zasu yi ta koma makaranta….”

        “Anƙi ta koma ɗin munahiki algungumi. Dama can niya nai na barta take zuwa. da ga yau da ga yanzu kuma na hwasa. Bata sake zuwa talla zataimani”.

      “Ashe kuwa zaki gurfana gaban mai-gari……”

       “Kaini gaban sarkin katsina ma ƙarewar mai-gari mana. Ke kuma munahika dan ubanki tashi ki shige ciki, ƴal bura’uban yarinya kulin bata iya komaiba sai janyoma mutane jidali da yaye-yaye a ƙwar gida. Zanyi maganin rawar kanki ne ai…”

       Yanda ta kaima Zinneerah duka ya sata miƙewa da gudu ta shige gidan. Shima Malam Badamasi bai sake tanka mataba ya bar ƙofar gidan rai ɓace. Inna kuwa masifa ta cigaba da zazzagawa har sai da Sa’a da Karima suka fito suka shiga da ita gida.

     Tana shiga ta hau dukan Zinneerah babu ji babu gani. Sai da tai mata lilis ta barta kwance tana numfashi da ƙyar. Zinneerah akwai taurin zuciyar tsiya da kafiya wani lokacin. Duk wahalar da take sha wajen Inna akan jima ba’aga kukanta ba idan ba ita taso ba. Idan kuwa kaga ta cika yawan kuka to lallai abin ya kai babba gareta sosai.

      Inna na tsaka da cigaba da jarabarta aka buga sallama. Sa’a ce ta amsa tare da nufar zauren gidan nasu dan taga wanene. (Sanƙira) mai shela idan abu ya faru a garinne tsaye yana baza babbar riga. Ta rissina tana gaidashi dan dattijo ne sosai, amma Baba zai iya girmarsa. 

     “Tsohuwar taki na nan ko?”.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button