MATAR UBA 2

???????????????????????????????? *MATAR UBA*
????????????????????????????????
_(A True Life Story_ )
*Short story*
“`Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)“`
Follow me on Wattpad @milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0
???? *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* ????????️
_(‘Kungiya d’aya tamkar da dubu)_ _____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* much Love.
”’CHAPTER 2”’
????????????????????????????????????????????
……….. Zaune take a Parlor ta d’aura kafa d’aya Kan d’aya tana kallon TV, ji tayi a na kwankwasa kofa tashi tayi ta bud’e ganin mijin tane yasa tayi Murmushi da saurin ta rungume shi had’e da sumbatar sa a kumatu, ganin mace a bayan sa hannun ta rike take da Ghana most go yasa tayi saurin sake shi Tace “who is she?”
Murmushi yayi yace “Sunan ta maijiddah, na d’auko tane sabida ta Rika Taya ki aiki”
Cike da mamaki take kallon sa Tace “Yar aiki a gidan Nan?”
Ya amsa da “Eh”
Tace “Na d’auka kace baka son yar aiki a gidan ka Kuma ya akayi ka canza shawara?”
“Gani nayi kina wahala sosai da aikace aikacen gidan Nan don gidan babbane Kuma Kinga zata Rika Taya ki kula da yaran Nan”
Murmushin gefen baki tayi Tace “Okay idan na fahimce ka karfin d’auko ta da ka yi shine don ta Rika kula da yaran ka ko?”
“Eh Haka ne”
Rai a b’ace tace “To Ni yaushe zaka Fara yin Abu sabida Ni a ko da yaushe maganar ‘ya ‘yan ka kake, sau nawa nake rokon ka da ka d’auko min Yar aiki Amma kaki? toh ban yarda ba ka maida ta inda ka d’auko ta” tana Kai Nan ta bar gun Yana Kiran ta Amma Bata kulashi ba cikin sauri ya bi bayanta sannan ya dawo yace “Maijiddah ki jira ni anan ko? Ina dawo wa”
Ta amsa da to.
Yana yafiya ta Fara kalle kalle tayi Nan tayi chan har ta hango wani kofa tana Shiga Ashe kofan kitchen ne ga mamakin ta taga Yara biyu suna aiki d’ayar na girki d’ayar kuma na wanke wanke hard’e hannu tayi tana kallon su a zuciyar ta Tace “Ikon Allah kananun yaran Nan da aiki haka har da girki abun tausayi?”
“Haba Baraka meyasa kike min haka ne ya kamata ki fahimce ni ki gane dalili na, Kinga idan Zaki fita yanzu Baki da wata matsala akwai Mai kula da su Kuma Kar ki manta idan na dawo daga London zamu tafi yawon shakawata a Saudi kin ga zai Zo Mana da sauki ko?”
Murmushi tayi Tace “To shikenan she can stay”
Zaro Ido yayi sannan ya durkusa a gaban ta yace “Dan Allah dagaske kin amince?”
Yar karamar dariya tayi Tace “Eh na amince”
“Kaai Mata Mata duk halin ku d’aya”
Dariya kawaii yayi.
Yace “Bari naje na yi magana da ita”
“Ya dai fi Kam Kar na canza shawara”
Tashi yayi yace “Allah ya shirya min ke Baraka” ta amsa da “ameen.”
Sai ya fita.
Shigowar sa palon yayi dai dai da fitowar Maijiddah daga kitchen yace “Yauwa Maijidda ta amince Zaki iya Fara aikin ki daga yanzu”
Ta ce “Amma yallab’ai naga akwai wasu Yara su biyu suna aiki Ina ganin kamar ba sai na zauna ba”
Cikin rashin fahimta yace “Yara Kuma masu aiki a gidan Nan? Kaai babu masu aiki ke dai kiyi yanda nace Miki”
Ta amsa da “Toh Yallab’ai”
Yace “Amma kamun Nan Bari na had’a ki da yarana Anisah da Asiyah” ta amsa da “Toh.”
“Asiyah!!! Anisah!!”
Shiru yace “Ina yaran Nan sukayi ne? Anisah!!Asiya!!!, bari na duba su a d’akin su yazo zai haura saman su ne yaji motsi kamar da kwai mutum a kitchen dawowa yayi da baya ya tura kofan kitchen d’in “Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un me ke faruwa a Nan?”
Kallon sa kawaii sukayi sannan suka cigaba da aikin su.
Rai a b’ace yace “Ku bar wannan shirmen ku biyoni”
Ba musu suka bi bayan sa.
“Baraka!!! Baraka!!!” Rai a b’ace yake Kiran sunan ta.
