Matar Hariji Page 41-50
Hajiya dake fitowa ta tsaya ta zubawa sarautar Allah ido Muneef ma dake dinning yanayin lunch ya juyo da sauri ya zuba musu ido, ta zame jikinta daga nasa ta matsa gefe saboda ganin Hajiya dake nufosu taja baya itama ta matso gabanta ta janyota da qarfi.
Ta kwada mata mari tace “dama kece farkar wannan mahaukacin? Ashe kece yar tatsitsiya dake kika gama da sangamemen qato irin wannan sai yanda kikayi da zuciyarsa”
Matsawa tayi gabansa kansa yana qasa tace “ka bani mamaki Lameer bantaba tunanin haka daga gareka ba uwarme zaka tsinta a jikin wannan ficiciyar yarinyar da ka kasa samu a gurin matarka har kuke ha’intarta ka watsar da haqqoqinta akan wannan aljanar yarinyar?”
Dagowa yayi da sauri gabansa na faduwa saboda yanda Jiddoh ta maqalqalesa tana wani mugun kuka saboda sosai marin na Hajiya ya shigeta kamar yanda shima yaji marin a qasan qahon zuciyarsa yace.
“Amma Hajiya meye Hauwah tayi miki daga shigowarta cikin family dinmu a fara yimata wannan tarbar Hajiya matatace fah kuma sonta nakeyi na biya sadaki na aureta iyayenta suka dauketa basaso suka bani ita ta amince kuma zatayi rayuwa dani duk da kasancewar iyayenta sun sallamamin ita, meye yasa Hajiya zakiyimin haka meye yasa ni baki taba tayani so da tattalin abinda nakeso ba?”
“Matsawa tayi gabansa ta sanya hannu ta shaqosa tace “kutmar ubanka ne yasa bazan tayaka sonta ba Lameer nace durun uwarka, ni zaka titsiye kace sai na fada maka meye yasa banason abinda kakeso to bari kaji in fada maka ba Hauwah ba ko makka ce banasonta bakuma zan taba sonta ba aurene kayi hankalinka Dana ubanka ya kwanta ka nunamin ban isa dakai ba, to naji kaje ka zauna da matarka amma kashedi kuma umarni daga yau idan ka qara dauko kucaka baqauyiyar bagidajiyar yarinyar nan ka kawomin gdan sai nayi maka abinda baka taba tunaniba.
Tunda ta fara mgnr Hauwah ta qara shigewa jikinsa ta lafe jikinta na rawa tana kuka me gunji tunda take a rayuwarta bata taba ganin abinda ya tsoratata kamar Hajiyan Lameer ba yanda ta haqiqance tana fada yafi komai ruguza lissafinta.
Numfashi yaja me huci yace “kiyi hq…..” Duka takaiwa bakinsa Jiddoh ta sake maqaleshi tana kuka rawar jikinta na qaruwa tace “nikam banason wannan masifaffiyar matar Ingarido ce ka fice dani daga gdannan wlh bani qara zuwa…”
Ranqwashi Hajiya takai Mata tace “tsohuwa ta ruga me tallan nono da fura itace Ingarido bani ba Koda yake kicemin abinda yafi Ingarido ma ba laifinki bane laifin wannan sabitu sallamammen ne shegiya yar gadon saida fura nikam duk yanda akayi ku mayune shiyasa daga siyan nono kika lashen kurwar Dana”.
Ganin haukan na Hajiya babbane yasashi janye Hauwah da baya da baya zasu fice Muneef ya taso yace “haba Hajiya meye hakan wannan ai ba girmanki bane ki tsaya kina fadar maganganu irin wannan a gaban surukarki matar danki meye laifin Yaya don ya farantawa zuciyarsa ya auro farin cikinsa wlh nikam ya burgeni 100%….”
Hannu ta daga masa tace “kauce ka bani guri auta ko inci ubanka to ko Abulle yayarku da taji wannan gamin gambizar auren na shashashannan saida ta sallame daga sallar magrib waccan shashashar Zaliha yar uwar dayan itace kawai harda murna to dakai da ita dashi da ita wannan bagidajiyar wlh tallahi uban maqerin babanku zanci nidai wannan mugun irin baiyimin ba inda na shukane ma bazan siya nakai gonataba”
Yanda zuciyarsa ke tafasa da kukan Jiddoh din idan ya tsaya zai iya fadawa uwartasa maganar da zata jefashi cikin fushin ubangiji saboda haka ya figi hannun matarsa tana kuka tana komai ya jefata a mota yayiwa motar key ya fice daga gdan a guje.
