MAKAUNIYAR KADDARA 49

Cikin rashin damuwa Farah tace, “Amma Mammah sai nake ganin kamar bata hanyar da mukebi zamu iya maidoshi garemuba. Kinsan dai yanada taurin kai, garama ki bari na kasance a kusa da shi maybe naji komai dake faruwa sai mu magance cikin sauƙi”.
Wani alama Mahma taima Farah da ido tana sakin murmushi da ɗauke kanta gefe kamar batasan sunayi ba.
Cike da masifa Aunty Zakiyya tace, “Mammah dan ALLAH barta taje, itace zatasha wahala a hannunsu ai bawani shege ba, su dangin miji har wani abin kwantarwa kai ne. Wlhy banason dangin miji bakuma zan taɓa sonsuba musamman irin naki. Kina dai ganin duk sadaukarwa da Mammah tayi ta bar karatunta da ƙasar data tashi a ciki ta biyo Abbansa daga ƙarshe mata har uku ya aure sai kace wani bazazzage (zazzagawa????????????????), mi ake da namiji mai shegen aure-aure. Kema idan kikai wasa haka kakarsu zatasa Abdul-Mutallab ɗin yayta aure-aure shiyyasa mukeson baki kariya tunkan faruwar hakan amma kina neman watsa mana ƙasa a ido”.
Wani irin tuƙukin bakin cikine da kishi ya tasoma Farah, a take tsanar da Mahma ta fara rage mata nasu Hajiya Iya ta ƙara dawo mata sabo, ganin yanda ta fara nutsuwa da maganar aunty Zakiyya yasa Mahma saurin tsoma musu baki.
Nikuwa da zakuji dakun barta ta tafi ɗin, ta hakanne kawai zamusan mike faruwa? Sannan muji ta tushiyar da aka samar da yaro, tun farkoma da haka kukayi da an wuce wajen, dan irinsu Abdul-Mutallab kwantar da kai sukafi so ga matansu ba shirme da hayaniya ba. Yanda yakeson Farah data lallami kuka bisa ko kuka sakata tabisa ita da kun kamo bakin zaren. Su kuma danginsa wannan kauɗin da kuke sakata tana musu shi zaisa su sakashi ƙara auren dan zasuga tanada ƙarancin tarbiya, tun farko data bisu a yanda sukeso da bahaka ba, kudaiyi tunani gaskiya”.
Zaram Farah ta miƙe tana faɗin, “Mahma maganarki gaskiyace wlhy, ni dai kuyi haƙuri Mammah bara naje, duk halin da ake ciki zakunaji ta waya insha ALLAH ”.
Daga haka bata saurari cewarsuba ta fice abinta dan Mahma ma tama driver dazai kaita magana.
Daga aunty Zakiyya har Mammah sun shaƙa, sai dai yanda Mahma ta haɗe gabas da yamma yasasu kasa cewa komai. Sunaji motar data ɗauka Farah ta wuce badan sunso ba.
Tafiyar Farah kano da kusan awa shidda wanda suka saka ya musu bincike ya iso gidan. Ko gaisuwar kirki basu bari sunyi dashi ba suka fara jera masa tambayoyi akan aikin da suka bashi. Sanin halin aunty Zakiyya yasa baice komaiba ya miƙa musu takardun hannunsa.
Mahma data fahimci komai zai iya faruwa ta dakatar da Mahma daga bude envelope ɗin, “Nikam da kun sallamesa ya wuce sannan zaifi”.
Babu musu Mammah ta miƙe ta ɗakko masa sauran kuɗin aikinsa ta bashi, yaji daɗin haka kuwa ya tafi yana musu godiya, dan ya tabbatar da ace sai da suka duba babu abinda zai samu.
Aunty Zakiyya ce ta fara cin karo da invitation ɗin walima da za’ai jibi idan ALLAH ya kaimu da liyafar cin abinci, jikinta har rawa yake wajen miƙama Mammah. Itama da taci karo da hoton Zinneerah da AK a take ta miƙe cikin rawar jiki tana kallon invitation ɗin. Wani shegen ashar ta kwaso ta dire akan Baffah.
Mahma da dariya ke neman kufce mata tai saurin riƙo hannunta tana girgiza mata kai ganin ta doshi ƙofar fita. “Hindatu ki nutsu mana, faɗamin mike faruwa?”.
