MAKAUNIYAR KADDARA 43

page 43*
………..A Nigeria kuwa yau cikin farin ciki AK yay barci rungume da Little, haka kawai wata nutsuwa da farin ciki suka mamayesa. Dukan wani ƙunci da
damuwa da tunani akan samuwarsa suka kwaranye, farin ciki da nutsuwa suka maye gurbinsa, jiyake tamkar ya haɗiye abinsa ya ƙara haifosa tsabar yanda yakejin
abun kamar almara. wai shine da ɗa da rana tsaka, ɗan da baisan ta yanda ya samar da shi ba, ɗan da baisan a ina ya samar dashi ba. Shi tsabar ma nazari
akan waɗanan tambayoyi. har ji yake ƙwalwar kansa na kuɗa, shiyyasa ya tattare komai ya ajiye gefe ya rungumi ɗansa tare da sumbatar goshinsa yana murmushi.
Ya jima barci bai ɗaukesaba yanata kallon little ɗin, sai can kusan ɗaya na dare barci yay awan gaba da shi. ALLAH ya soshi yaron baida fitina. Dan
bai farkaba sai gabannin asuba ya tashi yana kiran “Mama ruwa, mama ruwa”.
A hankali AK ya buɗe idanunsa, ya miƙa hannu ta bayansa ya kunna fitila dake a bedside drawer dan da alama basu da wuta. Zaune ya tashi da ƙyau yana
riƙo little dake neman yin kuka yana kiran ruwa. “Oh oh sweetheart i’m sorry ina zuwa”. Ya faɗa da ɗagashi gaba ɗayansa ya maida jikinsa. Kafin ya ɗakko
ruwan daya ajiye gefensu dan shima yakan tashi shan ruwan dare shiyyasa baya kwanciya babu shi a kusa. Sosai little yasha ruwan. Yana gamawa ya lafe a
jikinsa ya koma barci. Shiru yay yana kallon fuskar yaron mai tsananin kama da tashi, wani lallausan murmushi da ajiyar zuciya suka kufce masa a lokaci
ɗaya. Kwantar dashi yay a hankali yaja bargo ya rufa masa shi kuma ya sauka dan yasan bazai iya sake komawa barcinba kuma.
Harya fita sallar asuba ya dawo little nata barcinsa, shima sake kwanciyar yayi dan barcin yake buƙata.
Kusan takwas na safe ya farka dole saboda tsalle-tsallen da little ya farka yana masa a jiki, dole ya buɗe idanunsa da sukai nauyi irin na wanda ya
tashi a barci. Kamo hanunsa yay ya zaunar a jikinsa yana murmushi tare da kai hannu ya shafi fuskarsa. “Little Handsome ka hanani barci bayan kai kasha
naka”.
Cikin rashin damuwa little yace, “Abba tea”. Dariya AK ya ƙyarƙyale da shi yana miƙewa zaune dashi a jikinsa. “Wato kai yaren abinda kakeso kawai kake
ganewa ko? Inga bakin shan tea ɗin?”.
Babu musu little ya ko wage masa baki alamar gashi. Dariya nanma ya sakeyi da sumbatar goshin yaron wani farin ciki na saukar masa. Huzaifa dake tsaye
a ƙofar ɗaki yana kallonsu yay murmushi tare da jin daɗin ganin ɗan uwansa na walwala maiban mamaki, dan ba abu ƙarami bane a rayuwa ke saka AK ƙyalƙyala
dariya. Baiyi magabana ya juya abinsa. Shiko AK daba ganinsa yayiba little ya ɗauka zuwa toilet, da kansa yay masa wanka, ya naɗo abinsa a towel ya kawo
ɗaki ya ajiye a kan gado. Wayar Haneef ya kira yana tambayarsa sunzoma little ɗin da kaya ne?. Daga can Haneef ya amsa masa da eh bara ya kawo.
“Okay” ya amsa yana yanke wayar, game ya sakama little a waya ya nufi toilet ɗin shima yin wankan. Shigarsa babu jimawa sai ga Haneef, sai da yayi
sallama sau kusan uku, jin ba’a amsaba ya leƙo da kansa. Little kawai ya hango yana kokawa da waya, dan haka ya shigo yana dariya. “My Darling good morning
” ya faɗa yana kaiwa tsugunne gaban gadon. Little dayay busy abinsa ya ɗan ɗago ya dubesa ya sake maida kansa.
