MAKAUNIYAR KADDARA 54

tsakanin ɓacin rai da farin ciki. Sannan duk son da namiji ke miki kika nuna zaƙewa da yawa akan kishinsa har zargi na zuwa miki a harshe da tunani to
lallai ki tabbata zaki koma 0 a ziciyarsa. Matan yanzu da yawa ba kishin mazansune kaɗai matsalarsu ba, harda zargi. Idan miji ya fita zuciyarki na miki
kaikawo yanacan tare da wasu matan, idan ya shigo gida ya ɗauki waya bazakiyi masa zaton alkairi ba sai kice yana cheating da wasu matan. Idan yana huɗɗa da
mata a ikinsa ko kasuwanci zuciyarki taita kitsa miki karuwansa ne, idan mai yawan sakewa ne da mutane ki zargesa da yawan son mata. To dama kin taɓa ganin
namijin daya rayu babu mace a ransa? Komin tsanani da tsantsenin ki baki isa hana namiji ɗabi’ar son mata ba dan haka ALLAH ya haliccesu, ba kamar ke bace
da akai miki iyaka dakinyi aure shikenan. Daga lokacin da kishi ya sakaki yawan zargin miji koda hankalinsa baya kan matan ma to zai fara nutsuwa wajen
fuskantarsu, daga ƙarshe kodai ya ƙaro auren da kike tsoro, ko ya fara bin matan a waje su halakashi kema ya halakaki, waya janyo?. Ki nutsu ki zama jaruma
ta kowanne fanni, nasan yaƙine ba ƙaramiba amma inhar kinsa kanki zaki iya, koda kina kishin mijinki ki dinga dannewa kinayin mai aji wanda shi kansa zaisa
yaji shakkarki akan wata macen, da kuma shiga damuwar anya ma kina sonsa? Ya dingaji ƙaimi wajen kafa soyayyarsa a gareki dan yaga wannan kishin naki amma
hakan ya gagaresa, sai kiga yafi lalacewa a wajenki fiye da wadda yake hange a wajen. Duk da nasan maza kala-kala ne kuma kowanne da irin nashi salon, ki
nutsu ki karanci nakin, ki daina kuma tilastama kanki sai kin samesa ɗari bisa ɗari yanda kike buƙata. wannan bamai yuwuwa bane a gareki, dan kema baki cika
hundred percent ɗin ba a garesa. Mijinki na sonki Farah, yana kuma miki kawaici darajar mahaigiyarsa da na zuminci, amma kinata ƙara sakaci da damarki,
wadda idan har kikai wasa anzo gaɓar da zaki iya rasashi ma baki ɗaya wlhy, dan Abdul-Mutallab yana tarakine kawai, ina jimiki tsoron randa zai kai ƙarshe a
al’amuranki, duk yanda kike tunanin Hindatu na tsaya miki bazai sauraretaba itama, sai kuma kin fita kwana a ciki dan ita uwa ce babu yanda zai mata.
Aurensa bashi ke nufin ƙarshen rayuwarki yazo ba, yanzune ma ya dace ki zage damtse wajen dawo da kimarki da martabarki a wajensa, inba hakaba kuka yanzu
kika fara dan zaibi ta hanyar ƙara auren nasa ya rama dukkan ƙuntatawar da kike masa ke da Hindatu, hakama danginsa zasuyi amfani da ita wajen ganin sun
rusaku ke da ita ɗin tunda kin shiga makarantarta babu gaira babu dalili, itama ɗin da take hura hanci sun mata laifi banga ta inda sukai matanba balle ke
da kikai taka haye akan abinda bakisan yaya yake ba. Ƙiri-ƙiri tana amfani dake akan wani shashanci nata mara tushe balle makama. Sai ki shiga hankalinki
idan zaki shiga, dan daga ita har Zakiyyar ba hanyar da zata ɓille dake suke ɗauraki ba”.
Tana kaiwa nan ta miƙe ta barta da sharɓar kuka tana nazarin maganar Mahma ɗin dalla-dalla. Dan tabbas sanda bata zama haka ba dukkan kulawa da
tattalin rayuwa Yah Abdul-Mutallab yana batasu, danshi mutum ne mai kawaici, idan kuma ya ɓalle bayajin bari. Yasha nusar da ita illar kai ƙararsa da takeyi
ga Mammah da Aunty Zakiyya amma ta kasa fahimta, dan a ganinta Mammah da Aunty Zakiyyar ne kawai zasu iya saita mata bauɗaɗɗen halinsa na tsiya koda yanaso
ko bayaso. Ashe ba haka bane, sake kangarar masa da zuciya kawai sukeyi da kusantashi da dangin nasa da suka tsana. Itakam ta shiga uku, wlhy bazata iya
zama da wata ɗiya mace a matsayin kishiya ba koda kuwa ƴar waye.
