Uncategorized

MATAR UBA 11

????????????????????????????????          *MATAR UBA* 

????????????????????????????????

       _(A True Life Story_ )

            *Short story* 

 “`Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)“` 

Follow me on Wattpad @milhaat

Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0

???? *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* ????????️

 _(‘Kungiya d’aya tamkar da dubu)_ _____________________________

*MATAR UBA*  Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.

Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK*  much Love.

NOT EDITED

CHAPTER 11

????????????????????????????????????????

“Yanzu tashi Muje mu Sanarwa Ammi kina Nan Kinga Bata San kin shigo ba ko? ”

Ba musu suka fita, Ammi na ganin Asiyah tayi mamakin ganin ta baking bud’e Tace “Asiya kece da Daren Nan lafiya kuwa?”

Tab’e baki shamsiyya tayi Tace “Ammi Nan ma Baki gan ta sanda ta shigo ba a haukace” Nan ta jero Mata komai kamar yanda Asiyah ta fad’a Mata, kad’a Kai Mama tayi Tace “Baraka baza ta tab’a canzawa ba Kenan,Toh Allah ya kyauta, kuje kice ki bata abinci taci ku samu ku kwanta” tana kaina ta tashi ta shige d’akin ta.

????????????????????????????????????????????

WASHE GARI

Da Sallama ta Shiga makeken parlor jikin a Sanyaye, cikin sauri ta Fara haurawa sama, cikin tsawa ta ji ance “And where do you think you are going?”

Baraka na gani a tsaye tana bubbuga kafa had’e dayi Mata wani irin muguwar kallo,jiki a Sanyaye ta Fara saukowa daka stairs, da gwiwowinta ta zube kasa, tana kokarin b’oye hawayen da ya gangaro Mata, cikin Rawar murya Tace “Mummy ina kwana”

Wata gigiticiyar maruka ta shafa Mata sannan Tace ” Yar iska karuwar banza daga ina kike?”

Cikin kuka Mai cin Rai Tace ” Mummy gidan su shamsiyya nake”

“Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un, Asiyah Ashe haka Kika kware gun karya ki dubi tsabar idona kice min gidan su shamsiyya Kika kwana?” Tana maganar tana yarfa hannu.

” Wallahi daga chan nake Ni ba Yar iska bace”

Tab’e baki tayi Tace ” Chan Miki matsalar kice ba tawa ba,tashi ki bani wuri ko yanzun Nan na Tara Miki na jaki”

Cikin sauri ta haura sama,tana Shiga d’akin ta ta sauke ajiyar zuciya, a bakin kofa ta zauna ta had’a Kai da gwiwa kuka take sosai Wanda hakan yasa idanun ta sukayi jajir jiyoyin kanta suka you rad’a rad’a, sai da tayi kuka Mai isarta ta Fad’a toilet tati wanka sannan ta d’auro alwala, bayan ta idar da sallar walha, ta d’auko kayan ta masu datti da niyar wankewa, backyard na gidan ta nufa ta Fara wankin kayan ta, zuciyar ta faal bakin Ciki duk duniyar taji ta daina Mata Dadi a fili Tace “Dama ace ni matattiyace, Ina ma ace nice ba mutu ba ku ba” ta karasa maganar tana kuka tasa hannu ta sharce majinan hancin ta.

Ba ta ankare ba sai gani tayi an waso mata Kaya masu uban yawa a razane ta mike ga mamakin ta Safiyya ce tsaye a gaban ta tana wurga Mata harara tsaki taja sannan Tace “Malama ki bar wanke kayan Nan da kike ki wanke min nawa yanzun Nan”

Murmushin takaici tayi sannan Tace ” Safiyya nice zan Miki wanki” tana maganar tana nuna kanta, “eh ke Zaki wanke ko ban Kai na saki bane?”

“Lallai Safiyya wuyanki yayi kauri,ko ba komai ina gaba dake Amma kike min magana kamar wata sa’ar ki?”

” An Miki din Kuma dolen uwarki ki wanke”

” Uwata?”

Cikin sauri Asiyah ta shige cikin fidan tana Kiran sunan Mummy, cikin sauri ta fito “lafiya me ta Faru kike min irin wannan kiran haka?”

” Mummy Zo ki gani”

Cikin Rashin fahimta ta bi bayan Asiyah, Asiyah Tace “Mummy jinga abinda tayi Wai nice zan Mata wanki bayan nace Mata nice gaba da ita ta nemi ta zage Ni”

Yarfa hannu ta Shiga yi sannan Tace ” Amma Asiyah kinyi mugun Raina Ni, yanzu ke don uwarki Kiran da Kika min Kenan, to me a Ciki don tace ki Mata wanki?”

