MAKAUNIYAR KADDARA 42

Mommy”.

         “Ai ya isa kam agaji Babana. jeka huta kaji”.

     “Thanks you Mommy ”. AK ya faɗa yana murmushi da nufar ƙofa. Kamar an tsikari Little dake wasa jikin Huzaifa sai cayay “Abbah zanje”. Danshi kowa Abba 

ne a wajensa indai namijine babba.

    Cak AK ya tsaya tare da juyowa yana kallonsa. shiko da gudu ya sauka a jikin Huzaifa ya nufesa. Babu musu ya  kama hannunsa suka fice. 

       Da kallo duk suka bisu cike da sha’awa, a ransu sunajin tausayin yaron da baijiba bai ganiba, amma yaya zasuyi da ƙaddara kowa da irin tasa. ALLAH ya 

rubuta cewar ta hanyar daya samar da yaron yaso azurtashi da shi, ya kuma fisu sanin dalilin yin hakan, fatansu kawai ALLAH ya rayashi ya albarkaci 

rayuwarsa data ƙannensa masu zuwa.

        Huzaifa ne ya sake sauke numfashi, hakan yasa su Baffah dawo da kallonsu gareshi, cikin jinjina kai yace, “Ku daina zargin AK ya samar da yaron nan 

ta hanyar banza. Akwai wani voice recording dana taɓaji a wayar Adilah batare da itama tasan wayar ta naɗa ba, sai dai bai isa zama hujjaba sai nayi 

bincike”.

      Da sauri Mommy tace, “Voice recording kuma akanmi?”.

    “Kuyi haƙuri na bincika ɗin zaku sani, kudai ku tayani da addu’a ku kuma bani lokaci”.

       Cikin jinjina kai Baffah yace, “Mun baka ɗan albarka. ALLAH yayi jagora muji alkairi”.

     Da amin Huzaifa ya amsa yana miƙewa. dan shima so yake yaje ya kwanta ya huta.

________________________★

        *_LONDON_*

   Ganin yanda Hajiya iya ke murna ya saka Khalipha samun waje ya zauna danta gama ta gumtsa masa. Tana kuwa ajiye wayar ta ɗaga hannu sama tana ambaton 

Alhmdllh. 

    Katseta yayi da faɗin, “Niko Granny taƙaita addu’ar nan ki faɗamin minene?”.

     Hannu ta sauke tana masa daƙuwa. Sai kuma ta ƙara washe baki da gyara zama. “Burina ne ya cika Abdul-Mutallab ƙarami, ALLAH ya tabbatar da tarkon dana 

ɗana. Na kuma daɗe ina mafarki da addu’a. Bazan ɓoye makaba yau dama saboda Moddibo nasa aka bani Zinneerah. Dan nasan duk daren daɗewa zaizo ya ganta, ko 

yasota ko karya sota dama na tanadar masa itane. Sai kuma cikin hukuncin ALLAH ga wani sarƙi ya ɓilla a tsakani…….. (tsaf ta kwashe masa labari ta 

bashi). 

        Zuciyarsa ce ta shiga tsitstsinkewa, yay saurin yin ƙoƙarin dai-daita yanayin nasa yana haɗiye abinda ke neman toshe fitar numfashinsa. Cikin 

murmushi da ƴar dariyar yaƙe yace, “Kai kai kai Alhmdllh da wannan daddaɗar labari Granny. Wlhy wannan haɗi yayi kuwa, dan sun dace matuƙa, sannan hakan da 

baffa yayi shine maganin Aunty Farah da Mammah. Sai dai kuma abinda ya bani mamaki da al’ajabi wai little jinin Yayanmu ne. kainafa ya kulle”.

       “Nima nawan a kulle yake Khalipha, amma dai ni yanzu burina jin ta bakin Inno, tunda dai ai ba’a shan ciki a ruwa ko? Sannan kuma babu ta wata hanyar 

da mace zata samu ciki sai da namiji, dan haka dan ubansu zasuma faɗi yanda akayine su dukansu”.

        Ɗan jimm Khalipha yay yana wani nazari saboda maganar hajiya iya, yace, “Eh hakane Granny, amma dai yanzu akwai wasu hanyoyin da mace kan iya samun 

ciki koda babu alaƙar namiji a tsakaninsu”.

     Cikin sauri hajiya iya tace, “Kai Khalipha kaji tsoron ALLAH ta wace hanyace kuwa? Ni dai ban taɓa jiba gaskiya”.

