MAKAUNIYAR KADDARA 53

       Tana kitchen tana haɗo musu abin sha Bahijja ta kawo mata waya zasuyi magana da Granny. Cike da ɗoki da kewarta ta amsa tana mata sallama a shagwaɓe. Daga can Hajiya iya tai ƴar dariya da faɗin, “Inno na kinfa girma”.
    Sake marairaicewa Zinneerah tayi idanunta na tara ƙwalla tace, “Nidai a’a Granny. Ina kwana”. Hajiya iya na dariya ta amsa mata da tambayar lafiyarsu, sai kuma ta ɗora da tambayar “Baƙi sun sami Moddibo a gidan ko?”.
       Cikin rashin tabbas Zinneerah tace, “Eh, amma dai basuga juna ba”.
     “Oh to ai dama abinda nakeson ji kenan. Ki kira musu shi su gaisa ya sansu su sanshi. Ki nuna masa Gwaggonninki da ƴan uwanki su Gajeje”.
      A ɗan tsorace Zinneerah tace, “Amma Granny……”
       “Amma mi? Inno idan bai sansuba a yanzu yaushe zai sansu? Suma kuma ai ya kamata su sanshi. Banason shashanci maza jeki kira musu shi su gaisa karya fice wannan sarkin sabgogin”.
      A sanyaye tace, “To Granny”.