Cikin sauri ta fito Tace “Lafiya kuwa kake Kiran suna na haka?”
A tsawace yace “Me ke faruwa a gidan Nan wanda ni ban Sani ba?”
“Kamarya ban fahimce ka ba?”
” ‘ya ‘ya na gani suna wanke wanke da girki yaushe suka Fara hakan?”
Cikin Rawar murya Tace “Haba Taya Za’ayi suyi girki nice fa nake girkin shigowar kane na fita besides ya kamata su koyi aiki bai kamata su tashi da sakalci ba”
“Kar ki Raina min hankali Baraka yaran Nan suna aikin Nan da kwarewa alamu sun nuna sun dad’e suna aikin Nan sun Saba”
“Oh am sorry na manta a makaranta ne aka sa su yin girkin a wannan subject d’in em…emmm home economics ance su koyi girki nutrition, ko ba Haka bane yan mata?” Tana musu wani irin kallo.
Kirkiran Murmushi sukayi sannan sukace “haka Ne Daddy”
Numfashi ya sauke yace “Sai yanzu naji hankali na ya kwanta na d’auka aiki kike sa su yi ai”
“Haba mijina bazan yi hakan ba.”
“Toh shikenan Ni zan koma office, ki nuna Mata d’akin ta sai na dawo”
“A dawo lafiya”
Ya amsa da “ameen”
Ta koma d’aki tayi kwanciyar ta.
Basu d’au lokaci ba suka Saba da Maijiddah sabida Maijidda mutum ne Mai fara’a da son yara.
Tana Taya su yin assignment sannan Kuma tana Kara musu karatun al’qurani.
Anisah da Maijiddah na gani a Parlor zaune suke da littafai a gaban su da alama assignment suke.
Da sallama ta shigo suka amsa Anisah na ganin ta ta taahi da gudu tana fad’in “Oyoyo oyoyo Aunty Rukayya”
Wacce aka Kira da aunty Rukayya ta amsa da “Oyoyo” hade da rungumar ta.
Tace “ya kike?”
“Lafiya Lau”
“Ina Asiyah take?”
Ta amsa da “Tana d’aki Bari naje na Kira ta” tana Kai nan ta haura sama da gudu.
Maijiddah Tace “Bismillah ki zauna”
Murmushi tayi Tace “Nagode” had’e da Zama.
Tare suka fito da gudu ta rungume ta Tace “Sannu da zuwa Aunty Rukayya”
Shafa kan ta tayi Tace “Yauwa sannu Asiyah ya kike ya makaranta?”
“Lafiya kalau”
‘Wace ce wannan?”
Tana nuna Maijiddah.
“Sunan ta Aunty jiddah itace Mai kula damu”
“Aunty jiddah wannan itace aunty rukayya kanwar mamar mu Ina nufin mahaifiyarmu Wacce ta haife mu”
“Allah sarki nice to meet you jiddah”
Ta amsa da “Nice to meet you too”
“Zaki ban aron su please zamu fita”
Tace “Toh ba matsala”
“Okay thank you, nazo na cika alkwarin da na d’auka zamu fita outing kuje ku shirya” sai da ta Kare musu kallo Tace “Ko da yake naga a shirye kuke ku sako takalmin ku mu tafi” tsalle sukayi sannan suka haura sama Basu d’au lokaci ba suka fita.
*BAYAN WASU AWANNI*
“Maijiddah Ashe Baki da hankali ban Sani ba Taya zaki Bari a fita da yaran Na ba tare da Sani na ba?”
Kai a kasa tace “Kayi hakuri sir zasu dawo yanzu Kuma Tace min ita kanwar mamar suce”
“Yimin shiru tun d’azu nake Jin magana d’aya jirgin karfe biyar zan bi gashi karfe hud’u yanzu so kuke na tafi ba tare da na ga yarana ba”
Baraka Tace “Ya kamata ka Hana Rukayya zuwa gidan Nan ya za a yi ta Rika yin abinda ta ga dama kawaii don taga bamu gida sai ta d’auke su”
Rufe bakin ta ke da wuya sai suka jiyo sallamar su jiddah Tace “Yauwa gasu Nan ma sun dawo”
Rai a b’ace ya tashi yace “Haba Rukayya ya Zaki min haka? Ya kamata ki daina fita da yaran nan ba tare da izini na ba”
Kallon sa tayi cike da mamaki Tace “Sadeeq mene don na fita da su akwai wani matsala ne?”
Kan ya amsa Baraka tayi saurin fad’in “Akwai matsala babba ma ki daina zuwa gidana tunda Yar uwarki ta mutu ki rabu da mu Mana ko dai kina Shirin aure min Miji ne?”