” Mummy wanki fa wa Safiyya kanwatace Amma Kuma na Mata a gani na hakan Bai dace ba”

A tsawace Tace ” Would you shut up your dirty mouth, ki wanke su sannan ki tabbatar sunfita idan Naga Basu fita ba sai kin sake wanke su, bayan haka Kuma ki goge Mata su, wuwuyar banza idan Kika sake min haka wallahi zan Miki illa”

Ta Maida kallon ta ga Safiyya ta ce ” Ke Kuma ki wuce d’aki weather da zafi kije ki Sha sanyin AC”

Murmushi tayi Tace “Toh mummy” tare suka shige suka barta a gun zubewa tayi a kasa duk damuwar duniya ta hadu ta Mata yawa, kukan ma yanzu kasa yin shi tayi, a ranar wunu tayi tana wanki bayan sun bushe ta goge su, sai daff da la’asar ta gama , d’akin ta tashiga tayi wanka 

Sannan tayi alwala, bayan ta fito ta saka jallabiyar da take sallah dashi ta shimfida prayer mat ‘yar karamar tsaki ta jaa sannan Tace “An sa mutum zaiyi tarikussalat” tana idar da sallah Bata tsaya shafa Mai ba ta zurma uniform d’in islamiyar ta, d’akin Baraka ta nufa tayi Sallama Amma taji Shiru, a fili Tace maybe suna garden, cikin nitsuwa take tafiya harta Isa garden d’in sannan ne ta lura motar Baraka Bata Nan hakan ya tabbatar Mata da Bata gidan, “Safiyya idan Mummy ta dawo kice Mata naje islamiya”

Shiru Bata tanka Mata ba,ta sake Mata magana a Karo na biyu, Bata tanka ba, tab’e Baki tayi ta nufi gate, Cikin gadara da izza safiyya ta kwala Mata Kira “Asiyah!!!” 

A nitse Asiyah ta waigo, hannu ta d’aga Maya alamun kizo, har ta juya zata tafi sai Kuma ta dawo da baya, “Gani lafiya?”

Sai da ta d’auki tsawon mintuna biyu tana tsaye Kan Safiyya Tace “Jinga wanchan” tana nuna Mata ledan pure water guda biyu sai tray na silver, da ido tabi hannun ta sannan ta Maida kallon ta gareta Tace “Eh ba gani ya akayi”

“Mummy Tace na Fad’a Miki ki d’auka kije ki sayar sannan idan baki sayar ba Kar ki dawo gidan Nan”

” Islamiyar da?”

” Oho chan Miki, idan Zaki Koma kije ki cire uniform d’in da zai fi Miki kizo ki d’auka Kiyi yanda Tace”

Shiru tayi na ‘dan wasu lukata sanan ta hura iska Mai zafi sannan ta shige cikin gida, Safiyya kuwa tabi bayanta da kallo sannan ta kwashe da dariya, “Yarinya Baki ga komai ba, Wanda mummy take Miki nafila ne Akan Wanda Ni zan Miki, Mummy da Bata San da maganar pure wata ba”

Bata dad’e ba ta fito jikinta sanye yake da Pakistan dress green an mishi kwalliya da flowers jaa, da gyallen kayan tayi rolling sannnan ta d’auka ta fita, Mai gadi tausayin ta yaji sosai ganin yanda kamar Abubuwan da suke Mata bai dameta ba, ya Mata fatan Allah ya tsare ta amsa da ameen.

Tasha ta nufa don ta tabbata zaiyi saurin karewa hakan kuwa akayi Bata d’auki awa d’aya ba ta sayar dashi Tass, ta nufi hanyar gida sai da ta shigo estate dinsu ta nemi inuwar wata bishiya ta zauna tana huta gajiyan da tayi don ta tabbata in ta Koma ba barin ta za’a yi ta huta ba.

********

Motar Hashim na gani yana tukin Yana dube dube ko Allah zaisa ya ga wucewar ta don ya tabbata zuwa yanzu an tashi daga islamiya, parking a gefen titi kansa ya d’aura a Kan steering motan, da zaran ya rufe idon say ita ce take Masa gizo kullum cikin tunanin ta yake baida aiki sai tunaninta yayin da wutar so da kaunar ta yake Kara kururuwa a birnin zuciyar sa, hannu yasa a aljihunsa ya Ciro d’ankwalin ta da Bari ya sa a fuskan sa ya d’auki tsawon lokaci a haka, ganin basa ta Zo ba ya jaa taking ya kalli gefen motar sa, har ya tada motar sai Kuma yayi saurin kallon gidin bishiyar dake gefen motar sa, zaro idon sa yayi don ganin ita dince ko gizo ta ke masa, Murmushi yayi had’e da dariya Wanda baisan sanda yayi ba, da sauri ya bud’e kofar motar ya fito, ya dad’e a tsaye a kanta  ganin kamar kuka take yasa yayi sauri ya sunkuya yace “Kuka?”

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button