MAKAUNIYAR KADDARA 53

Page 53
…………Bai nuna yama fahimci yanda ta firgitan ba ya fara magana a hankali da ƙoƙarin buɗe kular tana a jikinsa. “Wannan ba aikin amarya bane, koda yake amaryan marowaciya ce”.
Yanda yay maganar a saitin kunnenta yasa tsigar jikinta tashi, ga ɗunbin mamakinsa dan batai zaton sa hakaba sam. ta ɗan ƙanƙame jikinta daya fara rawa dan wannan shine karon farko a rayuwarta data kasance da namiji a irin wannan kusanci. Abin tashin hankalin ma da ɗunbin kunya namijin ya kasance Yayansu, abinda bata taɓa kawowa a mafarkintaba balle hasashe.
Ƙamshin naman kazar da akaima gyara na musamman dake kular daya buɗe ɗin taɗan kalla jin yace, “Uhm-uhm Momie ta hutar dani sayen kazan amarya kenan”.
Ba ƙaramin mamakinsa ke ƙara dasuwa a rantaba, ta haɗiye yawu da ƙyar dan bata da burin daya wuce ya matsa daga manneta da yayi. Harta fara murna ganin ya maida kular ya rufe, ya ɗan matsa baya kaɗan yana raba jikinsa da nata. Sai kuma taji ya kamo hannunta cikin nasa ya juyo da ita suna facing juna.
Sake dulmiyewa cikin matsananciyar kunya tayi, tai azamar duƙar da kanta zuciyarta na harbawa da sauri-sauri. Shiko tsaywa ya gyara da ƙyau yana tura hannayensa cikin aljihun wandonsa. Duk da kanta a duƙe yake tanajin yanda idanunsa masu kaifi da ƙarfi suke yawo a jikinta. Tsahon mintuna biyu suna a haka har takaita ga daburcewa takai tsugunne tana cemasa ina kwana.
Dariya ta bashi sosai, musamman daya san dama da biyu yay mata hakan, amma ya gimtse baiyiba. Sai ma ɗan ranƙwafowa yay ya kamo kafaɗunta ya miƙar da ita tsaye tare da jawo kujerar dining ɗin ya zaunar da ita. Shima sai yaja ta kusa da ita ya zauna.
Yana ƙoƙarin buɗe kular dake kusa da shi cikin ɗan rawar muryar da jin nauyinsa ya haifar mata tace, “Kabari zan zuba maka Yayanmu”.
Komai baice mataba ya janye hannunsa. Hakan yasata miƙewa tsaye ta jawo plates ɗin data ajiye sannan ta bubbuɗe kukolin.
“Miza’a zuba a ciki”.
Tai tambayar batare data yarda ta kallesaba.
“Duk wanda yay miki” ya bata amsa yana ƙoƙarin ɗaukar wayarsa da kira ya shigo.
Cike da fargabar karta zuba abinda bayaso ta haɗa komai a gabansa, harda kunun gyaɗa dake cikin flask madaidaici, daga haka ta ɗanja kujerar baya da nufin barin wajen ya riƙo hannunta. Juyiwa tai ta ɗan kallesa dan ta zata wani abun yake buƙata. Da idanunsa dake lumshewa da buɗewa kamar maijin barci yay mata nuni data zauna. Babu zance musu a tsakaninsu dan haka ta koma ta zauna.
Wayarsa ya cigaba da yi da ɗaukar wani cokalin bayan wanda ta saka masa ya ajiye a gabanta, ya ja kofi ya fara haɗa kayan tea dake a dining ɗin a ciki. Ita dai bata motsaba tanata satar kallonsa da tunanin ko bazaisha kunun bane?, harya kammala komai ya buɗe ɗayan flask ɗin da ruwan zafi ke ciki ya tsiyaya. Motsawa ya farayi dai-dai suna sallama da Huzaifa dake faman masa sheri, ya ajiye wayar gefe da ɗaukar kofin ya ajiye gabanta muryarsa ƙasa-ƙasa yace, “Bismillah”.
Dole ta ɗago kai ta dubesa. A lokacin shi kuma yana ƙoƙarin kai Irish daya ɗebo bakinsa. Kai ta ɗan girgiza tana marmar da idanu tace, “Yayanmu na ƙoshi ni sai anjima zanci”.
Bai fasa cin abincinsaba bai kuma tanka mataba. Hakan da yay ta tabbatar bata da amsa kenan, dan haka ta ɗauka kofin tea ɗin ta fara sha badan yana mata daɗi a bakiba saboda zazzaɓin da take fama a kwana biyun nan.
Ko’a can gidan tasan baya wasa da abinci, cinsa yake bil haƙƙi idan ya samu musamman zaɓinsa. Dan haka ta dinga satar kallonsa zuciyarta na tuno mata ko ina little yake yanzun?.
