MAKAUNIYAR KADDARA 43

Hankalin AK ne ya kuma tashi, atake raunin da yake ɓoyema ƴar uwarsa ya bayyana. Idanunsa suka sake kaɗawa sukai jajur. “Adilah akwai matsalane, amma
yanzu sanin tushenta bashine abinyiba. Inason kije ki sace min passport ɗinta dana Farah ɗin duka”.
“Tab, wlhy Bro hakan dakamar wuya, dan inaga abinda Mahma tai niyyar yi kenan Mammah ɗin ta gani, yanzu hakama gata can harta fito da kayan tafiya
shine Mammah ta kulle ƙofan ta canja security”.
“Thanks GOD”. Ya faɗa yana furzar da zazzafar iska. Hakan da yayine ya sake tayarda hankalin Adilah, dan ta tabbatar Yayanta na cikin damuwa, tambaya
ta shiga masa amma bai iya bata amsa ko gudaba, sai ma yanke wayar yayi daga ƙarshe ya zame ya kwanta a gadon yana mai dafe kansa da yakejin ya fara sara
masa da ƙarfi.
A cikin gida kuwa little nacan yanata hidimarsa a tsakanin su Baffah hankali kwance. Dan tare yay karin kumallo da Baffah da Mommy abinsa. Hakan harya
dinga basu mamakin yanda ya saki jiki dasu sosai. Sai da suka kusa gamawa AK ya shigo falon. Gaidasu yayi sanan ya kai zaune kusa da Mommy. Ta shafa kansa
cikin kulawa take faɗin, “Kana lafiya kuwa Son?”.
Ɗan ɗagowa yay daga kwanciyar da yay jikin kujerar yay mata murmushin yaƙe. “Lafiya lau Momy gajiyan jiyace kawai”.
“Aiko ya kamata ta sakeka haka. Kodai Daddy nane bai barka kayi barciba?”. Tai maganar tana kallon little dake wasansa hankali kwance. Shima kallon
little ɗin yayi yaɗan ɗauke kansa da sakin guntun murmushi. “No Mommy, aishi wannan ko hidimarsa tasa idan ya kwanta bazai farkaba, kawai dai hajiyanne”.
“Ayya to sannu kaji, taso ka karya saika koma ka sake kwanciya ka huta”. Tai maganar tana faɗa haɗa masa abincin dake a tsakkiyar falon wanda basu
jima da gama ciba suma. Baffah dai najinsu amma bai tankaba, sai dai yaji a ransa babu wata gajiya dake damun AK ɗin akwai dai dalili. Dan yanayinsa baiyi
kama damai gajiyaba sai damuwa.
*_DANYA_*
Ba ƙaramin sake rikicewa Inna tai ba da ganin kayan goron ɗaurin aure wai duk na Zinneerah, yarinyar da aka cemata tana can ta kama ɗaki. Kai ina akwai
ƙarya a wannan al’amarin. Kawai dai ta fahimci Baba da wani sabon salo ya dawo danya. Kawai yayi hakane dan ace ƴarsa na cikin aminci. To itako zata
tabbatar masa ras take kallonsa.
Da wannan banzan tunanin nata yasa ta wartsake kamar babu abinda ya dameta. Sai ma ƙoƙari sakama kanta wata walwalar dole takeyi musamman idan ƴar
barka da gulma suka shigo, dan zuwa yanzu duk zancen ɗaurin auren Zinneerah ya shiga garin na Danya. Wasu kuma badan barkar suke zuwabama yanzu dan son gani
da idone da son tabbatarwa da abinda ke faruwa a gidan. Dawowar baba da sabuwar amarya harda tsohon ciki, auren Zinneerah da dawowar Karima gida.
Aiko dai suna ganin abinda sukazo neman, dan haka duk wacce zata fita saita gumtsi gulma ta fita dashi a baki, duk yanda Inna ke ƙoƙarin nuna ita ta
dake ranta kishinta da damuwarta sun kasa ɓoyuwa, sai zabga habaici take wasu Baba da gugar zana. Har takai Gwaggo Laritu na maida mata a kaikaice itama.
Sai da baba yaga abin zai zama fitina ya lallaɓa Gwaggo Laritu ta wuce gida aka bar Inna da takaici dan kukan zuci kawai take faman yi wanda yafi na
zahiri ciwo da cin rai.
