Uncategorized

MATAR UBA 2

Dariya tayi tace “Bani da lokacin ki Baraka”

Shafa kan Asiya da anisah tayi Tace “Zan dawo wani lokacin kunji ku kula da Kan ku” tayi ficewar ta.

A tsawace tace “Jiddah me kike kallo maza ki d’auki akwatin Nan ki fita da shi waje”

Ba musu ta d’auka ta fita dashi riko su yayi Yana Shirin yin magana tayi saurin katse shi ta janye su daga jikin sa sannan ta rungume shi.

Asiyah ta rike hannun Anisah Suka haura sama, sun dad’e a rungume da juna Kan ta sake shi har parking area ta rakashi sai da taga fitar sa sannan ta dawo cikin gidan.

*WASHE GARI* 

Ta dawo daga yawon gantalin ta tarar dasu su jiddah na musu assignment a tsawace Tace “Me ke faruwa anan?”

Jiddah Tace “Assignment nake musu?”

“Assignment?Karki manta ke Yar aiki ce a gidan na”

“Aunty na sani Amma ai nayi makaranta kawaii dai Allah baiyi zanyi gaba bane ”

“Ina magana kina magana? Ke tashi ki haura sama ki tattaro tsumma karanki ki ki bar min gida tunda Wanda ya kawo ki baya Nan”

Jiddah Tace “Amma…” Kan ta Karasa taji saukan Mari a fuskar ta “ki fita nace”

Ta watsar da littafaan tace “Uban me kuke kallon ku tashi ku bar Nan” a tsorace suka bar gun.

Asiyah da Anisah na kuka jiddah na rarrashin su, zata tafi ba don ta so ba.

*NEXT DAY* 

Yau ya kasance Monday sun shirya cikin shigar su ta uniform Riga da skirt ne skirt d’in green ne sannan rigar yellow sunyi kyau sosai bayan su kuma sun rataya jaka.

Har kasa suka durkusa Asiya Tace “Mummy mun shirya zamu tafi makaranta”

A tsawace Tace “Don uwarki sau nawa nace muku Ku daina kirana da Mummy Ni ba uwar ku bace ban haifi biri ba, sannan nace muku Kun daina makaranta yanzu ki ajiye Jakar Nan, Ke Asiyah ki d’auke roban Nan da nasa  lemo a Ciki ke Kuma Anisah ki d’auki ledan pure water Nan kuje ku sayar min”

Sai da suka Karewa lemo da pure water kallo Kan suka kalli juna sannan suka Maida kallon su gare ta.

????????????????????????????????

Mu had’u a page na gaba

Please share and comments

 *MILHAAT CE YAR TERAWA*

[ad_2]

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button