MAKAUNIYAR KADDARA 48

Zuwa yanzu kam ƴan Danya sun saba ganin yawan shigowar waɗanan manyan motoci, dan haka kai tsaye aka fara ƴan ƙananun maganar cewar angon Zinneerah ne yazo.
Su Zinneerah dai basusan anaiba, dan motar na tsayawa a ƙofar gidansu daya sha gyaran biki da aketa shirye-shiye sai zuciyarta ta ƙara karyewa. Itace ƙarshen fitowa jiki a sanyaye, sai da ta ƙarema anguwar tasu kallo da yara da suka baibaye motar waɗanda takeda tabbacin babu wanda ya shaidata, wasuma basu santaba. Murmushi tayi a karo na farko da ambaton Alhmdllhi cikin matuƙar rauni.
Da sauri ta buɗe idanun nata saboda jin maganar baba dake fitowa yanama Saifudden sannu da zuwa. Juyawa tai a hankali ƙirjinta na harbawa da sauri-sauri. Shima baban tunda idanunsa suka sauka akanta dukkan maganar bakinsa ta gagara fita. Yay tsai yana kallonta zuciyarsa fal wasiwasi. Tabbas fuskarnan dai ta ɗiyarsace, kuma irinta tsohuwar matarsa mafi soyuwa a garesa. Sai dai kuma yana tantama ace Zinneerah ɗinsa ce ta zama budurwa haka tamkar wata jinin larabawa. (Dan gyaran datasha ya sake ƙawatata da ƙyawu mai ɗaukar hankali)
A wani irin slowly Zinneerah ta nufi baba, batama san ta faɗa masa a jikiba ta fashe da kuka ba. Hakan yayi dai-dai da isowar Tinene ƙofar gidan wadda tun ɗazun aka aiketa amma sai yanzu take dawowa gidan, dan yanzu bata samun damar fita yawonta saita hanyar aikan.
Da mamaki take kallon wadda ke runme musu da baba, dan haka cikin sassarfa ta nufi cikin gidan kai rahoto. A zabure Inna data gama yima yarinyar karima wanka ta miƙe, hakama Sa’a dake wanke-wanke. Karima ma madai da Yaya Atine dake a cikin ɗaki sai gasu waje wuff babu shiri. Yaya Gajeje dake can gaban murhu ita da ɗiyar Baba Sabi’u suna suyar naman ragon sunan Karima suma dai duk duban Tinenen sukai, amaryar baba dai datasan ina zancen ya dosa tana ƙofar ɗaki zaune tana gyaran ƙumba da tsohon cikinta, murmushi kawai tayi hankali kwance. Kafin bakin wani ya samu damar furta kanzil sai ga baba ya shigo baki washe yana sharar ƙwalla, hannunsa riƙe da Zinneerah dake kuka rurus. Hajiya Falmata da Gwaggo Maryama biye dasu suna faman murmushin jin daɗi.
Yaya Gajeje ce ALLAH ya bama ikon gane Zinneerah, a take ta saki ludayin hannunta tana ƙwalalo idanu waje da faɗin, “Zinneerah!!”.
Da gudu Zinneerah ta saki hannun Baba tai kan Yaya Gajeje. Bata damu da a yanda yaya Gajejen takeba ta faɗa jikinta suka saki kuka tare. Tuni Sa’a ta saki soson wanke-wanke itama tayo kansu. Su kansu su Yaya Atine da ba ƙaunar Zinneerah ɗin sukeba, kuma tunda aka kawo kayan lefen nan nata ƙiri-ƙiri suka nuna hassadarsu suda Inna basu san sanda suka nufo ƴar uwar tasuba suka haɗu wajen rungumeta.
Hakan da sukai ya matuƙar saka baba jin daɗi, yayinda Inna ta daka musu wata irin gigitacciyar tsawa. Sai dai ina su bama susan tanaiba. Amaryar baba kuwa tashi tai da ƙyar tanama su Gwaggo Maryama barka da zuwa, waɗanda sai yanzu Inna tama gansu. Gabanta ne yay matuƙar faɗuwa datai tozali da fuskar Gwaggo Maryama, dan sarai ta ganeta. A kiɗime tace, “Dangin Hauwa a gidana?”. Karaf kuwa sai a kunnen baba. Kansa tsaye yace, “Hauwarma tana nan tafe a gidan naki”. Ya raɓata ya wuce abinsa dan tabarma zai amsa ya kaima Saifudden.
Ba ƙaramin dukan ƙirjinta furucinsa yayba. Tai baya tana neman faɗuwa ALLAH ya taimaketa ta dafe bango. Babu wanda ya lura da halin da take ciki dansu ta murnar ganin ƴar uwarsu sukeyi.