Ganin batacin abincin ya ɗago ya dubeta, karaf ya kamata tana satar kallonsa. Janyewa tai cike da basarwa. Yanda tayi ɗin ya sakashi sakin wani munafikin murmushin daya tsaya masa iya maƙoshi yana mai jinjina miskilancinta a ransa.
A fili kam sai yace, “Gulma dai ajaline. Kisa hannu kici abinci kona ɗura miki shi dan na gaji da wannan jan ajin.”
Wani irin waro idanu Zinneerah tayi a kansa babu shiri, har cikin ranta mamakine ke neman kasheta dan batasan bakinsa ya iya zaro zanceba kamar haka. Ganin yanda shima ya waro mata nasa manyan idanun masu kwarjini da faɗin, “Zancen nawa akwai gyara ne?” ya sata saurin janye nata zuciyarta na wani irin harbawa da sauri.
Dolene ta ɗauka cokalin ganin ya cigaba da tsareta da idanu, gashi duk wannan zaro maganar da yakeyi fuskarsa a ɗinke take kamar yanda ta sanshi. Tsakurar abincin ta farayi. Shima daga haka ya ɗauke kansa ya maida ga cin abincin.
Shine ya fara kammalawa saboda yangar da ita takema cin abincin ko nace kunya, ya cira tissue yana goge bakinsa da faɗin Alhmdllhi. Harta fara murnar zai tashi ya barta sai gani tai ya ɗaura hannunsa akan nata da take cin Irish ɗin da shi ya zare cokalin. Ɗebowa yay ya nufi bakinta yana ambaton “Haaah”.
Itakam yau taga idi, ta ayyana a ranta tana buɗe bakin domin bin umarninsa. Feeding ɗinta ya cigaba dayi har sai da ya tabbatar taci da yawa ta shanye tea ɗin daya haɗa mata rabin cup, dan tun acan gidan ya gama karanceta akan rashin son cin abinci.
Batare da yace mata uffanba ya miƙe ɗauke da wayarsa ya nufi bedroom ɗinta. Da kallo ta bisa tana sauke ɓoyayyun tagwayen ajiyar zuciya. Duk yanda taso tashi ta fara tattare kayan hakan ya gagara harya fito yazo ya wuce hannunsa ɗauke da ɗayar wayarsa, yanzunma baiyi magana ba.
Miƙewa tai ta shiga tattare dining ɗin tana ɗaukar kwanin da sukai amfani dasu takai kitchen. Zaman wankesu tayi, tana kammalawa kamar jira ta jiyo ƙarar door bell. Hannunta ta goge da ɗaukar mayafinta data ajiye ta yafa ta fito daga sashen nata gaba ɗaya zuwa general parlor. Ƙofarma ba wani a rufe yakeba, turawa kawai yayi, amma sai ta buɗe da tunanin ko bamai hurumin shigowa bane sai da izini.
Wani irin ɗan karen daɗine ya tsarga mata saboda ganin Bahijja da Meenal da tawagar su Yaya Gajeje da ƴan ɗan-musa. Suka rungume juna dasu Meenal, sannan ta sakesu ta koma gasu Gwaggo Laritu. har Tinene dake nishi da ƙyar na ciwo dasu Yaya Atine da suka saki baki suna kallon ikon ALLAH. Wai wannan shine gidan Zinneerah? Yarinyar da suke kallo a wulaƙance a ƙasƙance a cikinsu?……
Da wannan tunanin a zukatan mafi yawan ƴan Danya suka shigo ciki, inda anan nefa kallo ya koma sama. Bata barsu anan ba tai sashenta dasu, inda suka zube a falon farko su Meenal na mata magana ƙasa-ƙasa suna waige-waige.
“Madam naji ƙamshin turaren Yayanmu. ko yana ciki ne?”.
Hararsu Zinneerah tayi cikin gatse tace, “Eh kunada matsala da shi ne?”.
“Mu mun isa mu faɗa”. Cewar Bahijja tana sheƙewa da dariya da nufar ɗayan falon cikin sanɗa zata leƙa. Ɗauke hankalinta Zinneerah tai daga garesu ta maida kan ƴan uwanta daketa kalle-kalle kowa da kalar tunaninsa. Har ƙasa ta durƙusa ta gaida Gwaggoninta da yayunta, suka amsa mata suna jera mata addu’ar fatan alkairi da samun zaman lafiya a gidan aurenta. Ita dai bata iya ta amsa a fili ba dan kunya. sai su Meenal ke amsawa. Ita kuma ta kamo hannun Tinene dake kwance a ƙasa tana faɗin, “Tinene lafiya kike kuwa?”.
Da ƙyar tace, “Zazzaɓi nake tunda mukazo”.
“Ya salam amma shine ba’aje asibitiba? Anya Granny ta sani?”.
Meenal ce tace, “Gaskiya babu wanda ya sani, muma sai yanzuma mukeji”.
Sosai Zinneerah ta nuna tausayin ƴar uwar tata tanata faman jera mata sannu-sannu.