Gidansa ya nufa zuciyarsa a tafashe yana tuqin zuciyarsa na qara kumbura kukan nata shi yafi komai dukan zuciyarsa baisan sanda yaci wani uban birki ba yace “Hauwah ya isa hakaaaa” yanda yayi mgnr da qaraji yasata saurin hadiye kukan taja wata qaqqarfar ajiyar zuciya.
Sake taka motar yayi ya shiga unguwar ya taka burki yayi horn me gadin yazo ya bude masa ya shiga yayi parking ya kifa kansa a saman sitiyarin yace “innanillahi wa innah ilaihirraji’un Hauwah idan baki daina kukannan ba zaki tarwatsamin zuciya mu shiga kiyimin wani hukuncin banda wannan”
Dagowa tayi idonta sharkaf da hawaye tace “inane nan din Kad…” Rufe Mata baki yayi yace “gdanki ne nan ne gidana da iyalina anan zaki zauna kafin mu tafi Lagos amma banason sunan nan daga yau kidaina cemin Kado sunana Muhammad Lameer” rufe idonta tayi tace “shabdi rahin kunya kenan mu a Rugarmu baa fadar sunan babba” murmushi yayi yace “to kawai ki rinqa cemin babe kinji” batare data damu da abinda hakan yake nufi ba ta fara maimata “babi babe bebe bebi” dariya sosai tasashi wato ita a gurinta komai har ya wucce ta samu abin maimaitawa “babi babe bebe bebi tana nufin duka da haka zatake kirana nikam naga ta kaina” ya fada a ransa tare da bude motar…………
A fusace ya juya zai fita ta kamo kwalar rigarsa ta baya tace “wlh bazaka fita ba saika fadamin matsayina a gurinka nagaji da wannan rayuwar quncin dakai Lameer kai banji dadi dakai ta fanni mu’amala ta aure ba kai banji dadin zama dakai ta fannin rayuwa ba kai bansamu lkcnka ba wannan wanne irin jahilin aure ne mara ma’ana da rashi albarka ta baibayeshi ta ko ina Lameer na tsaneka na tsani jininka na tsani zama dakai na tsani komai naka ka rabu dani don Allah Lameer nidai nace ka sakeni kazauna da kucakar matarka”
Murmushi yayi Mata tare da dago kanta yace “saurin me kikeyi mmn Fadwah kin dade kina roqona saki naqi yi mikishi saboda abubuwa biyu da nake dubawa amma kidan qara hqr indai zakici gaba da fadamin duk abinda yazo bakinki to inayi miki albishir da saura qiris”
Yana fadin haka ya juya ya fice da sauri ya nufi kitchen ya dauki duk abinda yasan zai buqata ya fita ya koma part din Jiddoh ya shiga ya tarar da ita a tsaye tanata kalle kallenta ya shiga kitchen din tabishi ta tsaya tana kallon yanda yake hada komai.
Taliya ce ya dafa musu sai tomato soup da taji bushasshen kifi sai qamshi yakeyi ya zuba musu a flat daya ya dauka abin na arziqi ne suka fito ya jata dinning suka zauna ya dauki cokali ya juya ya debi yakai Mata bakinta ta kawar dakai ta wanke hannunta tasa ta juya ta diba takai bakinta.
Lumshe ido tayi tana tauna abincin a hankali yana kallonta harta hadiye na bakinga ta bude idonta taga ya diba a cokali zaikai bakinsa tayi saurin riqe cokalin ta janye flat din ta tashi ta sauka qasa ta juya masa baya.
Ajiye cokalin yayi ya zubawa sarautar Allah ido abincin da yawa amma ko a jikinta ta rinqa cin abinta tana kadakai, tashi yayi ya matsa gurinta yace “bazaki iya cinyewa ba ki bani na tayaki” wani mugun kallo ta watsa masa ta tureshi tace “aa mugunta zakayimin ka cinye nikam ka qyaleni wannan qaton bakin naka mugun lauma zaiyi.
Damuwarsa yaji ta gushe gabadaya yayi dariya yace “is ok amma wlh sai kin cinyeshi tas kin yarda?” Daga masa kai tayi taci gaba dacin abincinta, ya miqe ya shiga kitchen din ya zubo wani ya zauna a dinning din yanaci yana kallonta.
