Uncategorized

MAKAUNIYAR KADDARA 5

 *_Typing????_*

     *_????MAKAUNIYAR ƘADDARA!!????_*

                *_Bilyn Abdull ce????????_*

*_HAPPY HAUSA DAY!!????????????????_*

         _Inama ɗaukacin al’ummar HAUSAWA na duniya baki ɗaya murnar zagayowar wannan rana ta HAUSA ta duniya. Alkairin ALLAH yakai gareku a duk inda kuke,

ALLAH ya ƙara ɗaga darajar HAUSA da ɗaukacin HAUSAWA baki ɗaya. Harma da sauran yarukanmu????????_????

*Page 5*

……….Lallai da gaske shirin biki ake na ƴar gata. Dan bama Inna kawai ba hatta da Atine dake aure Rimaye ta shiryama bikin. Ko kayan ɗakin Karima daga can akayosu. Ita dai Yaya Gajeje bata biye musu. Sai ma nuna musu illar ƙulla wannan aure takeyi. Dan ta tabbatar an cuci Zinneerah. Tun abin bai kai hakaba take ma Inna magana amma bata saurarenta. Sai ɓacin rai dake biyo baya a tsakaninsu akan hakan. Zuwa yanzu kuma data tabbatar sunyi nisa saita zuba musu ido. Dan akwai ranar ƙin dillanci ai. Kuma nasihar baba ta shigeta. Dan shima da kansa yace ta barsu karta sake cewa komai akan auren. Inhar an cutama Zinneerah ne akan hakan ALLAH na nan baya barci.

         Tun ra da aka kawo lefe lafiya taima Zinneerah ƙaranci, a haka ta daure take komai na rayuwarta data saba. Harma ta ida zana jarabawarta ɗaya data rage ranar litinin. Sun kammala junior secondary school kenan suna jiran result kuma ya fito aga abinda ALLAH zaiyi.

         Biki kam dai shiryashi ake sosai kamar yaune aka fara aurar da ƴa a gidan. Ita dai Zinneerah nata ido ne kawai, sai idan ta keɓe ne takan sha kukan zuci. A randa aka saka Karima a lalle jikinta yay tsanani, har takaita da kaiwa kwance dole.

      Cike da damuwa Yaya Gajeje ta takura mata taci alala da suka girka a gidan saboda baƙi da sukazo daga marabar musawa dangin Inna. Da ƙyar Zinneerah ta iya cinye guda ɗaya sai amai. Kowa ya tausaya mata anata mata sannu. Harma wata ƙanwar Inna na cewa shawara ce a nemamata sassaƙe tasha. Itadai bata iya magana sai amsawa da kai harta samu ta koma ɗaki ta kwanta.

     Cikin tsoffin da sukazo daga maraba ne ɗaya ta dubi Yaya Atine dake gefenta tana shayar da ƴarta da take goyo. “Niko nace Atine”.

      “Na’am Gwaggo ladi”. Yaya Atine ta amsa tana kallonta tana maido hankalinta gareta. Wadda aka kira da Gwaggo Ladi tace, “Wanan ƴar uwar taku tayi aure ne dama bamu da labari?”.

      Da mamaki a fuskar Yaya Atine tace, “Gwaggo wai kina nufin Zinneerah? Indai itace batai aureba. Yaya zatai aure baku jiba”.

     Cikin waro idanu na alamar gulma tace, “Kanjakar ubancan kayyasa. To lallai idon Asabe a rufe yake a gidan nan bata bahimtar komai daɗa”.

      “Gwaggo miyasa kika hiɗi haka”. Yaya Atine ta sake faɗa tana duban Gwaggon nasu da ƙyau.

     “Uhm-uhm babu komai Atine. Kawai dai naga abinda yafi ƙarhin ganina ne. Dan wannan ɗiyar ciki ke ga jikinta, harma ya tasa gashi nan”.

      A razane Atine ta saki ƴarta ƙasa da dukan ƙirjinta tace, “Gwaggo ciki?!! Zinni ɗince ke da ciki!!?”.

     Yanda tai maganarne ya jawo hankalin sauran mutanen dake a gidan kansu. Ga ƴarta data saki ƙasa ta tsage da kuka saboda zafin faɗuwar da taji..

            Yaya Gajeje ma a ruɗe ta saki kwanon data ɗakko zata saka a sayoma Zinneerah kunu ko zata iya sha. Ta ƙaraso gasu Atine da sassarfa tana faɗin, “Atine wannan wane irin mugun alkaba’ine kike hiɗi dan ALLAH?”.

        Da sauri Atine tace, “A’a yaya Gajeje bafa ni na hiɗi ba….”

     “To waya hiɗi?”.

Gajeje ta katse ƴar uwar tata.

         “Kunga bafa zancen hayaniya bane ba Gajeje. Ku kira yarinyar tazo nan”. Gwaggo Ladi duk ta katsesu.

