MATAR UBA 17

Asiya Tace “Allah sarki Baba Mai gadi sai faman wahala yake a dalili na”
“Gaskiya yana da kirki d’azu nazo wucewa naji Labarin da kike bashi gaskiya matar uba batayi ba, bata da imani ko kad’an, Amma Dan Allah ya sunan ki?”
“Asiyah”
” Masha Allah Asiyah, tun safe Baki ci komai ba tashi ki zauna, da fatan zaki ci Indomie?”
Murmushi tayi ta amsa da “Eh” dama Asiyah yunwa take ji kamar zata mutu rabon ta da abinci tun jiya da safe Nan ma shayi da two slice of bread ta ci, A Baki Dr ke Bata abincin sanda ta cinye shi Tass ta Bata ruwa Tasha Tace “Nagode sosai Dr, Allah ya daka da Alhairi”
Murmushi tayi Tace “Asiya kenan zan so ki kirani da Badiyya”
Ita ma Asiyah Murmushi tayi duk da bata ganin ta Tace “Toh Aunty Badiyya nagode”
Shafa kanta tayi tace “Bakomai Asiyah.”
Shiru sukayi babu Wanda ya sake cewa komai, ko wanne zancen zuci yake Asiyah tunanin ta duk ya koma Kan baba Mai gadi a yayine da Dr Badiyya tunaninta ya koma Kan Asiyah,”shin Anya zan iya barin yarinyar Nan anan ita kad’ai? Kai ina idan nayi hakan hankali na bazai kwanta ba kawai zan Kwana anan muga yanda Allah zaiyi zuwa gobe”
Asiyah ce ta dawo da ita daga tunanin da ta Lula Tace “Aunty kince Zaki koma gida ko kamar dare Yana yi?”
“Eh Asiyah so nake na jira Nan da karfe Tara muga ko zai dawo”
” Yanzu karfe nawa ne Aunty?”
” Karfe takwas ne na dare”
Kai kawaii ta d’aga Mata,ita Kuma Dr Badiyya kallon agogon hannunta tayi lokacin karfe Tara har da rabi ne.
Hashim tun bayan rubuwar su day Asiyah yake Jin hankalin sa a tashe,ji ya jikin sa Asiyah na cikin damuwa Amma Taya zaiyi ya tabbatar da hakan,bazai iya zuwa gidan su ba sabida duk sanda yaje sai ya Zama dalilin kukan shi Kuma baya son kukanta ko da Wasa ne sannan bata da waya bare ya kirata.
Tashi yayi ya d’auki motar sa ya fice daga gidan a hanyar islamiyar su yayi parking Yana jiran fitowar ta daga gida ganin har karfe biyar tayi a fili yace “Maybe ta Riga ta wuce, Asiyah zan jira har ku tashi don hakan shine kad’ai kwanciyar hankali na.”
Zama yayi agun kamar yace har karfe shida duk d’aliban sun wuce Amma bai ganta ba jiki a Sanyaye ya koma gida a ransa Babu irin tunanin da baiyi ba daga bisani yace “Kila aiki aka sata ko Kuma an Hana ta tunda sun Saba a haka ya kwanta bacci barawo ya sace shi.
Baraka da Safiya hankalin su a kwance yake babu abinda ya Sha musu kai kid’a suka saka kure Volume d’in sukayi sai shashewan su suke sun manta da maganar wata Asiya da Mai gadi,a fad’in ta gobe zata nemi wani tunda ya kuskura ta tsallake aikin sa ya bar Mata gate ba kowa.
*ASIBITI*
“Aunty Badiyya ki tafi kawaii abunki ba sai kin jira shi na Naga har yanzu Bai dawo ba”
Rike hannun ta tayi tace ” Kar ki dmau Asiyah har Kwana sai muyi dake anan ban damu ba fatana Allah yasa ya samu kud’in Nan”
” Toh Shikenan Aunty Nagode.”
A ranta Tace ” Kiyi hakuri asiyah i have to lie, Dole na miki karya, don idan na fad’a Miki halin da yake ciki hankalin ki Kara tashi zaiyi.”
Abban Yesmin karfe biyun dare ya fad’a ban d’aki yayi alwala sannan ya tada Nana “Nana bacci bai kamace mu ba ya kamata mu koma ga Allah don mu nemi gafarar sa”
Ba musu ta tashi ta d’auro alwala, tunda suka Fara jero nafilfili Basu tsaya ba har sai da aka Fara Kiraye-kirayen sallar asuba sai da sukayi sallar asuba suka koma bacci.
Yesmin ganin mahaifiyar ta bata fito ba hakan yasa ta Shiga kicin ta had’a wa kanta breakfast ta wuce makaranta.
????????????????????????????????
Mu had’u a page na gaba
MILHAT CE
YAR TERAWA
[ad_2]