Cikinta fah ya cika gashi ko rabin abincin bataci ba abinka dame qaramin tanki, juyowa tayi ta kalleshi ya daure girar sama data qasa babu alamun Wasa fuskarsa yanacin abincinsa a nutse yana danna wayarsa, sakeyin qasa tayi da kanta tana cakalar abincin shikuma yana satar kallonta, idan taci abinda zata iya saita dago ta kalleshi.
Hardai tagaji ta dago tace “Kado na qosh…..” Hannunsa ya daura a bakinsa yace “sheeeeeet!” Sannan ya miqe ya dauki lemo da ruwa ya tsiyaya a cup ya tsugunna gabanta yakai Mata bakinta ta karba tasha sannan ya sake tura nata abincin yace.
“Alqawari mukayi dake zaki cinye saboda haka saikin cinyeshi tass” ai baigama rufe bakinsa ba sai hawaye sharrrr ya miqe ya koma ya zauna saman stool din dinning din yace “oya kiyi ki cinye kiyi wanka zanje masallaci na dawo an fara kiran magrib” miqewa yayi ya shiga daki ta kuma tusa abincin a gaba.
Turawa takeyi tana kuka cikinta kamar zai fashe har wani yunqurin amai takeyi tanata jan zuciya, fitowa yayi da sauri baiko kalli inda take a yana daura agogo yace “idan na dawo naga baki cinye abincin nan ba sainayi gunduwa gunduwa da sassan jikinki”
Wawuyarku takuwa sake rushewa da kuka dataji yace zaiyi gunduwa gunduwa da ita har tana auna gabobinta yau tasan idan bata cinye abincin nan ba dafgenta zasuyi, Kai abu tun kamar zai yuwu harta kai qarshe kawai ta tusa abincin a gaba ta hade kai da gwiwa ta kurma uban ihu.
Daidai lkcn da yake haurowa saman ya qaraso da sauri ganin yanda ta riqe ciki tana kuka wiwi yasashi komawa ya zauna yace “me kikeyiwa ihun bayan kince zaki iya cinyewa?” Cikin shassheqar kuka tace “Qur’anin Allah na dauka abincin kadanne ashe dayawa kuma ai kaine mugu ka zubo da yawa”
Wata cafka yayiwa gashinta yace “nine mugu?” Kuka ta rushe dashi tace “eh mana mugun mugaye na saicin alhakina kakeyi ka tsotsemin Inninina kayimin wanka sannan kasani na cinye abincin da kasan yafi qarfina wlh sai munyi hisabi a lahira kai gidansu Ingarido zaa kaika idan ka mutu nikuwa gidansu Hamana”????
Dariya ce tasashi qarasa zama yace “waye Hamana?” Shiru tayi tace “wazirin Fir’aunu ne kuma babban babbansu a gidansu???? Murmushi yayi yace “kintaba zuwa islamiyya?” Turo baki tayi tace “Modibbo Gambaje yana koya mana idan ya dawo daga rani”
Murmushi yayi yace “makaranta hudu zansaki ta islamiyya data boko zan dauko masu koya miki a gida sannan ta koyon girki zan kaiki Catherine school sai ta koyan kwalliya da zama da miji” numfashi ta sauke tace “nidai bazani b…” Rufe mata baki yayi yace “aikuwa sai kinje karma ki qara cewa bazaki ba banason musu”
Shiru tayi tana riqe cikinta tace “wayyohh cikina” da sauri ya dagota yace “meyene kuma?” Kuka tasa masa tace “kaga kasani naci wannan taliyar yar leda kuma…..” Rufe bakin tayi taqara riqe cikin tana kuka yace “dallah kiyi mgn mene?” Kuka ta Kuma rushewa dashi ta kwanta a jikinsa tace “kashi nakeji kuma babu jejin da zan zagaya a kusa yanzu yaya zanyi”????
___________????Riqota yayi jikinsa suka nufi qofar shiga gidan ya bude ya shiga da sallamarsa Mubaraka dake fitowa daga kitchen ta dago domin amsa sallamar ai batasan sanda ta saki flat din hannunta ba saboda tsananin firgici da mamaki.
Janye Hauwah yayi a jikinsa ya zaunar da ita saman daya cikin kujerun falon yace “sannu da gda uwargida sarautar Mata ya kadaici” bata iya amsawa ba saboda wani yawu me daci data hadiye daqyar ta matso gabansa cikin macewar gabobi tace “Lameer wacece wannan”
Tayi maganar tana kallon Jiddoh wadda itama ita take kallo qurrr tanata zuba santi a ranta na kyawun Mubaraka tayi ajiyar numfashi a ranta tana fadin “dama nice”
Miqewa yayi yana cewa “qanwarki ce Ina fatan Isa ya gyara wannan bangaren?”
