Al-Ajab

Matar da ta haifi tagwaye sau biyu da ‘yan dai-dai sau tara da kuma ‘yan biyar

Wasu mutane a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya sun fara kiran wata mata mai suna Hajara Shu’aibu da cewa ita ce mace mafi haihuwa a kasar saboda yawan ‘ya’yan da ta haifa inda ta haifi ‘yan biyar a baya-bayan nan.

Matar ta haifi tagwaye sau biyu sannan ta haifi dai-dai sau tara sannan kuma a yanzu ta haifi ‘yan biyar, jumulla ‘ya’ya 18 kenan.

A tattaunawarta da BBC kan haihuwar da ta yi ta ‘yan-biyar a karshen nan ta ce babu wani sauyi da ta ji ko tsammanin cewa za ta haifi abin da ya fice da daya.

Ta ce ko awon ciki ba ta taba zuwa ba, haka ta haife su a gida da taimakon ungozoma, inda bayan ta sauka ne sai aka tafi da su babban asibitin Funtua domin a duba lafiyarta da jariran.
Zuwansu asibitin ne ta ce, sai aka kara mata jini aka ce, mata ta samu ta huta, tana mai karin bayani da cewa dukkanin sauran haihuwar da ta yi a baya ba ta taba zuwa asibiti ba a gida ta yi, kuma ba tare da an yi mata tiyata ba.

Hajara wadda ta ce ita matar aure ce da ke zaman gida kawai ba wani aiki ko sana’a da take yi, ta ce ba wani abinci na daban ko wani abu na daban da take yi da ke sa ta haihuwa da yawa irin wannan.

Ta ce, ”Ikon Allah ne kawai, ba wani abu nake ci ba na musamman da ke sa ni haihuwa da yawa.”

Matar
“Yan biyar din da aka haifa

Matar ta yi roko ga gwamnati da sauran jama’a da su taimaka musu kan yadda za su kula da ‘ya’yan.

Sai dai kuma mijin wannan mata wato mahaifin wadannan jarirai Shu’aibu Umar ya gaya wa BBC cewa biyu daga cikin jariran sun rasu washegari bayan haihuwarsu ranar Laraba.

Amma ragowar ukun suna nan da ransu, sai dai an kai su Babban Asibitin Tarayya na Katsina tare da mahaifiyar domin kula da su yadda ya kamata.

Ya ce a babban asibitin na Funtua babu kwalba da za a sa jariran saboda haka ne aka tura su zuwa cibiyar gwamnatin tarayyar ta Katsina inda yanzu suke samun kulawar da suke bukata.

Shu’aibu wanda manomi ne a kauyen Doma na jihar ta Katsina ya ce, ya dauki ‘ya’ya a matsayin wata baiwa da rahama daga Allah.

Amma ba wani abinci na musamman da matarsa take ci ko wani abu da take yi da ke sa tana haihuwa da yawa haka.

Mutumin ya ce shugaban karamar hukumar Faskari a jihar ta Katsina ya taimaka musu da Naira dubu 100, amma har yanzu suna bukatar taimako domin kula da iyalin.

Umar Hussaini wanda shi ne mahaifin Hajara ya ce ya aurar da ‘yar tasa tun shekara 21 da ta gabata.

Ya ce “Shekarar Hajara 35 kuma ta yi aure tun shekara 21 da ta gabata, a dangane da yawan haihuwarta sai in ce wata baiwa ce daga Allah.’’

Da BBC ta tambayi Hajara ko za ta sake haihuwa nan gaba sai ta ce lamarin ba a hannunta yake ba, Allah ne Yake da komai, ‘’Idan Ya kaddara zan sake haihuwa zan haihu.’’

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button