“Ai komaima ya faru Addah, ni Kabeer zai rainama hankali, yasan mi yake ƙullawa akan Abdul-Mutallab shiyyasa yace muyi game. Na rantse da ALLAH sai na nunama guy ɗin nan asalin color ɗina. Na shiga uku shikenan ya ƙwacemin yarana. Wlhy bazan bashiba ko sama da ƙasa zai haɗe……”
“A’a bama sai sama da ƙasa ya haɗeba kwantar da hankalinki”. Mahma ta faɗa tana zaunar da ita a kujera. Amma ina Mammah zillewa take tana botsewa hawaye fal fuskarta wasu na korar wasu. Sai masifa take tamkar zata haɗe harshenta. Tana ta rantsuwar saita maka Baffah kotu akan ƴaƴanta dan bazata yarda ya rabata dasuba. Kuma auren AK ta rantse saita rabashi da Farah kawai zai rayu.
Aunty Zakiyya ma masifa take iyakar iyawa. Sai dai ita Mahma batabi takantaba dan nata mai sauƙine. Da ƙyar Mahma ta samu ta taushi Mammah akan ta bari sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu suje Kano ɗin suyi nagana da Baffah. Sanin Baffah na matuƙar ganin girma dajin maganar Mahma yasa ta haƙura akan sai zuwa goben, sai dai tanata neman no ɗin AK a kashe, dan dama Mahma ta sakashi ya kashe wayar, baƙon na zuwa ta turama AK text message.
___________★
A kano kam lafiya lau Farah suka isa. Kasancewar dama shirine tsakanin AK da Mahma kai tsaye gidansa aka wuce da Farah ɗin. Taji daɗin hakan dan bata ƙaunar zuwa family house ɗinsu dama. Ta gwammaci suyi zamansu nan su biyu hartaji gaskiyar zance akan little. Dan ba ƙaramin yaƙi zatai da zuciyartaba wajen bin shawarar Mahma akan ta kwantar da hankalinta wajen AK.
Shiko AK duk da abinda tai masa naƙin bin umarninsa datai ta koma haka ya danne yay mata tarba data bata mamaki. Daga ƙarshema suka shiga duniyar soyayya. Biye masa tayi da ƙoƙarin danne damuwarta, amma duk da haka sai da ta tambayesa ina ya samu gida?.
Murmushi kawai yay mata da kissing goshinta, a AK ɗinsa data sani mai tattalinta da bata kulawa ya amsa mata da cewar, “Gidanki ne da baƙyason zuwa, ina fata dai komai ya miki?”.
Fuska taɗan ɓata tana gyara kwanciya a jikinsa, “My hero ko yamin miye amfaninsa tunda ba zama cikinsa zanyiba, dama ka sayar kayi wani hidimar da kuɗinka danni nanda sati gudama zan koma london”.
Wani shegen murmushi ya sakar mata da kashe mata ido ɗaya, yace, “Yayi Mrs Shira, nifa shiyyasa kike matuƙar birgeni”.
Yanda yay mata ɗin ya sakata nishaɗi ta ƙara ƙanƙamesa tana dariya. Da ga haka suka sake komawa duniyar masoya ƙasan ran kowa da abinda ya damesa, sai dai sunata ƙoƙarin ɓoyema junansu bisa mabanbanta dalilai.
Washe gari tunda safe AK yabar gidan bayan Khalipha da kansa yazo ya kawo musu breakfast, lokacin ma Farah nashan barcin gajiyar murzar juna da sukai jiya, shima sai note ya bar mata suka fice tare da Khalipha.
*_DANYA_*
A Danya shagalin biki ake na gaske, dan dangin mmn sadiq har safiyar yau zuwa sukeyi, hakama abokan arziƙinta na nan danya sunta zuwa mata baici duk da zuwa yanzu ta wuce da saninsu. Kusan goma na safe sai ga dj da kayan kiɗa dasu Haneef, dama sun haɗa ɗan meeting nasu zasuzo Danya su cashe tunda Yayansu ya hanasu a kano, su dukansu suka taho har Adilah da ƴaƴan Uncle Ahmad da zuwa yau dai sun zama ƴan gari kodan halin su Haneef na barkwanci.
Sosai isowarsu da dj ya karama bikin armashi, dan a take suka warware sauti biki ya ɗau harama ƴan danya suka ƙara shaidawa. Dan su Meenal da ƴan ɗan musa filin rawa suka shi su Moos’ab suka dinga zazzaga musu liƙi. Yaran gari dana dj na daka wawa. Al’amarin kamar wasa saiga biki yayi armashi, dan ita Zinneerah harma ta faraji a ranta ko Moos’ab ɗin aka aura matane.