Bata iya cewa dashi qala ba saboda wani baqin ciki da yake turnuqar zuciyarta yaja hannun Hauwah domin su hau saman Amma sai ta noqe tace “tabdi salon naje na taka na fado nikam ka barni anan”
Itadai bazata rabu da abin mgn ba ya fada yana figar hannunta da qarfi ta fada jikinsa ya dagata cak tana ihu ya haura saman ya direta a tsakiyar parlourn yayi shigewarsa daki.
Tsayawa tayi tana kallon gurin ta zube a gurin tana kallon kowacce kusurwa ta falon cike tsoro da mamaki komai juya Mata yakeyi saboda ko a mafarki bata taba tunanin tsintar kanta a irin wannan gurin ba.
Miqewa tayi tana latsa kujerun tana dariya tana cewa “laha’ilallah Kado zo zokaji wlh wanan gumakan na gurin nan duk laushine dasu kamar jikinka”
Fitowa yayi ya tsaya jikin qofar ya zuba Mata ido yana kallon inda taken komai na parlourn tana shafawa tana dariya
Murmushi yayi ya matsa ya sha gabanta ta dago ta kalleshi ta nuna masa standard A.C dake tsaye a kusurwar hagu ta parlourn tace “wannan kuma meyene Dana taba naji yanata kwararar da sanyi?”
Ajiyar numfashi yayi yajata suka zauna yace “A.C ce” kallonsa tayi tace “tohhh sunanshi kenan ic meyesa bana ganinsa a rugarmu?” Dariya yayi yace “ai bakuda wutar lantarki shiyasa baki ganinsa a rugarku yarinya”
“Miqewa tayi tace “aa Kado in zaayi wasa ai wasa banda tsikarin uwar miji da tabarya kada ka qara cemin yarinya danni ba yarinya bace na fada maka…”
Bata ida fadin abinda ke bakinta ba taji yayi sama da ita bai direta ko inaba sai kitchen din dake cikin parlourn saman yace “shirmenki yayi yawa Hauwah yunwa nakeji me zamuci?” Turo baki tayi tace “nan kuma dakin wayene?” Janyota yayi jikinsa yace “kitchen ne anan akeyin girkin duk abinda zaaci”
Dariya tayi sosai tace “amma Kado kai dan rainin hankali ne yanzu nan duk jeran nan kana nufin madafi ne to inma banda ka rainani Ina zaa girka murhu?”
Haɗiye dariyarsa yayi yace “aiga murhun nan zo kiga inda ake kunnawa” matsawa tayi ya dauki abin kunna gass ya danna ta saki qara tare da cewa “wayyohh kunne na wayyohh zai qonani!” dariya sosai yace “zo kiyi mana girkin abinda zamuci yunwa nakeji”
Turo baki tayi tace “chabdi nidai aa bazan iya girki ba ni ko kunu ban taba damawa ba balle wannan jagwalgwalon naku na yan birni” murmushi yayi ya dauko tukunya sabuwa dal a cikin kitchen cabinet ya zuba ruwa ya dora ya goge hannunsa ya jata suka fito yace.
“Zauna Ina zuwa” baijira cewarta ba ya nufi downstairs din ya sauka ya nufi matattakalar da zata kaishi part din Mubaraka ya haura ya tarar da ita a tsaye da waya a hannunta tana yafa mayafi yace “ina Zaki?” Cikin kallo irin na tsantsar tuhuma tace.
“Zanje na tambayi tsohuwarka ne da saninta ka kawomin wannan kucakar karuwar taka gidana har kayi Mata bangare a cikinsa ka shige daki da ita sama da awa guda” Murmushinsa ya fadada yace
“Abinne yazo a bazata wlh shiyasa ban sanar dake ba kiyi hqr nasan nayi miki laifi duk da qila kinsamu lbrn dama Ina neman aure, Mmn Fadwah wannan yarinyar da kike gani matatace ta sunnah da aure yabani matsayinku daya a gurina babu wacce tafi wata sai wacce tafi kwantarmin da hankali”
Numfashi yaja yaci gaba da cewa “Mubaraka Hauwah yarinya ce qarama qanwar bayanki ta qarshe gaba daya bazata wucce saar Zainab qanwarki ta hudu ba, haka Allah ya nufa kuma ya qaddara batasan komai ba dani dake mune zamu sanar da ita idan mukayi Mata mugun karatu dashi zata tashi idan muka bata sahihin karatu da babu mugunta ko sonkai a cikinsa to shine zaita zagawa tsakaninmu alkhairi zai wanzu cikin zamantakewarmu ya bamu kyakkyawar alaqa da fahimtar juna wanda hakan zaiyi tasirin bibiyarmu har qarshen rayuwarmu…..”
