MAKAUNIYAR KADDARA 47

masa tana ƙoƙarin haɗiye kukanta. Batare daya amsaba ya raɓata zai wuce 

da faɗin, “Idan baki shiga hankalinki da saka wannan janbakin ba saina 

tsinke waɗanan lips ɗin da haƙori mtsoww”.

        Duk yanda Zinneerah taso daurewa kasawa tai sai da ta bisa da 

kallo mamaki ƙarara akan fuskarta. Ganin bata biyosaba ya sakashi 

tsayawa cak. Da sauri ta nufesa saboda fahimtar dan ita ɗin ya dakata. 

Jerawa sukai a tare gwanin sha’awa, dan yanda yake tafiya babu garaje 

haka itama take tafiyar, amma kasancewar abinda ya faru tana tsoron sake 

laifi ya ƙara hanzarta tata tafiyar, sai suka samu daidaito dashi dan ya 

fita kuzari da tsaho.

      Shigarsu wajen ya sake bayyana ɓacin ransa a saman fuska ganin 

yanda mutane ke ɗan kallonsu jefi-jefi, a bazata kawai taji ya ruƙo 

hannunta cikin nasa mai taushi da ƙamshi tamkar nata ɗinma, dan zuwa 

yanzu ta fahimci jin daɗi ke kawo irin wannan baiwar ga fata bawai 

shafe-shafe ba. A kusan tare ita da shi suka lumshe idanu saboda jin 

sabon al’amarin dake saukar musu a gangar jiki da magudanar jini, ya 

sake damƙe hannun da ƙyau yana ƙoƙarin dai-daita kansa gudun kar ayi 

abin kunya.

    Zinneerah kam ai murus bakinta ya ƙara mutuwa sai sama da ƙasa da 

numfashinta keyi tana ƙoƙarin fisgosa da ƙyar. Haka tanaji tana gani ya 

shiga zagayawa dasu yana ɗaukar abubuwa da sakawa a basket ɗin da ɗaya a 

ma’aikatan wajen ke biye dasu da shi. Itama kuma sai yanda budurwar ke 

kwarkwasa da wani iyayi a gaban Yayan nasu ya bama Zinneerah haushi ta 

shiga hararta ta gefen ido tana faman yamutse fuska.

      AK bai fahimci halin da take ciki ba sai da sukazo wajen biyan 

kuɗi, har lokacin yana riƙe da hannunta tamkar ance za’a ƙwace. ATM ya 

ciro a aljihun wandon getzner shaddarsa ash zai miƙa budurwar data 

tayasu takai hannu zata amsa cike da yauƙi, caraf Zinneerah ta kawo 

hannu ta amsa daga hannunsa tana wani juya ido da sake miskile fuska.

    Yanda tai ɗin ya saka wata dake kusa dasu kwashewa da dariya ita da 

ƙawarta. A fili tace, “Wlhy yarinya kin birgeni, adana abinki kar ƴan 

shishshigi suyi miki wuff da shi”. 

     Sarai Zinneerah ta jita, amma sai ko kallon inda suke bataiba tama 

ɗauke kai gefe. AK ma da sarai yajisu bai nuna yajiba, sai dai ya ɗan 

dubi Zinneerah ta gefen ido maganar ƴammatan na masa kaikawo a zuciya da 

ƙwaƙwalwa. 

     Koda aka gama saka musu a leda budurwar bata daddaraba duk da 

yarfatan da ƙawayenta sukayi da Zinneerah ta sake kai hannu zata ɗauka 

ledar Zinneerah ta rigata ɗauka da faɗin, “Don’t worry, thanks”.

     Kasa haƙuri AK yayi yanzu kam sai da ya ɗan dubeta, mi zuciyarsa ta 

ayyana masa oho sai gashi da sakin wani malalacin murmushi yana sake 

damƙe hannunta dake cikin nasa, daga haka ya jata suka fito yana mamakin 

miskilancinta da kame kai tamkar ba ƙaramar yarinya ba.

         Zinneerah na ganin sun fito ta fara ƙoƙarin zame hannunta a 

nasa, shima babu musu ya saki tare dayin gaba abinsa. Sai dai kuma 

abinda sukema gudun su Granny, kuma sun gani. Dan Granny dake bama Mommy 

labarin da Zinneerah ta bata akan zuwanta katsina aikatau tun bayan 

fitarsuce ta fara hangosu. Ta taɓa Mommy tana faɗin, “Auta kalla 

mutanenki”.