___________________★
Koda AK ya kammala karyawa fita sukai shi da Huzaifa da little, dan yanason rage damuwar Mammah dake cin ransa suk da yaji daɗin abinda Mahma tayi.
Sai da suka fita ya samu damar yin waya da Hajiya Iya ta wayar Khalipha daketa ƙoƙarin danne damuwarsa.
Sun jima suna wayar da Hajiya iya harma da Huzaifa da little dataji daɗin gani tare dasu dan video call ne. A bakin Hajiya iyan ne ma yakejin wai
Farah ta fita da akwati a gidan tun ɗazun, kuma su basusan ina ta nufaba dan bataima kowa maganaba.
Murmushi AK yayi, cikin rashin damuwa yace, “Karki damu Granny gidan Mammah ta tafi, kuma Mahma zatai maganinta ne ta dawo da ƙafafunta”.
Baki Hajiya iya ta taɓe da faɗin, “Kai nifa yanzu kam taitayi dan bata cikin lissafina. Tunda ALLAH ya baka ƴar mutunci da nakeda tabbacin zata share
hawayenka in ALLAH ya yarda. Fatana dai ka riƙemin yarinya da ƙyau Moddibo, dan wlhy inhar Inno tai kuka akanka kaima sai kayi”.
Fiska ya ɓata yana wani ɗan yatsinata. Yace, “Oh kukuma naku salon kenan Granny?”.
“Ai mun wucema haka, dan wlhy bazan baka Inno ba saina shimfiɗa maka dokoki, ko ɗaya ka tsallaka kuwa saika haɗu da fushina”.
“To lallai naku babbane, nikam sai anjimanki”.
“Zakaci ubanka Kabirune yaro, bauɗaɗen banza jikan ƴan Morocco”.
“Ahaka dai kuka gani kuka nane”. Ya faɗa a hasale saboda zagar masa uba da tayi. Itako Hajiya iya dama tayine danta hasalashi ɗin dan haka ta hau
dariya. Huzaifa fa ma dai dariyar yakeyi. Hajiya iya tace, “Kaima ai ina zuwa kanka dan uwarka Balkisu, tuzurun banza kana neman tsofewa a gida babu aure.
Why bara dai na dawo ƴar kowa na samu aura maka zanyi a dangi, da wani shegen kansa uwa sheƙar angulu”.
A take shima ya shanye tasa dariyar yana ɓata fuska, “To kin kuma dawo kaina? Kefa ALLAH Granny kinada matsa kiyita zagema mutum iyaye babu laifin
zaune babu na tsaye. Sai ki nema wanda zaki samoma mata a ƙauye badai niba wlhy”.
“An zageka ɗin mai kama da zucbibin ƴan Lagos, bara dai na dawo kaga yanda zanyi maganinka wlhy, inba hakaba nasa Bashir ɗin yima uwarka kishiya itama
wlhy. (Daddynsa take nufi????) dan haka ya waro idanu waje da faɗin, “Kai! Wai ke Granny miyasa lamarin naki kullum gaba yakeyi?, sam bakison zaman lafiya?”.
“Oh bama kasan yana yin gaba ba saina dawo Nigeria”. Tai maganar tana yanke kiran.
“Tsohuwarnan akwai tarin matsaloli a kanta yasin”.
Cewar Huzaifa rai ɓace. Shi adole yaji haushi ance za’a saka aima Mommy kishiya????.
“Ai indai Granny ce ta wuce duk yanda kake tunaninta”. Cewar AK yana wani ɓata fuska shima. Little da baisan anaiba wasansa kawai yake zabgawa.
Biyawa sukai ta gidan Dr Mahmud suka ɗaukesa dan gona zasuje duba masu aikin shinkafa, daga na su leƙa company da ayanzu haka an fara zuba aikinsa
shima. Kasancewar sun tahoma Little da kayan ciye-ciye ko damuwa baiyiba, sai uban rashinji yake zubawa a gonar alamar yana cikin ƙoshin lafiya.
Huzaifa akwai son irin wannan wajajen, dan haka ya shiga cikin gonar sosai yana duba aikin da yaba ƙyawun da yayi. Da wannan damar AK da Dr Mahmud
suka tattauna akan abinda ya shafesu game da ginin company nin shinkafa da kuma aikin shinkafar, dan a shirinsa so yake ya koma london zuwa jibi idan ALLAH