MAKAUNIYAR KADDARA 48

Cikin mamaki da ɗaukarta mahaukaciya su Momie ke kallonta, yayinda su Gwaggo Laritu da sukasan hali basubi takantaba, sai maida hankali a murna da farin cikin Zinni tayi goshi da sukai, suna kuma yaddama Inna habaici akaikaice. Cikin ƙanƙanin lokaci gidan ya sake haukacewa da makwafta da yara ƴan kallo, dole aka maida su Mommy ɗaki dan suma su samu suyi salla. Su dai yanda mutan garin keta arerewa akan wannan lefe nasu sai abin ya ƙayatar dasu ainun, Adilah harda yin video dan ita kam wani ƙayatar da ita suke da sakata nishaɗi, sai washe baki take ranta fes.
A waje ma dai yanda mata ke gudun shigowa gidan da yara sai abin ya dinga saka su Khalipha dariya, da birgesu. Dan suma suna zaune ne a ƙofar gidan a ƙarƙashin bishiya ni’imtacciyar iska na kaɗasu.
Haka suka kasance a ƙauyen danya suna kallon yanda ake kai kawo akan ganin lefe. Sai da sukai sallar la’asar sukai haramar baro garin cike da alkairi da tukuyci, duk da sunƙi amsa Baba yace indai basu rainaba su amsa dan ALLAH. Jin furucinsa yasa dole suka amsa suna mai yaba ƙoƙarinsa da dattako. Daga haka akai musu rakkiya suka shiga motoci suka ɗauka hanyar tafiya kano akan sai kuma ranar juma’a sunzo ɗaukar amaryarsu da zata iso zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu itama.
Koda suka taho a hanya labarin yanda al’amarin ya faru suketayi, dan sun baro Inna ta birkicema jama’a kamar sabuwar kamu a hauka. Duk da dai Yaya Gajeje da Karima na ƙoƙarin tausarta. Gida su mmn halima suka wuce, suma suka wuce nasu gidan inda suka kaima hajiya iya labarin farin ciki. AK na zaune a dining yana cin abinci shi da little yana jinsu, sai dai uffan bai tofaba bayan sannu da zuwa da yay musu.
Adilah ce tazo inda yake bakinta a washe ta sumbaci little da tunda tazo take maƙalle da yaron, cikin sabawa daya farayi da ita ta bashi nata kumatun shima yay mata kiss suna dariya. AK dake kallonsu yay ɗan murmushi kawai batare da yace komaiba.
Zama tayi tana fara bashi labari, tare da nuna masa video ɗin da tayo a waya. Shi kansa abin ya burgesa da bashi dariya. amma sai baiyiba yaɗan murmusa kawai yana ajiye wayar da dubanta cike da kulawa.
“Yaushe zakije ki gaida su Mammah?”.
A take fara’ar fuskarta ya ɓace, ta shagwaɓe fuska idanunta na cika da ƙwalla. “Bro ka barni Please basai najeba, kuma bama kace tana katsina ba tunda mukazo da Mahma?”.
“Kema ai katsinan zakije, gobe idan ALLAH ya kaimu zanje sai muje tare na baroki can ki biyo Mahma ranar biki”.
Hawayen da suka cika mata ido suka gangaro, sai kawai ta miƙe tabar dining ɗin ta shige ɗakin Hajiya iya. Binta yay da kallo kawai yana dariya a ransa. Dama tsokanarta kawai yakeyi, shima yaso zuwan amma Mahma ta hana, tace ya bari ai zata ɗakko su Mammah suzo wajen bikin dan dole suma dangin mahaifiyarsa su kasance ai tunda aure abin farin cikine ga kowacce zuri’a. Yanzu kuma Mammah ɗin kanta a zafi yake zuwansa bazai haifar da ɗa mai ido ba.
_________________________________
A washe garin da aka kai lefe hajiya iya ta samu Zinneerah a gidan Hajiya Falmata ita da Adilah. Yanda Zinneerah ta ƙara canjawa a cikin sati ɗaya ya saka hajiya iya jin daɗi matuƙa, hakama Adilah da sau ɗaya kawai suka taɓa ganin juna a london rungume tayi dan tunda ta ga yarinyar dama ta shiga mata rai, da Hajiya iya ta bata labarin komai kuma shima AK ya bata sai ta ƙarajin tausayi da ƙaunar Zinneerah, tare da ƙara taya ɗan uwanta murnar samun mata dai-dai da shi da zata kawo ma rayuwarsa farin ciki tunda Farah taƙi kwantar da hankalinta ta daina biyema Mammah ta riƙe mijinta kamar yanda ta fara a farkon aurensu.