       Zinneerah na ɗaki kwance tana sauke numfashin wahalar amai da tayi wata cikin ƴan bikin ta shigo ɗakin tana ƙwala mata kira. Miƙewa tai daga kwancen da take a razane tana dubanta batare data amsaba.

    Matar tace, “Kinga taso ana kiranki a waje”.

         Batare da tunanin komaiba Zinneerah ta miƙe ta biyo bayanta cike da dauriya. Tana fitowa gabanta ya faɗi ganin kowa na gidan ya zubo mata idanu, har waɗanda ke a cikin ɗakin Inna duk sun fito tsaye cirko-cirko. Rasa ina zata dosa tayi dan ruɗiya. Sai da yaya Gajeje tai ƙarfin halin kiran sunanta cike da tashin hankali. Dan ita kanta kam zuciyarta ta fara gaskata zancan tsohuwar saboda wani irin canjawar da Zinneerah tayi, wanda ada sam hankalinta bai taɓa bata abu makamancin ciki ba akan canjin….

     Ƙarasowar Zinneerah inda suke ne ya katse tunaninta. Tsohuwa Gwaggo Ladi ta kamo hannun Zinneerah ta buɗe tafin tana kallo, ta kuma ɗago fuskarta ta gwale mata idanu nanma. Sai kuma tace ta buɗe bakinta ta turo harshenta waje. Ita dai Zinneerah babu musu komai yi take cike da tunanin ko wani ciwone ya kamata. dan a watani uku ɗin nan data dawo gida ƙwarai da gaske tanajin canji sosai a jikinta wanda batasan kansa ba…..

       “Wlhy wannan yarinyar ciki ne da ita Asabe. idanma baku yarda ba ku kaita ayi gwaji wajen likita”.

     Zancen Gwaggo Ladi ya katse tunanin Zinneerah. Yayinda a take gidan ya harmutse da salllami da gulma. Sam Zinneerah bata fahimci komai a zancen Gwaggo Ladi ɗinba, duk da yanayin mutanen dake gidan ya sake sakata a tashin hankali.

     A haukace Inna tazo ta kai hannu zata kai mata maguza wata ƙanwarta ta tare tana janye Zinneerah ɗin. “Haba Asabe, ita dake cikin wannan halin zaki kaima wannan bugun? Kamata yayi a bita a sannu asan inda al’amarin ya hito ai ko?”.

         “A ina ya hito banda wajen yawonta na tazubar Haule. Idan na hiɗi ya rinyarnan nabin maza sai ace sheri nake mata dan ban haiheta ba. Kwanan nan fa tahiya tai babu wanda yasan ina taje kusan mako huɗu sannan ta dawo. Amma da yake ubanta shashasha ne bai ɗauki wani mataki a kantaba. Wace irin makauniyar rayuwace wannan? Na rantse da ALLAH bata zaunamin gida da cikin rariya. Sai dai ta koma can gidan wanda ya ƙunsa mata masihwar su ƙarata tambaɗaɗɗiyar yarinya”.

      Yanda Inna ke masifa kamar zata haɗiye harshentane ya saka gidan yin tsit kowa yana saurarenta. Yayinda hajijiya take juyama Zinneerah garin a hankali. Babu zato sai ganinta kawai akai ƙasa ta zube.

     Babu wanda yay yunƙurin taimaka mata sai Sa’a dake kuka tun farkon fara maganar, ta taho da gudu ta durƙusa gabanta tare da ɗagota jikinta tana jijjigata. Tsawa inna ta daka mata akan ta tashi a wajen kota tsine mata.

     Cikin kukan Sa’a ke girgizama Inna kanta. “Haba Innarmu! Haba Innarmu!. Wlhy Innarmu Zinni ba ƴar iska bace. Wlhy Zinni bata iskanc……”

    Ta kasa ƙarasawa saboda kukan daya sarƙeta. Yaya Gajeje ce ta tako inda suke itama tana share hawaye da bakin zaninta. Ta durƙusa ta kamo kan Zinneerah dake a jikin Sa’a ta maido kan cinyarta tana fashewa da kuka maiban tausayi…..

         Bayyana irin tashin hankalin da Zinneerah ta tsinci kanta a cikin wannan rana da duk wani masoyinta ma ɓata lokacine. Hatta da maƙiyan nata jimami suke nunawa a zahiri, a baɗini kam ransu fari tas musamman ma Inna da ke ganin fatanta ya tabbata.

       Kamar yanda Zinneerah ta yanke jiki ta faɗi sai da aka zuba mata ruwa haka Baba ma da labarin ya riskesa tamkar saukar aradu ya zube babu numfashi sai da aka zuba masa ruwa ya farfaɗo da ƙyar.

      Kafin wani dogon lokaci garin ya ɗauki zance Zinneerah tayi cikin shege. Tofa abin nema ya samu ga masu ƴancin faɗin albarkacin baki. Wasu suce mugun alkaba’in Inna ne ya kamata, wasu suce wahalar da Innar ke batace ta kaita da fara bin mazan ai. Wasu suce babu wani dama halintane. Dan kawai tana shan wahala a gidansu sai ta bi maza.

1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button