MAKAUNIYAR KADDARA 47

itama ganinsa tayi.
Bata samu zama da mahaifiyartaba sai dare bayan yaran sunyi barci,
kasancewar ɗakin mmn sadiq ɗin zata kwana suka sami damar yin hira,
yayinda mmn sadiq ketama ƴar tata nasiha a kaikaice akan aure da
muhimmancinsa da darajojinsa. Ita dai Zinneerah saurarenta kawai takeyi
bawai fahimtar dalilin yinsuba. Sai dai suna shiga kwakwalwarta tana
kuma ƙoƙarin adanawa da fatan yin aiki dasu a duk sanda ƙaddara ta
tilasta mata yin aure dan bata kawosa a lissafinta sam. ita kullum
lissafi da budget ɗinta akan karatune mai zurfi kawai.
Washe gari ma bayan tafiyar su Abdul skull sake zaman hira tayi da
mamanta. A yau ɗinma hirar ta kasance kusan duk nasiha da dabarun zaman
gidan aure koda da kishiya. Harma dai takai abin ya fara bama Zinneerah
mamaki amma saita danne a ranta kawai.
Karfe huɗu dai-dai sai ga Ni’ima da driver sunzo ɗaukarta, jitai
kamar ta fasa kuka. Amma jin mmn sadiq tace zasuje taron biki Danya kuma
harda ita nanda kwanaki tara yasa taɗanji daɗi a ranta har fuskarta ta
nuna. Bayan ta gama matse-matsen hawayenta ta shirya suka wuce ɗauke da
madaidaicin botikin gullisuwa da mmn sadiq ɗin tai musu.
Koda suka iso gidan cike da murna suka tari juna dasu Bahijja
daketa mata ƙorafin basusan zataje wajen mama ba da sun bita. dan sai da
su Mommy suka dawo suka sani. Haƙuri ta basu kawai, daga haka suka shiga
hidimar cin gwullisuwa kuma.
Ana idar da sallar magrib hajiya iya tai baƙuwa. Bayan sun
shiga ɗaki kusan awa ɗaya aka kira Zinneerah, kai tsaye hajiya iya tace
mata ta shirya zasu tafi da baƙuwar gidanta. Mamaki ya kama Zinneerah,
amma ganin yanda hajiya iya ta fiske dole itama ta shanye mamakin nata.
Bayan ta shirya Hajiya iya ta jata gefe tai mata ƴar nasiha da
gargaɗin duk abinda akai mata a inda zataje kartai jayayya, karkuma tai
wasa wajen koyon komai ɗin. Ta amsama hajiya iya da girmamawa ita dai
tana matsar ƙwalla, dan hankalinta ya tashi jin wai sati ɗaya zatai
acan, a hakanma hajiya fadi take waje ya ƙure ba haka tasoba.
Zinneerah naji na gani ta tafi tabar su Meenal tana hawaye suma
sunayi tamkar masu rabuwa har abada. Hajiya iya kanta sai da taji
kewarta, to amma wannan shine kawai gatan da zatai mata ta miƙata wajen
kwararrun mata ta fannin sanin gyaran jiki da wasu sirrika irin su
hajiya Falmata su gyara mata ƴar jikallen tata. Dan idan tai dubi da
abinda ya faru da kuma kishiya irin Farah saita ƙara jin wannan shine
gatan.
Koda suka iso gidan hajiya falmata bata tsaya sanyaba saboda
gargaɗi da sharuɗɗan hajiya iya akan irin salon gyaran da take buƙata
aima Zinneerah ɗin, itako hajiya falmata dama aikinta kawai ta sani
batasan wasaba. Musamman ma aiki irin wannan na manyan mutane kamar su
hajiya iya da suke alaƙa tun zamanin ƙuruciya ba abinda zatai sanya
bane. Dan haka tun a ranar ta fara gyara Zinneerah daga isowarsu gidan
ko hutawa batama bari sunyi zaman yiba. Tun Zinneerah na kallon abin
wani iri hardai ta fara jin yana shiga jikinta da sha’awarsa ganin yanda
ta fara canjawa da ƙamshi mai kama jiki da gogewar fata a cikin kwana
biyu.
Babu abinda ke damunta sai kewarsu Jamal da hajiya iya dan ko
abinci da ake bata na musamman ne. Hajiya Falmata kuwa nata aikinta da
koya mata abubuwa kai tsaye har kunya na neman kashe Zinneerah da ganin
hajiya falmata zata iskantar da ita shekarunta basu kai ba. A ranta kuma
tana mamaki yanda ake mata magana mai kama da harshen damo akan aure da
zamantakewarsa. Ta rasa wannan dalili itakam, takumayi alwashin bazata
tambayaba zata cigaba dabi da ido da kuma saurare.
A Ɓangaren su Hajiya iya kuwa Zinneerah na barin gidan aka ware
fara tsare-tsaren biki da maganar invitations dan hajiya iya da Baffah
fa shiri suke gagarumi kodan ƙular dasu Mammah dake can hotel suna jiran
tsammani daga mai bincike, AK kuwa daketa ƙoƙari akan aikin shinkafarsa
yana sane dasu, dan tuni yasa aka bincika masa inda suke, ya kuma shirya
ɗaukar mataki akan Farah data bijirema maganarsa.
Akan gyaran gidansa kuwa Dr Mahmud da Huzaifa ne tsaye akai duk da
gidan bama taɓa zamansa Farah tayiba. Garamashi yankan zauna lokacin da
yake shigowa ƙasar a munafunce.
Ranar da Zinneerah ta cika kwanaki huɗu wajen Hajiya falmata lefen
da Momie ta haɗa gudunmawarta ya iso, sai kuma ga Adilah da Mahma daga
london suma sun iso da nasu kayan lefen, dan AK na sanar da ita komai
bai ɓoyeba, takuma bashi goyon baya ɗari bisa ɗari.
Zokaga yanda Adilah ke murna da farin cikin kasancewarta cikin ƴan
uwa. mahma kuwa abinci kawai taci anan taɗan huta ta nema inda su Mammah
suke, dan bata son ita kanta su san da maganar auren har sai ranar
tariyar insha ALLAHU…………..✍
[ad_2]