MAKAUNIYAR KADDARA 48

Itama Zinneerah tayi kuka jin labarin yanda baba ya kasance, amma tayi farin cikin ƙara aurensa wanda yasa Inna ji kamar ta kasheta, sai dai babu damar yin magana baba ya kafa sharaɗi. Yanda kuwa yayin ta tabbatar zai iya sakin nata akan Zinneerah. Shiyyasa tai gum da bakinta tana binsu da ido, lokaci-lokaci takan fakaici ido ta share hawaye. Dan ga abin faɗa fal a bakinta amma babu damar faɗin sai tsinar Zinneerah dai take kawai.
Murnar dawowar Zinneerah yasa yaya Gajeje kwana a gidan, acewartama sai biki ya tashi kuma kenan. Aiko kusan kwana sukai hira da Zinneerah dan ɗaki ɗaya suka kwana. Hajiya Falmata nason cigaba da aikinta dole ta haƙura, sai dai ta bata abubuwan sha da abinda yake mai sauƙi da bazai takura Zinneerah zaman hira da ƴan uwantaba…………✍
[ad_2]