MAKAUNIYAR KADDARA 4

Sosai hankalin Zinneerah ya tashi, dan zuwa yanzu dai ta tabbatar Babawo kam ya barta har abada. Sum-sum ta lallaɓa ta shige ɗakinsu tunda babu wanda ya ganta hankalinsu nakan ganin kayan. Hijjab kawai ta cire ta zauna tana haɗiyar zuciya da ƙoƙarin ganin hawayenta basu zuba ba. Tsawon lokaci tana zaune hayaniyar mata da yara na daɗa ƙaruwa harda guɗe-guɗe. Ganin abin nasu bana ƙare bane ta zame ta kwanta hawayen da taketa ƙoƙarin dannewa suka shiga silalowa a kumatunta. Daga haka ta lula duniyar tunani mai zurfi har barci yay gaba da ita bata farga ba.
Timmmm!!!
Kakejin ƙarar saukar dundu. A firgice Zinneerah ta farka tana sosa gadon bayanta inda Karima ta daketa.
“Munahika ƴar buƙulu. Ashe nan kikazo kika ɓuya kina baƙin ciki da abun hwarin cikin daya sameni ko? To bara ki ji sai dai ki mutu wlhy. Ni Karima kamar na zama matar Babawo na gama. Dan nan da sati biyu za’a ɗaura mana aure ma”. Ta ƙare maganar da ƙyalƙyalewa da dariyar rashin mutunci.
Ita dai Zinneerah ko ɗaga kai ta kalleta batayiba. Ta kuma ƙi yarda tai kuka. Dan dama wani lokacin haka take da shegen taurin zuciya. Musamman akan abinda ta tabbatar da natane akai mata fin ƙarfi. Haka Karima ta cigaba da mata tujara har sai da Yaya Gajeje da bata tafi ba ta shigo tana zaginta sannan tabar Zinneerah.
Karan farko da baba ya nuna tsananin ɓacin ransa akan abinda akema Zinneerah har takaisa da yima Karima faɗa. Dan duk abinda tayi ya farune a kunnensa kasancewar ya shigo gidan.
Babu wanda ya iya magana har Inna. Dan ita kanta yau sai taji wani shakkar Baban a cikin ranta. Dama ance mai haƙuri bai iya faɗa ba.
Ɗan Murmushi Zinneerah dake a ɗaki zaune har yanzu tayi. A ranta kuwa tana mai tsananin jin tausayin mahaifin nasu da ta tabbatar anfi ƙarfinsa ne dama game da al’amarin gidan nasa, bawai dan Inna ta gagaresa bane ba.
★★★
Tun daga wannan rana su Inna suka hau shirin biki. Dama can a shirye suke tsaf dan sun daɗe suna jiran wannan ranar dan dai kawai Babawon nata musu yawo da hankaline kamar ma zai suɓuce. Sai kuma gashi cikin lokaci ƙanƙani hankalin nasa ya sake dawowa ga Karimar a bazata………….✍
*_ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL sunzo da sabon salon da duk ya zarta na baya_*
Dan haka masoya karku bari ayi tafiyar bana babu ku a ciki????????????????.
*_★ AL-ƘIBLA_*????
_Na Safiyya Huguma_
*_★ MABUƊIN ZUCIYA_*????
_Hafsat Rano_
*_★ DALAAL_*????
_Na Miss xoxo_
*_★ UBAYD MALEEK_*????
_Na Mamu gee_
*_★ MAKAUNIYAR ƘADDARA_*????
_Na Bilyn Abdull_
Lalai daga ji babu tambaya bana ma ZAFAFAN ku da turirinsu suke tafe. Dan dagani kasan za’a ragargaza cakwakiya, soyayya. Tare da nishaɗi????????????????????????????????.
Gasu duka akan farashi mai rahusar gaske.
Kamar haka????????????????
Ɗaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huɗu____500
Biyar_____700
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki????????
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)????????
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU????????
0903 234 5899
????????????????????????????????????????
TEAM—-ZAFAFA BIYAR????????????????