MAKAUNIYAR KADDARA 49

    Tayi ƙyau cikin less lemon green da ratsin orange, Meenal ta tsara mata kwalliya ta fito ɗas a amaryarta abin shawa da birgewa. Gyaran da tasha yana nuna kansa a fartarta da ƙamshinta da duk inda ta zauna sai ya cika waje. Ga lalle tasha a daren jiya da yay matuƙar mata ƙyau. Badan tasoba Jamal ya jata har tsakkiyar fili inda su Saifudden suka rufeta da liƙin ƴan ɗari bibbiyu sabbi ƙal. Ai sai bama tasan lokacin data fashe da kuka ba bisa dalilai masu yawa. Hakan da sukai yasa yaya gajeje ma zuwa ta farama Zinneerah liƙin ƴan hamsin-hamsin tana hawayen daɗi, sai ga Sa’a da chewing gum da sweet itama data siya ta fara zazzagesu akan Zinneerah. Aifa sai guri yaɗau ihu da sowa dan sun burge. Gwaggo maryama ma shigowa tai tayi nata liƙin, suma sai ga ƴan ɗan musa suna nuna tasu bajintar kowa dai-dai karfinsa. Wanima naira 100 zaizo ya liƙa mata ya fita.

      Wannan al’amari ya ƙuntata zuciyar Inna matuƙa, har takai ta yanke jiki ta faɗi sai da akai kama-kama wajen kaita ɗakinta. Sai Karima da Atine da Tinene da nunkufurci kecin ransu suka zauna da ita a ɗaki suna zage-zage wai da biyu su maman sadiq sukazo suka kafa bikin ai dama a danya. Duk da wasu a ƴan uwan mmn sadiq ɗin sunji sai basu kulasuba. Dan tunkan su taho an roƙesu kosunzo dan ALLAH karsu shiga sabgar Inna Asabe komi zatayi, dan su dai farin cikine ya kaisu suje ayi a tashi lafiya a miƙa amarya ɗakinta. Da wannan yasa suka sharesu.

    Su Yaya Gajeje kuwa basusan mike faruwaba suna can anashan dj dasu a waje hankali kwance.

     Shagali kam dai an shasa sai dai ace Alhamdulillahi, Zinneerah tayi kukan daɗi, tayi na damuwa, tayi na godiya ga ALLAH, ansha hotuna kuma da mai hoto dasu Mas’ood sukazo dashi, zuwa ƙarfe huɗu kuma sai ga motsocin ɗaukar amarya sunzo.

     Kasancewar Zinneerah tasha faɗa wajen iyaye da kakanni tun a daren jiya sai yazam yau sallama kawai aka kaita taima su baba da danginsa. har ɗakin Inna da sai yanzu kowa yasan da faɗuwarta, amma kasancewar ta farfaɗo hakan bai hana su Yaya Gajeje shirin raka ƙanwarsu ɗakintaba. Hardasu Karima mai jego kuwa dan sunce sai sunje sunga uwar da ake nusu fariyya da ita sukam.

    Inna bata hanasuba, dan itama daga ƙarshe catai zataje duk da halin da take a ciki na alamar ciwo. Dan ko gani batayi daƙyau saboda jininta da ya hau sama ƙololuwa dan damuwa da ruɗanin tashin hankalin da take a ciki. Baba zai hanata Gwaggo Laritu tace ya barta. Ai gara taje ta gano komai da idanunta zaifi. Amma yace sam bazatajeba sai daga baya saje da amaryarsa idan ALLAH ya sauketa lafiya. Tamaji da kanta. Badan tasoba dole ta haƙura dan da gaske tana a cikin wani hali dannewa kawai takesonyi dan zuwa taga ƙwaƙwaf. Amma tunawa ga ƴaƴanta nan yasa ta haƙura ta shige ɗaki tana kukan da bataso kowa ya gani.

       Tunda aka saka Zinneerah ta shirya bayan an ɗanƙara mata nasiha take rusar kuka da shiga tashin hankalin tunanin wanene mijin nata. Dan yanda Moos’ab ya nuna mata baiyi kama da miji a garetaba. Sai dai idan suna ɓoyewane har sai taje can ta gani. Kasancewar an turo motoci babu laifi kowa sai da ya samu wajen zama duk da wasu a matse suka tafi, ga kuma motocin ƴan ɗan musa suma sun sake taimakawa. dan a danya har ƴan gayyar soɗi dason ɗakko rahoto sai da sukabi.

     Motar da baba ya kama amarya Zinneerah kuwa ya saka da hannunsa sabuwace dal a ledarta Baffah ya bada a ɗakkota ciki, ita da Gwaggo Laritu da wata Gwaggo Aisha ƴar ɗan musa suka shiga tana tsakkiya, Adilah na gaba kusa da Huzaifa da zai ja motar. Wasu a cikin baƙin ɗan musa zasu wucene gidan mmn sadiq sai zuwa gobe suje suga ɗakin amarya kafin su koma gida. Dan haka motocin ɗaukar amarya sun riga su mmn sadiq tafiya dan su sai da sukai zaman yin sallama da mutane da godiya ga baba sannan suka taho gab da magriba.

Zuwa lokacin motocin ɗaukar amarya tuni sun isa cikin kano har Shira’s house, inda Zinneerah keta kwasar kuka har suka iso gidan. Gidan da take zaune a cikinsa matsayin ƴa gata ta dawo a matsayin amarya.

     Hajiya iya da kanta ta fito ta tarbi Innon ta bakinta kamar zai yage dan fara’a. Zinneerah ta faɗa jikinta tana sakin wani sabon kukan. Itama rungumeta tayi cike da farin ciki.

      Ƴan kawo amaryama sun sami tarba ta mutunci da girmamawa. Inda aka saukesu a sashen Mommy dan sassan gidan duk cike suke da baƙi, hatta sashen Uncle Ahmad da matarsa keta baƙin rai sai da hajiya iya ta tura baƙi idanma mutuwa zatai ta mutu matsalartace cewar hajiya iya.

     Zinneerah kuwa direct sashen hajiya iya aka nufa da ita. Baƙi kuwa aka sake karramasu da lafiyayyen abinci mai rai da lafiya. Aikam su kam warshan, dan babu wanda yayma kansa mugunta ci sukai sukai nak banda Tinene da ta faraci tahau amai.

     Wannan abu ya bama kowa mamaki har aka shiga kallan kallo, amma gudun tada zaune tsaye Gwaggo Laritu da ke kallon tinene gabanta na faɗuwa ta janyeta gefe tana sanarmusu shawarace taima Tinene mugun kamu. Shiru dai kowa yayi badan baida abin faɗaba. Musamman ma su yaya Gajeje da tsoronsu ya fito ƙarara a fuskokinsu suna bin Tinenen da kallo.

        Bikin mata ya cigaba da gudana a cikin gidan, dan sai zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu za’ai walima and liyafar cin abinci, su AK kuma bayan isha’i zasuyi fatin da su Huzaifa suka shirya wanda sai a yammacin yau yasan dashi. Faɗa yaytayi su Dr Mahmud na lallaɓashi, sai da yaji iyakar su mazane kawai ya sami nutsuwa ya sassauta masifar yana maida numfashi. 

         Dole badan yasoba yay shirin cikin ɗanyar shadda bayan sallar isha suka tafi hall ɗin da fatin zai gudana. bayan yama Farah dabara irin na maza akan zaije bikin wani abokinsa ne. Sanin baya zuwa irin waɗan nan abubuwan da ita saboda kishi yasa batako damuba……………✍

[ad_2]

Previous page 1 2 3

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button