Daga masa hannu tayi tace “kayyy dakata munafukin Allah ta’ala kana nufin wadannan matsiyatan kalaman naka sune zasuyi tasiri a kaina? Hmmm wai qanwa wlh kayi tsararo Allah ya kiyasheni tabewa yin qanwa da wannan bagidajiyar yarinyar kaidai daka kwaso ta kware maka can Amma badani ba”
Yanda take mgnr tana nufoshi kamar zata dakeshi yasashi sakin baki yana kallon ikon Allah har ta iso gabanshi tace “wannan itace sakayyar halaccin da nayi maka ko Lameer kaje ka ajiye karuwa a Lagos sannan ka tashi dawowa ka dawomin da kishiya kishiyar ma wannan qazamar kucakar yarinyar da bazata taba wayewa ba a rayuwarta, to wlh saidai ka zaba koni ko ita nikam bazan taba zama da ita a matsayin kishiya ba Wai muna amsa suna daya gurin mijinmu.
Ka cuceni a abubuwa da yawa Lameer baka damu da saukemin haqqina ba wata da watanni kana qwarata kana barina da damuwar da banida me yimin maganinta saikai sannan yanzu ace kayi aure wannan ma ai cin fuskane da wulaqanci da wanne kuzarin zaka riqemu mu biyu har ka biyawa kowa buqatarta?”
Shafa sumarsa yayi yace “duk wannan ba damuwarki bace abinda ya shafeki kuma haqqi a gareki shine na sanar dake matsayin Hauwah a gurina kuma na sanar dake ruwa nane na kusanceta kullum ruwa nane na shekara ban kusanceta ba kamar yanda nakeyi miki wannan ba matsalarka bace, amma dai ki sani kuma kisa a ranki aurena da Hauwah yin Allah ne kuma ya qullu babu wanda ya Isa ya hanashi kamar yanda mahaifinta da danginta suka qi kuma suka qyale akayishi yaka duk wani dan baqin ciki zaiyi quncinsa ya qyalemu, idan kuma mutum yana ganin bazai iya hqra ba to ya hadiyi zuciya ya mutu kowa ya huta”
Wani mugun tashin hankali ta tsinci kanta a ciki da bata taba tunanin Lameer zai sata a ciki ba tunda sukayi aure tsayin shekara uku baitaba daga muryarsa sama da tata ba sai akan wata mace macen ma wannan qazamar kucakar bafulatanar dako yar cikinsa inda yayi auren wuri batakai ba, lallai da aiki ja a gabanta dole ta tashi hankalinsa dana zuri’arsa, babban tashin hankalinta yanzu cikin da take dauke dashi na watanni biyu wanda a lissafe idan zaiyi lissafi watansu hudu rabon da wani harka ta auratayya ta shiga tsakaninsu sai kwanaki takwas daya wucce ranar da tayi masa tujarar nan, yanzu ta yaya zata fara liqa masa cikin kamar yanda ta liqa masa na Fadwah?..……………
Miqewa yayi yace “kewai komai ma baki iya ba bakiga toilet a bathroom ba dazu da kikayi wanka zakicemin wani kashi kikeji” sakeyin raurau da ido tayi tace “ni wlh banga juji ba” ya lura itafa komai bata ganewa sai anyi mata gwari gwari hakan yasa ya kama hannunta suka shiga bandakin ya bude seet toilet din yace “ga gurinda akeyin kashi nan idan kika gama sai ki murda wannan ki zaro tissues ki goge saiki sake danna nan ruwa zai zubo saikisa sabulu ki wanke idan kin gama kuma ki danna nan zakiga ruwa yazo yayi flurshing”
Fita yayi yabarta a tsaye tana leqen cikin toilet din tana kallon ruwan ciki gare gare tace “to aini dazu a wannan randar na debi ruwan alwala”????