       Ɗago kan Mommy yayi dai-dai da sakin hannun juna da sukayi, dan 

haka ta murmushi kawai da faɗin, “Inna tarkon nan naki fa mai ƙarfine, 

dan na ƙaramin damƙa yayma ɗana ba, yana dai ƙoƙarin nuna halin nasa na 

basarwa ne”.

      Baki Hajiya ita ta taɓe da cewa, “Ai sai yayma ubanda baisan 

halinsaba. Ni tuni na harbosa ai. Itace dai na kasa gane kanta dan itama 

gidan miskilancince, bansan yanda gidan nasu zai kasanceba an tara masu 

shegen baƙin rai da miskilanci. Shiyyasa banason a faɗa mata har sai ta 

tare suje can su ƙarata”.

     Dariya Mommy ta sanya har su Zinneerah suka iso wajen, sai da suka 

shigo mota ta haɗiye abinta tana musu sannu. Duk amsawa sukai yana tada 

motar, daga haka sai gidan mmn sadiq da Zinneerah taita mamakin tayaya 

ya sani?.

    ★★

  Tarba suka samu maiban mamaki daga mmn sadiq da maman halima. ashe 

hajiya iya ta sanar musu da zuwan nasu, shiyyasa mmn sadiq datai niyyar 

zuwa dubata yau dole ta haƙura. Zinneerah kam ai tuni ta faɗa jikin mmn 

sadig tana murnar ganinta ita da mmn halima. hakan datai har sai da ya 

bama AK mamaki dan baiyi zatonta hakaba. Kasancewar Abba na gida yana 

jiransu a falonsa aka sauke AK, su Hajiya iya kuwa da mmn sadiq keji 

kamar ta goya suna a sashenta. 

        Duk yanda mmn sakina taso nuna halin nata garesu saita kasa. Dan 

wani cika mata ido sukai dole ta kama kanta harda zuwa ɗakin mmn sadiq 

gaishesu. Ai kam sun amsa mata da fara’a da mutuntawa, hakan da sukai 

kuma sai ya ƙara musu kima a idonta da shakka. Mmn halima ma cike da 

girmamawa tazo ta gaidasu, Hajiya iya nata sanya mata albarka dan bata 

manta da fuskartaba taje mata gaiauwar Inno.

        Saboda zuwa nan hajiya iya dama taƙi cin abinci, dan ta taho da 

shirin cin abincin gidan ɗiyar tata. Aiko taji daɗin samun masa da mmn 

sadiq tai musu, sai gashi daga ita har Mommy sunci sosai suna godiya. 

hakan yasa Mmn sadiq ƙara jin daɗi da nutsuwa. Dan koba komai ai sun 

bata kimarta. Zinneerah kam tuni tana sashen mmn halima ta barsu dan su 

sake da kuma kasancewarsu manya a gareta.

    Da wannan damar mmn sadiq da baƙinta sukai hirar zuminci da 

tattaunawa game da labarin da Zinneerah ta bama hajiya iya da kuma 

abinda ya faru akan zancen little da maganar ɗaurin aurenta. Harma da 

shirye-shiryen tariya da a take mommy ta tabatar musu ita ta gama shirya 

komai rana kawai suke jira insha ALLAHU.

    Hawaye sosai mmn sadiq keyi har sai da hajiya iya ta shiga 

lallashinta. 

     Sai da akai sallar la’asar Abba ya shigo gaida su hajiya iya tare 

da AK da shima yaci masa sosai dan yana sonta, ya kuma sha zoɓo shima. 

Sun gaisa cikin mutunta juna, suka ɗan ƙara tattaunawa har zuwa kusan 

biyar da rabi sannan sukai haramar tafiya.

    Sai kuma ga Zinneerah tai ƙwalkwal da idanu na kewar hajiya iya da 

zatayi duk da dai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu zata koma. Sau biyu suna 

haɗa ido da AK da tuni ya shige mota ta mirror ɗin waje, daga ƙarshe dai 

ta matsa daga saitinsa tana ɗaga musu hannu.

    Tafiyarsu da mintuna basufi talatinba su Sadiq suka dawo gida. Ganin 

Zinneerah suka haukace da murna suna tambayarya ina little ɗinsu?, su 

dai sunyi kewarsa dan ALLAH a dawo musu da abinsu. Dariya kawai take 

musu dan ita dai wannan ba huruminta baneba ai. Tunda batasan yaje canba 

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button