A lokacin da Mahma da Farah ke wannan maganar Zakiyya da Mammah nacan sun kulle kansu a garden suna maganar da suka gagara samun sararin yi tun
ɗazun.
“Mammah inajin tsoro wlhy, anya mutanen nan basu fahimci wani abu daga garemuba suketa ambaton zancen dashen ciki? Gashi munyi sakaci wannan harmutsin
na neman kaimu ga tonon silili, lokaci yayi da Farah zata koma Morocco da zama harta haihu amma hakan ya gagara. Kigafa yanda abokinsa yayi jiya da akace
tanada ciki”.
“Hakane Zakiyya, nima kaina da abin nan na kwana a raina jiya, babban tashin hankalina kuma yaƙin da mukeyi ɗinma baiyi amfaniba, tunda gashi dai
Kabeer na neman cin galaba a kaina tunda sun aura masa wadda suke so ɗin, amma na ɗau alwashin sai Abdul-Mutallab ya saketa wlhy. Babban tashin hankalina a
yanzu zancen yaron nan da Abdul-Mutallab ya haifa da yarinyarnan. Nasanshi sarai akan faɗar gaskiya, da ace ya aikata wani abu a gareta har aka samu cikin
ko zamu kashesa sai ya faɗi yanda akayi, amma ki dubafa yace shima baisan yarinyarba sai a gidansu, kuma ma idan mukai aiki da hankalinmu muma ta ina zai
santa? ita da akace a wani ƙauyen ƙayau take da ko kwalta basu da. Wlhy na rasa ina tunanina zai shiga, yarinyar dai dana san anyima aikin farko a gabanmu
tai ɓari balle muce ko ƙarya tai mana taje ta haihu a wani waje. Kuma bama ita bace wannan dan waccan babbace ma ai, wannan kuwa yarinyace ƙarama fa sweet
17”.
Gumi aunty Zakiyya ta share wani bahagon tunani nason mata kutse a ƙwaƙwalwa, ta haɗiye yawu da ƙyar tana gyara tsaiwa, “Mammah inason ganin ita wannan
yarinyar dan kinsan ni bamma santaba”.
“To Zakiyya miye amfanin ganinta tunda tunda ba wani abu muka haɗa da itaba. Ko akwai wani abu da kike tunani wanda ni ban sanshiba?”.
“A’a wlhy Mammah ”. Tai saurin faɗa tana girgiza kanta da ƙara share gumi.
“To kin gani. ai ganin nata baida amfani dan jira nake yazo gidan ma yanzun nan ya rubuta mata takardar saki ta kama gabanta. A yau kuma nakeson mubar
ƙasarnan da Farah kafin ita kanta Addah da farga da halin da muke ciki, dole kuma mu sake neman wanda zai mana bincike sosai akan yarinyarnan, dan na kula
wancan da yay mana shirme kawai ya tafka yaci kuɗi shegen, dan binciken nasa akan auren Abdul-Mutallab da yarinyar kawai ya tsaya. Ni kuma ta inda
yarinyarnan ta samu ciki nakeson sani, dan ta wannan hanyar ne kawai zamu fahimci inda matsalar ta faro mukumayi maganinta kafin su Kabeer su kaimi ƙasa.
Duk da yaron na tsananin kama da Abdul-Mutallab ban yarda da gwajin da akace an musu ba, gani nake kawai haɗin bakine dasu Kabeer dan a tabbatar da ɗan
nasane a kaini ƙasa wajen aura masa yarinyar da maidosa zama cikinsu”.
Nanma kai kawai Zakiyya ta gyaɗama Mammah dan tunaninta ya fara ƙarfi akan abinda zuciyarta keta mata kai kawo….
AK dake tsaye a ƙofar garden ɗin tun fara maganarsu ya dinga jan ƙafafunsa da sukai masa nauyi da baya-baya zuciyarsa na wani irin harbawa, idan har
lissafinsa da abinda yaji zasu iya zama a muhalli dai-dai kamar akwai lauje cikin naɗi a maganar Mammah da aunty Zakiyya. Dan tun fara maganarsu akan
kunnuwansa suka shiga kaf. Kasancewar a can wajen gate ya ajiye motarsa ya shigo shi kaɗai. Hango a yanda su Mammah suka nufi garden ɗin lokacin da yake