Har yaja qofar yace “ehh!” Tare da zaro ido yace “kika debi ruwan alwala anan?” Daga masa kai tayi tace “eh aradun Allah kuma ruwan dumine dashi danasashi a bakina har wani zaqi yakeyi” ai baisan sanda yayi qasa ba yace “kinsha fitsarina Hauwah kewai wacce irin shashashar yarinya ce bakiga inda nayi tawa alwalar ba” turo baki tayi tace “toni Ina ruwana bakaine kace nazo nayi alwala ba”
Takaici ne yasashi miqewa ya fice daga toilet din ita kuma tahau kan masan, memakon ta zauna aa saita tsuguna akai qafafunta nakan gurin zaman idan tayi kashin ya fada tsulum saita qyalqyale da dariya tace “danwake daya ya fada” haka harta gama tayi duk yanda yace.
Ta wanke hannunta ta fito baya cikin dakin hakan ya bata damar yin sallar magrib da Isha ta kwanta a qasan.
Ya turo qofar ya shigo ya hangeta a qasa ya matsa da sauri ya dagota yace “kekam baki gudun mgn kin mayi wanka kuwa?”
Kada masa Kai tayi ya dagata yace “ok muje kiyi wankan mu kwanta gobe litinin jirgin asuba zamu bi mu wucce Lagos” itadai batace masa komai ba ya dagota suka shiga bathroom din to yanzun ma a bataso tana zillewa shine yayi mata wanka ya fito da ita shima yayi suka kwanta bayqn yayi musu addu’a.
Kiran sallar farko akan kunnensa ya tashi yayi wanka ya tasheta ya fito Mata da wata doguwar rigar atamfa cikin kayan da ya bayar tunkan yatafi a dinka mata yasata ta sanya ya bata mayafi da takalmi da jaka ya koma yana kallonta tayi masifar kyau kamar ba itaba.
Murmushi yayi yace “dama kada kiyi shirmenki ki nuna kanki idan mun tafi banason qauyancinki ki ajiyeshi anan idan mun dawo kya dauka ki saka kinajina ko? Daga masa kai tayi ya fita ya hado musu tea ya bata tasha daqyar kasancewar asubace biyar ma bata qarasaba ya kama hannunta su fito zuwa qasan.
Ya saki hannunta yace “ki jirani anan bari nayiwa yar uwarki sallama” batace qala ba ta nemi guri ta zauna shikuma ya haura saman ya kwankwasa dakin Mubaraka, ta miqe zumbur shima farkan nata ya miqe tace “mun shiga uku gashinan wlh shine bugun qofarsa ne”
Cikin kadawar ciki Muneef yace “yanzu ya zamuyi” kafin tabashi amsa ya tashi ya shige bayan manyan labulen ta qasa ya kwanta luf, ta sauke ajiyar zuciya ta bude masa qofar tana miqa ya shigo dakin yana rarraba ido yace “na tasheki ko? Zamu wucce Lagos shiyasa nayi miki transfer kudi a account dinki nasan zasu isheki duk da ba dadewa zamuyi ba”
Kallonsa takeyi sake da baki kafin tayi mgn ya juya yace “Ina Fadwah ne ko tana gdan Hajiya” nan ma bata bashi amsa ba ya sauka yace da Jiddoh taso mu tafi kinga har rana ta fara fitowa”
Suna fita drivensa yaja suka tafi yakaisu airport to dayake yayi mata federal warning yadan samu sauqin shirmenta kuma dadin dadawa taga babu fuska hakanan duk da tsoron da take ciki na hawa jirgin ta haqura saidai qanqameshi da tayi jirgin ya tashi ita kuma ta kama bacci a jikinsa.
Lkcn da suka isa Lagos din tanata sharar baccinta ya sabata a kafadarsa har mota yasata a ciki suka nufi Quarters din tasu saida driven ya shiga har ciki sannan ya tsaya a daidai qofar bangarensa ya bude ya fito itama ta tashi yace ta fito ta fito suka shiga ciki.
Wayyohhhh Allah nan Hauwah taga qarshen haduwa bawai fin sauran gidajen da tashiga kayan qawa yayi ba aa saidai kawai yafisu tsaruwa ga wasu manyan hotunansa guda biyu da yayiwa parlourn ado dasu sai nata Suma guda biyu daya dauketa wata rana a bakin qoramar da suke zama suna fira farkon haduwarsu.
An wanke hoton ya fito sosai kamar a kirata ta amsa, kallonsa tayi shima ita yake kallo yayi murmushi yace “kina mamaki ne?” Daga masa kai tayi ya fadada fara’arsa ya matso gabanta ya dago fuskarta ya sauke Mata lebbansa biyu yace “to ki daina yanzu wasan zai fara, yanzu zamu fara sabuwar rayuwa dagani saike, ki dauka bakida kowa sanin nima zan dauka banida kowa sai ke kadai”