MATAR UBA 11

A razane ta d’ago Kai ta kalle shi, ganinsa yasa ta d’an jaa da baya,cikin tashin hankali yace “Meyasa kike kuka? Me aka Miki?”
Tashi tayi da niyar barin gun yayi saurin fad’in “Dan Allah ki saurare Ni, yau shine Karo na uku ina neman magana dake Amma kin hanani Dan Allah kinda shine zai Zama taimako na karshe da zan nema a gunki ki saurare Ni”
Shiru tayi a zuciyar ta Tace ” Asiyah ki saurare Shi kiji da me yazo Miki, ko h
Ba komai ya ceci rayurwar ki a gun Yan iskan Nan, da Allah ne kad’ai yasan abinda zasu Miki”
Kai a kasa tana Wasa da hannun ta Tace “Ina sauraron ka”
Murmushin samun nasara yayi yace “Daga farko dai Ni suna na Hashim,ko zan iya sanin sunan ki?”
Chan Ciki ta amsa ” Suna Na Asiyah”
Murmushi yayi yace ” Nice name Asiyah, Ina so mu kulla abota da ke ,idan Kuma Zaki bani dama na zame Miki jigo a Rayuwar ki?”
‘dago kanta tayi Tace ” Jigo kuma? Kamarya?”
Murmushi yayi yace ” kina da murya Mai Dadi,Ina nufin na zame Miki Dan Uwa Amma fa idan baza ki damu ba?”
Murmushi tayi Tace ” Na amince , nagode ranar ka Shiga tsakanina da mugayen nan”
Shafe kansa yayi, sai ya juya Mata baya Yana Jin wani Dadi a ransa ko ba komai yasan baza ta manta dashi ba, sai ya juya da niyar Mata magana, ga mamakin sa bata gun, a gigice ya Fara duba ta Bai ganta ba , ya duba yaga ta manta tray d’inta , ya d’auka da sauri ya Shiga mota ya kunna Mata key, ya Fara yawon duba ta, Cikin Sa’a ya hango bayan ta tana Shiga cikin gida, Murmushi yayi yace “So Nan ne gidan su” sai ya juya ya bar gun.
????????????????????????????????
PLEASE SHARE AND COMMENTS
[ad_2]