Dole badan taso ba ta nufi cika umarnin Granny bayan ta kawoma baƙin ruwa da lemon da aka tanada dansu ita da su Bahijja, tana ɗan sissinne kai tacema Gwaggo Laritu “Bara na kira Yayanmu ku gaisa”.
       Cikin fara’a Gwaggo Laritu tace, “Eh to ai haka shine dai-dai, ya kamata muga ɗan namu kar ai shirme shima ya gammu kuma”.
    Ita dai Zinneerah kai kawai ta kaɗa mata, ranta fal fargaba ta fito daga sashen nata, dan ko nashi sashen ba sani tai ba. Tsaye tai a general falo tana ƙarema kowacce kusurwa kallo cike da fargaba. Ita yanzu ina ita ina shigar masa ɗaki banda dai rigimar Granny da bata ƙarewa dan ALLAH?.
       Ƙofar dake facing sashenta ta fara zuwa ta taɓa. jinta a kulle sai zuciyarta ta bata maybe sashen matarsa ne. Ta kalli wadda take a tsakkiyarsu ranta na biya mata nan ne nashi. Mayafinta ta gyara da ƙyau ta nufi ƙofar zuciyarta na rawa na shakku da ganin kamar ta zaƙe. Sai dai tasan bata da mafitar daya wuce bin umarni. Koda ta buɗe ƙofar tana rumtse ido da corridor ta fara cin karo saɓanin nasu da falo ne. Ta ɗan ƙarema corridor ɗin daya sha ado da kallo kafin ta ɗaga ƙafa daƙyar zuwa ƙofar data gani ita kaɗai. Anan kam batai gigin tafiya kai tsaye ba sai tai knocking a hankali kamar mai tsoron a jita. Shiru babu alamar akwai motsin mutum sai ta ƙara da ɗan ƙarfi fiye dana farko. Nanma dai shiru, ta ɗaga hannu zata ƙara na biyu aka buɗe ƙofar. Baya taɗan ja tana mar-mar da idanu.
       Jin ƙamshin turarensa yasata ɗan dubansa zatai magana ya juya ciki da barin mata ƙofar buɗe alamar dai ta shigo. Sai da ta cije leɓe da dafe goshi irin (mutum nan ko) sannan ta bi bayansa.
      Masha ALLAH ta ambata a zuciyarta saboda yin tozali da ni’imtaccen falon nasa dayaji kayan kuɗi. Komai na cikinsa lemon green and milk color ne. Sai ƙamshi ke tashi ga uban sanyin ac da tsigar jikinta har tashi takeyi. Bata da zaɓin daya wuce ƙarasawa inda yake dan tuni ya koma inda ya taso zaune cikin kujera 1seater takardu barbaje a kan centre table ɗin daya maida gab da kujerar alamar aiki yakeyi. Sai dai yanzu ya zauna ne ƙafa ɗaya kan ɗaya yana kallonta harta ƙaraso tana harhaɗewa saboda idanunsa masu kaifi gareta.
       Idanunsa ya ɗan lumshe yana ɗauke kansa daga kanta zuciyarsa na jinjina rashin saurin sabonta, ganin zata kai tsugunne ya sake maido dubansa gareta, “Banason wannan durƙuson zauna a kujera”.
    Bata musa masaba ta zaune a kujerar dake gab da ita. Kanta a ƙasa tace, “Dama baƙine su Gwaggo sukazo, sh…. Shine Granny tace na faɗa maka ku gaisa”.
       Kallon yanda take cuɗa yatsun hannunta dake cikin jan lalle da baƙi kawai yake, ya ɗan ɗauke kansa yana girgizawa. “Taso nan ki sake maimaitawa banjiba”.
       Ɗagowa tai ta ɗan kallesa. Ganin yanda ya ɗauke kai gefe yana ƙoƙarin rage sautin tv ya sata ɗan tura baki, dan ita dai tasan babu yanda za’ai ace ba’a jitaba. Miƙewa tai ta nufesa. Zuwanta gab da shi dai-dai da ajiye remote ɗin hannunsa. jitai kawai ya riƙo mata hannu sai gata a saman cinyarsa.
     Ba firgitaba kaɗan ya rage tayo aman zuciyarta a tafin hannu dan razana da ɗunbin mamakinsa. Ganin yanda ta daburce ya riƙo haɓarta yana juyo da fuskarta saitin tashi, ƙoƙarin ganin sun haɗa ido yake amma taƙi. Sai jikinta dake tsuma. “Maimaita”. Ya faɗa yana ƙara ɗago haɓarta.
      “Granny ce dama tace na kiraka ku gaisa da baƙi”. Ta faɗa da in ina.
     Idanunsa akan laɓɓanta yace, “Inda bataceba fa?”..
Shiru tai dan batasan amsar da zata bashiba. Cikin matso da fuskarsa daf da tata yace, “Uhmyim”.
    Sosai tsigar jikinta ya tashi ta fara marmar da idanu dake neman fara tara ƙwalla.
     “Oh, inada hanyoyin da zaki magantu ai”. Ya faɗa yana sake matso da fuskarsa daf da tatan har hancinsu na gogar na juna. Ba ƙaramin wantsalawa hanjin cikin Zinneerah sukaiba, mamakin Yayan nasu na neman kasheta. A bazata taji saukar laɓɓansa saman nata. Bama tasan ta zazzaro idanuba. da wannan damar ya samu saka nashi idanun cikin nata suna kallon juna. Duk yanda taso ta kauce nata hakan ya gagara sai jikintane ya hau ɓari jin yanda yake sarrafa lips ɗinta cikin bakinsa.
       Tsabar ruɗewa bama tasan ta faɗa jikinsa ta ƙanƙamesaba saboda neman hanyar kuɓuta. Hakan datai ya masa dai-dai shikam, sai kawai ya lumshe idanunsa yana ƙara adanata a jikinsa.
        Sai da ya tabbatar ta ruɗu sannan ya sarara mata. Jin ta ƙubta ta cusa kanta a ƙirjinsa jikinta na wata irin tsuma. rungumeta yayi shima da ƙyau yana murmushi da lumshe idanunsa wani irin kasala na neman saukar masa. Bakinsa ya kai saitin kunnenta muryarsa a ƙasan maƙoshi sosai yace, “A ƙara ne?”.
      Duk da yanda jikinta yay laushi bata san tama zabura ta miƙe ba. Karan farko a rayuwarta dataga yayi murmushi har haƙoransa na bayyana. Baya ta juya masa tana rumtse idanunta itama murmushin na suɓuce mata da sabuwar matsananciyar kunyarsa.
         Batare da ya sake ce mata komaiba ya miƙe shima yana gyara rigarsa data ɗan yamutse saboda zama da tai a cinyarsa. Raɓata yay ya wuce. Sai da yaje fita ya ɗan juyo ya kalleta har yanzu fuskarsa da sauran murmushin ɗazun. Saurin jan mayafinta tai ta rufe fuska…………✍

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button