Uncategorized

MAKAUNIYAR KADDARA 5

     Kowa dai da inda nasa furucin ke sauka. Duk da ba yaune ainahin ɗaurin aure ba sai ga mutane na tururuwar shigowa gidan gulma da son ganin ƙwaƙwaf. Ƴammata kam harda waɗanda Karima ma bata gayyata zaman ƙunshin ba sai gasu.

      Inna kam tanata zabga bala’i sai Zinneerah ta bar mata gida ƴan uwanta na tausarta. Yayinda Zinneerah ke a ɗakinsu tare da Baba da Yaya Gajeje da Sa’a. Sai wasu ƙanen Baban maza su uku da mace ɗaya sun turketa akan saita faɗa musu a ina ta samo wannan jidalin?…

      Kuka Zinneerah keyi tamkar numfashinta zai rabu da gangar jikinta. A karo na babu adadi ta sake faɗin, “Wlhy! Ta-kwaran-kwatsa Kawu ban taɓa aikata iskanci ba. Wlhy ni banda ciki.”

       Cikin daka mata tsawa Kawu haruna yace, “Kinci uwarki Zinni. Su waɗanda sukace kinada cikin zasu maki ƙarya kenan? Bayan duk ga alamomin mai juna biyu tattare da ke. Idanfa baki hiɗi mamu wanda kukai wannan lalatar to kuwa kina barin garinga kije can ki nema wasu iyayen bamuba. Dan bamu zama da mai halin banza cikin zuri’armu kau…”

        “Ai bama barin gariba ni nan da kake gani rami zansa amani na bizneta da ranta har sai ta mutu idan bata hiɗi mamu gaskiya”.

     Tirƙashi. Tunfa su kawu nabin Zinneerah da lallami akan sanin gaskiyar magana har takai Kawu Sabi’u da fara bugunta amma ta kafe akan itafa bata taɓa aikata abinda ake tuhumarta ba. Tsabar tashin hankali kowa kansa ya ɗauki zafi. Baba ma ya kasa magana sam.

     Ganin suna neman halaka yarinya wata a cikin ƴan uwan Inna dake aure a kankia tace, “Kunga karkuce ta wannan hanyar zaku tuhumi yarinyarnan. Sannan har yanzu babu tabbacin cikinne a jikinta ko saɓanin haka. Kamata yayi ku sami likita yay mata gwaji, idan an tabbatar cikinne sai a bita ta hanya mai sauƙi a binciketa bawai ta kwakwazo da azabtarwaba. Dan yanzu idan cikinne ai sai kuyi mata lahani ita da shi k…….”

       “K Halima bamu son tsarin banza da wohi. Kinason hiɗin ita Yaya Ladi ƙarya tayi kenan da tace akwai cikin? Bayan duk wanda ya kalla wannan sheɗaniyar yarinyar zai tabbatar da alamomin mai ciki tattare da ita…”

       “Ba haka nake nihi ba yaya Asabe. Tayaya zan ƙaryata Yaya Ladi ni kuwa. Ni dai ina nuna maku muhimmancin bin komai a sannune. Yanzu wannan ruɗama yarinyar tunani da bugun nata da akeyine zaisa ta hiɗi gaskiya? A ganina idan anbi komai a sannu sai a kamo gaskiyar al’amarin da mahwarinsa basai anbi hanyar ilatata ba a dawo kuma ana dana sani”.

    Inna zata sake magana Yaya Gajeje ta katseta. “Maganar Gwaggo Halima gaskiyane. Ya kamata mubi komai a sannu kawu. Dan kowa yasan halin Zinni bazata aikata wannan al’amari da ganganba inma har ya tabbata hakane. Ba muba ko jama’ar gari idan zasu hiɗi gaskiya sunsan Zinni yarinyace mai nutsuwa da haƙuri. Wlhy inaji a raina inhar da gaske ciki ne a jikin Zinni sai dai ɗayan biyu ne ya hwaru. Kodai wani la’ananne ne yay mata wayo ya ɓata mata rayuwa. Ko kuma acan inda ta baro wani yay mata hin ƙarhi ya aikata mata wannan zaluncin. Ku tunafa yarinyarnan nemarta akai aka rasa rana tsaka. sai kuma gata ta dawo babu zato. Abin mamaki kuma tamkar an rihe mana bakuna har yanzu bamu sake bi takanta muji yaya akai tabar garinga ba ta kuma dawo? Miya hwaru da ita data tahi? Ina taje? Waye silar hitar tata? Duk bamu binciketa b……….”

       “Gajeje!!!” 

  Inna ta faɗa da wata irin mahaukaciyar tsawa tana nunata. Ta cigaba da faɗin, “Na rantse da ALLAH idan baki hita batun wannan ƴar iskar yarinyar ba daga yau sai na tsine maki a gidan nan ke da Sa’a. Har uban waye zai hiddata a gida da gari banda abokan iskancinta wanda ga sakamakon abibda takeyi ɗin nan ya bayyana kowa ya gansa”.

      Dubanta Gajeje tayi zatai magana. Sai kuma mita tuna oho tai shiru kawai tai ƙasa da kanta tana sharce hawayen dake sakko mata.

