Uncategorized

MAKAUNIYAR KADDARA 4

“Eh baba tana nan”.

“To maza sanar mata mai-gari na biɗar ganinta. inko bata zuwa cikin salama ƴan doka zasuzo su kaita da kansu. Tazo tare da ƴar uwarki zinneerah”.

      Sosai gaban Sa’a ya faɗi, amma ta daure cikin girmamawa ta amsa masa tare da juyawa cikin gidan. 

       Inna ta dubi Sa’a cikin haushin Zinneerah da bai gama sakintaba tace, “Ke kuma minene kika shigo ma mutane haka? Halan shegen nanne bai tahi ba?”.

     Kan Sa’a a ƙasa tace, “A’a Inna. Baba Lado sanƙira ne fa, wai ana kiranki gidan mai-gari ke da Zinni….”

       “Ki koma ki hiɗi masa ba’a zuwa. Ba’a kamar ana zuwa ɗin…”

    “Inna wlhy cayay fa idan baki zuwa ƴan sanda zasuzo su tahi da ke”.

       Shiru Innar tayi ƙirjinta na bugawa. Ta tsani harkar ƴan sanda, dan tun sanda sukai faɗa da Lamunde aka adashi ta kaita kusada ofishin ƴan sanda akazo har gida aka kamata sai da tai kwana biyu a kusada hannunsu take shakkarsu. Ba ƙaramin wuya taciyo a kwana biyun datai wajensu ba. Amma a fili sai ta ƙyaɓe baki zata fara masifa kuma…….

       “Shin wai Asabe saƙon mai-gari bai iso gareki bane?”.

    Karaɗin Sanƙira daga ƙofar gida ya katse mata masifar datai nufin farawa. A tsorace Karima tace, “Innarmu dan ALLAH kije, tunda kinga harda ita akace kuje. Kinsanfa mai-garin nan ba mutuncine da shi ba wlhy yana iya kira maki ƴan dokar”.

      Kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Ta kai dubanta ga Zinneerah dake kwance barci ya fara ɗaukarta. Tsawa ta daka mata wadda ta sakata tashi a firgice babu shiri.

      Ran Inna fal masifa ta tasa Zinneerah gaba Sanƙira na biye dasu suka tafi gidan mai-gari. Acan suka iske malam badamasi. Tun daga nesa Inna ta dinga antaya masa uwar harara kai kace idonta zasu zubo ƙasa ne. Shiko baima san tanaiba. Dan hankalinsa dana mai-garin da fadawa duk yana kan Zinneerah ne dake ɗingishi.

       “Ranka ya daɗe ka ga abinda nake hidi maka ko! Da alama bayan barowata gidan bugunta tai”.

      Ran mai-gari a ɓace ya wurgawa Inna mugun kallo. “Ke dai Asabe baki gamawa da duniya lahiya inhar baki canja halinki. Ace mutum shi dai baisan komaiba sai mugunta, ke shikenan zicciyarki tamkar ta kahiran hwarkon ƙarni! Kai ALLAH ya wadaran halinki wlhy Asabe. shi dai malam Sule bai sa’ar mace irinki ba. Ya auri ta arziƙin kin koreta a gidan kina kuma gallazama abunda ta haihwa. Wlhy ina mai tabbatar maki wata rana sai kinyi nadama, dan wanga ɗiya sai ta zame miki ɗan hakkin faka raina, RAINA KAMA kuma mara mutuncin mata”.

        Kan Inna a ƙasa tanata faman kumurya da kumatu babu damar magana, sai da mai-gari ya ƙare mata zagi tas da gorin asalinta kafin ya ɗora da gargaɗi.

      “To naji kince baki sake barin yarinyar nan taje makaranta. Kece kika sata ne?”.

     Kan Inna a ƙasa har yanzu tace, “ALLAH shi sawwaƙa ranka ya daɗe. Niko miya ja mani kai ɗiyana boko. Ubana bai saniba bani kai ɗiyana su tabaɗe. Can abokan cin mushenta ne suka kaita……”

        “E, ai shi abokin cin mushen nata da kike magana shine kika asirce ya koma kan ɗiyanki, kinga ashe kema abikiyar cin mushen tashi ce ko?”.

     Malam badamasi ya faɗa a harzuƙe cikin katse Inna. Babu wanda ya dakatar da shi, dan kowa yasan Babawo take nufi, tunda shine yay tsaye tsayin daka har Zinneerah ta shiga makaranta saboda tana so. Amma yaran gidansu daga firamari basa cigaba. Sa’a ce ma taɗan fara sakandire ɗin itama zango ɗaya tayi ta gudo saboda wani malami ya daketa Inna taje tai masa tijara tace Sa’ar bata sake zuwa. Daga nan kuma bata sake zuwan ba.