“Zinneerah kece kika koma haka kamar wata ƴar ƙasar waje?”. Yaya Gajeje ta faɗa tana sharema Zinneerah hawayenta, itako murmushi kawai take ga hawaye shaɓe-shaɓe.
Sa’a dake riƙe da hannunta tace, “ALLAH na gode maka daka nunamin wannan rana da naketa mahwalki da fatan gani, nagodema UBANGIJI daya maido ƴar uwata gida cikin kamala da mutunci harda igiyar aure akanta”.
Yanda take maganar da kuka ya sake raunana zuciyar Zinneerah dasu Gwaggo Maryama da amaryar baba ta sama tabarma a ɗakinta, dan suna jiyosu. Sake faɗawa jikin Sa’a Zinneerah tayi tana sakin wani sabon kukan.
Sai a lokacin baba daya dawo ɗaukama Saifudden buta zaiyi alwala yay sallar la’asar ya ɗauka hanyar komawa ya lura da halin suma da Inna ke ciki. Sallallami ya fara da nufarta, a take suma hankalinsu ya dawo kanta duk suka juya. Ita Zinneerah ma sai yanzu idanunta sukaga Innar.
Ruwa aka yayyafa mata ta farfaɗo, tana buɗe idanu sai akan Zinneerah, ai sai kawai ta fashe da kukan daya bama kowa mamaki da tsoro a wajen. Tashi Baba yay abinsa ya ɗauka butar data kawosa ya fice.
Zinneerah ta matsa jikin Inna tana hawaye da nufin rungumarta, hankaɗeta Inna tai cikin kuka da faɗa. “Munahika karki taɓeni, kinje kin gama yawon tazubar ɗinki zakizo ki goga mana ƙanjamau. To idan uwarki tayo asiri da rufe ido da bakin kowa akan hakan ni na gagareta, asirinta bazai ciniba. Nasan komai kina ikko kina karuwanci, shima shegen da aka ɗaura muku auren ƙaryar abokin cin mushenki ne. ALLAH ya wadatanki tambaɗaɗɗiyar yarinya gantalalla”.
“Kece gantalalliya, ni Sulaiman ban haifi gantalalliya ba”.
Baba ya bata amsa a fusace yana nunata da ɗan yatsa. Ya cigaba da faɗin, “Wlhy kika ƙara aibantamin ɗiya koda da furucin bakine saikin bar gidan nan, bari kuma nahar abada tunda ke bakisan ANNABI ya fakuba mara mutunci kawai.
Wani irin waro idanu Inna tai tana kallon baba, cikin rawar baki tace, “Malam ni kake cewa zan bar maka gida akan Zinni?”.
“Da giduma kuwa, harda jan kati”.
Da sauri Zinneerah ta shiga girgiza kanta tana hawaye. “Baba dan ALLAH kayi haƙuri ka daina faɗi, Inna uwace a gareni, komai ta faɗa a kaina ba laifi bane”.
Baba ya buɗe baki zai bama Zinneerah amsa Gwaggo Laritu da Tinene taje kaima rahoto ta shigo gidan. Zinneerah na ganinta ta miƙe da gudu tai kanta. Sai kuma gasu baba Rabilu suma harda ƴaƴansu. Cikin ƙanƙanin lokaci gidafa ya haukace da sabon murna. Makwafta nata shigowa ganin Zinni. Kafin kace mi zance ya fara yawo amarya Zinneerah tazo kamar an sata a injin gyara mutane ta koma balarabiya.
Haramin da gidan ya ɗauka yasaka kowa mantawa da wata Inna. Har Saifudden ma ya wuce su Gwaggo Maryam basu saniba. Aiko dai a wannan rana Zinneerah bata iya ta samu kantaba har dare, sai can kusan goma yaya Gajeje ta janyeta ɗaki ta bata abinci taɗanci. Daga haka aka zaman sake kafa sabuwar hira dan har zu baba Sabi’u suna gidan har lokacin basu tafiba. Zinneerah ta basu labarin daya sakasu kuka sosai dan tausayi.
Suka shiga godema ALLAH daya saka Zinneerah faɗawa a hannun nagari har ya sadata da mahaifiyarta. Wannan rahamarsace da jin ƙansa ba wayo ko dabarar waninsu ba. Sun kuma tabbatar a katsina aka lalatama Zinneerah rayuwa itama bada sanintaba, saboda a yanda ta basu labarin zuwanta. Inna nata zaginta da tsinarta akan ta mata sharri ita ƙarya Zinneerah tai mata akan cewar itace tasa tabi hajji lanti. Babu wanda yace da ita uffan akan hakan kaf ɗinsu.