     Murmushi Khalipha yayi, cike da rashin damuwa ko tunaninsa kaiwa nan ɗin da wata manufa yace, “Granny karki manta nifa Doctor ne. Doctor ɗinma dakeda 

alaƙa da matsaloli irin na mata. Akwai hanyoyi da dama kamar su yin dashen ciki da makamantansu”.

       “Kamarya dashen ciki?”.

Dariya yayi yana miƙewa. “Oh oh Granny wannan ai bayanine mai zaman kansa. Amma dai ki sani yanzu ana iya dasama mace ciki ta haihu wlhy”.

       Baki hajiya iya ta taɓe da faɗin, “Ah kudai da shegen ƙaƙale-ƙaƙalenku na likitoci dalilin yin karatu cikin masu jajayen kunnuwa ba. Mudai ko anayin 

wannan sheɗancin baije manaba kaji, danni wannan ai badan karna yanke hukunciba sai nace kamar wuce wuri ne”.

          “Tab Granny wlhy mutanenmu ma sunayi, duk da dai gaskiya turawa sukafiyi, amma yanzu kinga kamar a kudancin ƙasarmu sosai sukeyi, wasuma sana’a 

suka maidashi wlhy. A dasa musu cikin idan lokacin haihuwarsa yayi su haifa suba masu cikin ɗansu. ALLAH dai ya ƙyauta, dan wasu tsiraru a mutanenmu ma sun 

tsunduma wannan harkar sosai musamman ƴan gayun mata da basa son wahala, sai su bada a ɗaukar musu cikin idan ya isa haihuwa a haifa a basu abinsu. Wasuma a 

asibitin ake ajiye musu ba jikin kowaba. Idan ya isa haihuwa a ciresa a basu”.

       “Kai wannan masifa dami tai kama. A lallai wannan duniya tazo ƙarahe kuwa”.

     “Sosai ma” Khalipha ya faɗa yana ƙoƙarin ficewa dan bayaso halin da yake ciki yakai ga bayyana a fuskarsa har Hajiya iya ta fahimta.

      A falo ya wuce su Zinneerah dake kallo, yanda ya wuce ko kallonsu baiyiba yasa Jamal cewa, “Tofa, inaga Granny da Yah Khalipha anɗan dambacebe naga 

kamar ya wuce a fusace”.

       Dariya su Meenal sukayi. Zinneerah ko tayi kamar bata jiba dan tun ɗazun gabanta ke wani irin faduwa. zuciyarya na mata rauni kamar maijin tsoron 

faruwar wani abu a gareta. Sai dai ta daure bata sanarma kowaba tanata addu’a a zuciyarta. Dan kallonma yinsa kawai take ba fahimta takeba sam.

       Duk wannn abu dake faruwa Farah na ɗakinta cike da damuwa. Dan tunda taji AK ya tafi Nigeria zuciyarya bata samu nutsuwaba. Wannan dalilin ya sata 

kiran Aunty Zakiyya ta sanar mata, ta kuma turama Mammah text message. Aunty Zakiyya ce ta kira Mammah suka tattauna, duk da ba’a kano takeba Mammah ta bata 

damar sakawa a mata binciken zancen yaron.

      Daga haka ta kira baffa a gadarance tana tabbatar masa bai isa rabata da AK ba. Idan ma wani abu yake ƙullawa sunyi ta banza, dan ko aure suka saka AK 

yayi har aka samu wannan yaron ya tabbatar sai AK ya saki koma ƴar uban wacece. taji zafin maganganun da Baffah ya yaɓa mata, dan haka ta yanke shawarar 

Aunty Zakiyya na gama mata bincike zata tafi Nigeria ɗin da kanta, shiyyasa ta kira Farah ta kwantar mata da hankali da mata nasiha akan karta sake shiga 

harkar kowa a gidan harsu gama bincikensu.

     To wannan nasiha ta Mammah tasa Aunty Farah nutsuwa waje guda ita a dole ta kama kanta.????. Suma dai su Hajiya iya daba sanin miya faru sukaiba babu 

wanda ya shiga harkar tata. Dan yanda bata nema ganin kowaba tun bayan tafiyar mijinta, suma sai basu nemetaba. Dan a matsayinta na matar gida ita keda 

haƙƙin bin yanda suka tashi ko sukaci suka sha a gidan. Amma bata taba yiba tayaya suma zasu takura kansu ne akan damuwa da al’amarinta. Gara su rike 

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button