Daɗin yanda Zinneerah tai ƙyau mai ɗaukar hankali yasa hajiya iya harda ƙarama hajiya falmata kuɗi tana jera mata tagwayen godiya. Cike dajin daɗi itama hajiya falmata tace, “Ai hajiya namaso ace daga gidan nan sai gidan mijinta za’a kaita, amma hakanma babu laifi tare dani zata tafi can ƙauyen muɗan ƙarasa abubuwan da suka rage”.
Hajiya iya taji daɗin wannan karamci na hajiya falmata, dan duk da yanda Zinneerah ta canja kogi bayaƙin ƙari. Da wannan damar hajiya iya ta zauna ta sakema Zinneerah nasiha, a yau kuma ta sanar mata an ɗaura mata aure amma bata sanar mata da waye ba. Share-share sai ga Zinni na kuka da hawaye tana kallon haijiya tamkar wata sokuwa.
Cike da kulawa hajiya iya ta kamo hannunta cikin nata da sigar lallashi tace, “Nasan bamu ƙyauta mikiba Inno, amma insha ALLAH wannan shine gatan da zamuyi miki na har abada. Ki saka a ranki wannan itace taki nasarar cin jarabawar, insha ALLAH nasan bazakiyi kuka ba a wajen wanda muka baki, inamiki fatan alkairi da tarin farin ciki mai ɗorewa a rayuwarki da rayuwar aurenki”.
Kasa magana Zinneerah tayi sai kuka, ta faɗa jikin hajiya iya tana abinta. Itace kuma aka ɗaurama aure bayan taci alwashin bazata taɓa aureba. Gaskiya da anyi shawara da ita da haka bata kasanceba, batason tai aure a gorantama little, batason tai aure a aibantata akan ta taɓa haihuwa a waje. Bata da burin daya wuce yin karatu mai zurfi a rayuwarta, sai dai kuma duk waɗanan burikan nata da farga basu kai daraja da kimar hajiya iya ba a wajenta. Ta cancanci sadaukar mata da komai kodan alkairinta a gareta. Takumayi imani hajiya iya bazata badata ga wanda zata cutuba insha ALLAH, dan haka zatai haƙuri tayi biyayya a gareta insha ALLAHU. Ashe shiyyasa mmn sadiq keta mata nasiha mai harshen damo ita da hajiya falmata.
Lallashinta sosai hajiya iya tayi da sake mata nasiha itama tana hawayen, dan dauriya dama kawai takeyi, amma harga ALLAH tana tsananin ƙaunar yarinyar, wannan kuma hukuncine na ALLAH mai saka soyayyar wani a zuciyar waninsa dominsa badan wani abu dake garesaba. Sannan ta sanar mata yau za’a kaita danya wajen babanta, daga can za’a ɗakkota insha ALLAH zuwa gidan mijinta.
Nanma dai Zinni tayi kuka dajin fargabar tunkarar garin nasu data baro bisa ga dalili mai ƙarfi, takumaji ɗokin zuwa taga babanta da akace ya dawo da ƴan uwanta kuma.
Hajiya iya na gidan har Zinneerah da hajiya falmata suka kammala shirinsu na tafiya, sai Saifudden da zai kaisu wanda ya iso gidan hajiya Falmatan daga baya ya samesu.
★★★★★
Koda suka baro gidan hajiya Falmata gidan mmn sadiq suka nufa domin ɗaukar Gwaggo Maryama, ai ko Zinneerah nayin arba da ita ta faɗa jikinta tana kukaama. Ta basu tausayi daga ita har maman sadiq, to amma wannan shine kawai gatan da zasuyima rayuwarta koda ace babu ransu ta dinga tunawa sun mata gata. Dan little ga mahaifinsa kawai zai kasance itama ta samu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya. Lallashinta suka sake zamanyi da mata nasiha, kafin Gwaggo Maryama ta shirya su fito dan da ita zasu wuce danya kafin su Mmn sadiq su biyosu suma daga baya.
Tunda suka ɗauki hanya Saifudden ne kawai ke hira da hajiya falmata da Gwaggo Maryama, itako tayi shiru lafe cikin kujera idanunta a lumshe. Kasancewar tafiyar ba ita kaɗai bace sai taji fargabar tunkarar danyan ta ragu mata a zuciya. Har suka iso gidan mutun ɗaya suka ɗauka hanyar kusada bata buɗe idoba. Sai da taji sun hau hanyar Danya ta buɗe idanu da kallon hanya cike da kewar garinta da tunano abubuwa masu yawan gaske da suka gudana. Isowarsu cikin garin yasa zuciyarta karyewa, sai gata tana hawaye shaɓe-shaɓe.