       Mai-gari ya cigaba da faɗin, “To bara na gaya miki a gaban kowa ki riƙe a ranki yarinyarnan zata cigaba da karatunta har sai ta gama. Ni nan mai-gari zan ɗauki nauyin ɗawainiyar karatun natama daga yau, tunda ance dama yaron daya kaita ya janye dama daga yi saboda sherin da kikayo ta ƙarƙashin ƙasa. Wlhy kinji na rantse, dai-dai da rana ɗaya yarinyarnan kika hanata zuwa makaranta sai kin kwana a kusada ofishin ƴan sanda. Kowa dake nan ya shaida”.

       A take duk suka amsa masa da cewar sun shaida. Banda Inna dakeji tamkar zata haɗiye zuciyarta ta mace. Zinneerah kam a ranta wani irin daɗi ne ya lulluɓeta. 

        Sai da mai-gari ya ƙarama Inna dogon gargaɗi sannan ya sallameta banda Zinneerah.  

      Bayan wucewar Inna Mai-gari ya shiga yima Zinneerah tambayoyi tana bashi amsa kanta a ƙasa. Sosai tausayinta ya sake mamayesu, suka shiga mata nasiha akan muhimmancin haƙuri da ribar da mai yinsa kanci a duniya ko a lahira. Sannan ya damƙa amanarta hannun malam Badamasi. Tare da tabbatar masa duk abinda za’a buƙata na ɓangaren makaranta na Zinneerah yazo gunsa ya amsa. Daga haka aka sallamesu bayan mai garin ya bata ƙyauta jikka biyu da rabi (500).

       Godiya tai musu sosai cike da girmamawa itama, tare da addu’oin fatan alkairi sannan suka taso ita da malam badamasi daya rakota har gida yana ƙara mata nasiha.

      Koda Zinneerah ta dawo gida tayi tunanin inna zata hukuntata akan abinda ya faru a gidan mai-gari. Amma sai taji shiru batace da ita ƙala ba. sai dai tana ɗaure mata fuska fiye da yanda ta saba. Sannan komai ƙanƙantar aiki ita ake kira tayi koda su Sa’a na zaune a kusa da ita.

★★”★★”★★”★★

           Akwana a tashi babu wahala wajen UBANGIJI, haka rayuwa ta cigaba da shuɗawa. Yau fari gobe tsumma a gidan su Zinneerah. Ita dai batasan minene farin ciki ba ko jin daɗi a gidansu. 

       Tun randa sukaje gidan mai-gari da inna sai ta sake ninka gallazawar da take mata fiye da da. Makaranta dai ta barta tana cigaba da zuwa. Amma kafin ta wuce ƙa’ida saita kammala ayyukanta. Idan kuma ta dawo ta iske wasu na jiranta him. Ga tallar riɗi da gyaɗa babu fashi gareta. Tsangwama wajen Karima da Tinene sai abinda yay gaba. Idan kaga taji daɗi sai wajen Sa’a da Yaya Gajeje idan tazo gidan. Shi dama Baba ba’a sakashi a lissafi. Dan tamkar bashi da wanima amfani a gidan. Idanma baiso ba sai ya yini a gona tun safe sai yamma zai dawo. Duk abinda Inna zatai a gidan ƙala bai iya cewa saboda tsoron da yake mata.

       A haka su Zinneerah suka fara jarabawar junior waec ɗinsu. Zinneerah ba wani ƙoƙari ne da ita sosai ba. Sai dai tanada naci akan abu sosai. Duk abinda takeso takan dage a kansa domin ganin ta cimma nasara. Hakan yasa sam bata da wasa, musamman ma daya kasance itaɗin miskilace ta gaske. Ga halin gidansu ya sake maidata shiru-shiru da rashin son sakewa da mutane.

     Zuwa yanzu ta daina jin ciwon cikin nan da kasala. Sai wani irin ƙiba take mai ban mamaki da haske. Ɗan matashin ƙirjinta na ƙara fitowa fili sosai fiye da da. 

      Kowa ya ganta sai ya tanka canjawar tata na ƙanƙanin lokaci, dan abun na bama mutane mamaki sosai. Musamman da aka san bawani daɗi takeji a gidan nasu ba. Ita kanta Innar bata gajiya da kallon Zinneerah ɗin a ƴan kwanakin nan. Sai dai tanayi tana jan tsaki da ƙyaɓe fuska.

            A yau ma data kasance juma’a bayan tasowarta makaranta gida tayo. dan jarabawa ɗaya kacal sukayi, wadda daga ita sai ta ƙarshe da zasu zana. Cike ta iske gidan nasu da ƴan kawo lefen yaya Karima, wanda aka kawo da ga gidan su Babawonta. akwatina uku zuƙa-zuƙa ƴan yayine. Itace kuma budurwar farko da akaima akwati uku a garin, dan ɗaya sukeyi kacal su haɗa rio irin na saka kayan yara ɗin nan babba. Wasuma basayin Rio ɗin. Amma sai ga Babawo shi yayi har uku, ga kaya fal.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button