        Har dare gidan ya gagara komawa dai-dai. Zinneerah kam tana can ƙuryar ɗakinsu ta ɓuya tana cigaba da kukanta. amma duk da haka bata kasa jiyo yanda ake aibantata a tsakar gidanba ita da mahaifiyarta a bakunan wasu a cikin dangin Inna. Yayinda ƴammata masu zaman ƙunshin Karima suka fara raira mata waƙa cikin habaici da izgili kamar yanda Karima ta sakasu.

     Babu wanda ya hanasu, dan Yaya Gajeje tabar gidan tun ɗazun. Baba kuwa yana zaune daga can bayan runbunsu shiba mai rai ba shiba gunki ba. Sam zuciyarsa da ƙwaƙwalwarsa basa aiki irin na mutane.

        Duk da ƙarancin shekarunta yinin yau ya sake tabbatar mata da rayuwa ta sake kaita wani ajin jarabawar da yafi zaman gidansu ƙunci da tashin hankali. Ita dai ko Al-qur’ani aka bata zata iya rantsewa da shi akan bata taɓa aikata iskanci ba, amma sai gashi yau an wayi gari ita ake kira da suna mai ciki, cikinma cikin shege. Ta sake fashewa da kuka mai cin rai.

★★★

        Zamu iya cewa a wannan dare barci ɓarawo ne kawai ya saci Zinneerah kasancewarsa gwanin iya sata. Amma badan taji sha’awar yinsaba ko buƙata.

      A kiran sallar farko ta tashi, taji daɗin jin gidan shiru alamar kowa bai tashiba. Ta lallaɓa ta fito zuwa bayi. Bayan ta kammala lalurarta tai alwala ta sake shigewa ɗakinsu. Daga haka bata sake fitowa ba har sai da rana ta haska. Zuwa lokacin gidan ya cika da hayaniyar baƙi da yaransu. Kamar jiya dai kowa da zancen cikin nata ya tashi a baki, hakan yasa ta sake maƙurewa a ɗaki taƙi fitowa.

    Tana zaune kanta cikin gwiwarta taji muryar Gwaggo Laritu ƙanwar su baba na kiran sunanta. Kanta ta ɗago muryarta data sha kuka a dusashe tana amsawa. Fuskar Gwaggo Laritu a haɗe tace, “Taso ki hito”.

       Sosai gabanta ya faɗi, sai dai babu damar musu dole ta miƙe tana rangajin yunwa da damuwa. Kamar jira ake ta fito tsakar gidan yay tsit idanu caahh a kanta. Tai ƙasa da kai zuciyarta na tsitstsinkewa dan tashin hankali…

      “Munahika, ƴar iskar yarinya. Ƙyahwa ta duƙar da kai kamar balamar tunkiya tunda kin kwaso mamu abin kunya”.

    Inna ta faɗa tana jan tsaki. Ita dai Zinneerah kanta a duƙe bata yarda ta kalli kowaba. Ta kuma kasa ɗaga ƙafarta dan batasan ina zata dosaba. 

        Sa’a ce ta taso daga inda take zaune tazo ta kama hannunta, itama muryar tata a dasashe alamar tasha kuka tace, “Muje Zinni, su baba na jiranki a zaure”.

     Da ƙyar ta iya ɗaga ƙafafunta tabi Sa’a har zauren. Baba na zaune shi da su Kawu Haruna. Ƙasa ta zube cikin rawar murya tana gaishesu. Babu wanda ya karɓa mata, sai Gwaggo Laritu ce tace, “Ya kamata mutahi kar rana tai tsaka tunda ta hito”.

     Nanma babu wanda ya iya cewa komai, sai miƙewa da su kawun sukai amma banda Baba da kansa ke ƙasa. tunda Zinneerah ta fito ko motsi baimayiba. Koda sukai masa sallama zasu tafinma bai motsa ba. Bai kuma ce uffanba har suka tasa Zinneerah gaba suka fice.

      Mashina biyu dake jiransu suka taras a ƙofar gida. Kawu Sabi’u da Kawu Haruna suka hau ɗaya. Ita kuma da Gwaggo Laritu suka hau ɗaya batare da tasan ina suka nufa ba. 

         Ƙasa zinneerah tai da kanta har suka baro cikin garin Danya. Wanda tasan tunda kasancewar safiyane kowa yaga tahowar tasu, waɗandama basu ganiba zasu samu labari ga waɗanda suka gani ɗin.

          

      Har cikin Kusada masu mashinan nan suka kaisu babban asibitin Kusada. Kasancewar ɗan mashin ɗin daya goyo su Kawu babban ɗan Kawu Sabi’u ne shine yay musu shige da ficin komai har suka sami ganin likita kusan sha ɗaya na rana. Duk da a matuƙar tsorace Zinneerah take bataƙi amsa tambayar da duk likitan yay mata ba. Bayan ya gama mata tambayoyin yasa aka kira masa wata matashiyar budurwa. Zinneerah ya nuna mata yana faɗin, “Maryam kuje da ita tai hitsari akaima Bashir”.

Previous page 1 2 3Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button