Yanda yayi ɗin sai ya bama Haneef dariya, ya fisge wayar yana faɗin, “Haba my man ni zakama jama aji danka samu phone?”.
Ɓata fuska little yay zaiyi kuka Haneef ya maida masa wayar yana dariya. Daga haka ya miƙe ya ɗakko man Yayansu daya hanga a kan mirror yazo ya yayema
little towel ɗin da yake a ciki ya hau shafa masa. Sunayi ana kokawa dan little baison ajiye wayar hannunsa. Har dai aka gama. Yana saka masa kaya AK ya
fito. Gaidashi Haneef yayi. Ya amsa shikam yana binsu da kallo, dan yanda suke kokawa wajen saka kayan kawai zai tabbatar maka akwai shaƙuwa a tsakaninsu
sosai.
Haneef na gama shirya little ya ɗaukesa suka fice danya bama Yayansu damar shiryawa. A hankali AK ya sauke numfashi, zama yay a bakin gadon yana ɗan
kai hannu ya murza goshinsa, hakan yayi dai-dai da shigowar kira a wayarsa.
Kamar zai share sai kuma ya ɗauka wayar dake a kife, duk da ganin Mammah da yayi ɓaro-ɓaro a jikin screen ɗin bai kawo komai a ransa ba ya ɗaga.
Sama-sama ta amsa masa sallanarsa, gaisuwa kuwama bata amsaba ta shiga masa magana cikin faɗa. “Yanzu Abdul-Mutallab danka maidani banza harka iya
ɗaukar ƙafa ka tafi Nigeria bakako sanar minba!!?”.
Idanunsa yaɗan lumshe da raunan muryarsa gareta kodan daraja ta uwa da ALLAH ya bata, cikin girgiza kai kamar yana a gabanta yace, “Am so sorry
Mammah, nima tafiyar ta dolece wlhy, ki gafarceni”.
“Dole kace ta dolece tunda ubanka ya gama gayamin magana jiya, aiko yayi da ƴar halak da bazata raga masaba. Dan insha ALLAH yau zan baro london nima
zuwa Nigeria ɗin, sai naga munafurcin da kuke son biznewa”.
Babu shiri AK ya miƙe yana faɗin “Mammah Nigeria kuma?”.
“Ƙwarai da gaske, ko karnazo ne ubana?!”.
Bakinsa ya cije dakai hannu ya dafe kansa, zaiyi magana ta yanke wayar ƙitt
Rasa abinyi AK yayi a ɗakin, ya shiga kai kawo kamar mai ɗawafi. Sam baiso Mammah tazo Nigeria a wannan gaɓar, dan yanda Baffah ya ɗauki zafi
wlhy ba raga mata zaiyiba. Shiko baya buƙatar ganin suna shiga irin wannan rikicin dan ƙara nisantasu yakeyi.
Wayar Mahma ya kira da sauri dan yasan itace kawai zata iya takama Mammah birki. Harta tsinke ba’a ɗagaba, dan haka ya sake kira. Jin an ɗauka ya
sauke ajiyar zuciya. Sai dai jin muryar Adilah na faɗin, “Sweet bro surprise”. Ya sakashi maida hannunsa a goshinsa yana murzawa. Ƙoƙarin dai-daita muryarsa
yayi yace, “Uhmyim Darling badai kina london ba?”.
Ɓata fuska tayi daga can kamar tana gabansa. Cikin shagwaɓa tace, “Uhm ai dama nasan yanzu ka daina sona ALLAH, yau kwana biyu ina nemanka a waya
saboda dawowana amma bana samunka, na dawo ɗazun nan, saina tarar wai kana 9ja, yanzu haka ina shirin tafiya can gidanka wajen Granny ne, ina jiran Khalipha
yace zaizo mutafi idan ya fito school”.
“Oh parrot har yanzu dai baki canjaba. Ina Mahma ne?”.
Baki ta tura duk da kuwa bata kasance ƙaramar yarinyaba, dan tama girmi Khalipha da kusan shekara biyu. Cikin shagwaɓa tace, “Haka dai kakeson parrot
ɗin nan taka. mahma gata can suna rikici da Mammah akan wai zatazo Nigeria ita da Farah. Wai mike faruwane na isketa sai faɗa faɗa, ni wlhy namaji dama ban
dawo ba. Shiyyasa zan tafiyata gidanka dan banason faɗan nan na Mammah taita zagin mana Baffahn mu”.