MATAR UBA 3

Bayan ta Kwantar da ita ta fito ta zauna a corridor tana kuka ta had’a Kai da gwiwa tana fad’in “Mummy Ina kike Dan Allah ki dawo,mummy Kinga irin abinda ake Mana kin kasance mutumiyar kirki, mace ta gari Kuma Uwa ta gari kece irin uwar da ko wani d’a zaiyi fatan samu,ko Ina ana yabon kyawawan halin ki, Allah ya jikan ki yasa kin huta.”
Sai da tayi kuka Mai isarta Kan ta tashi ta koma d’aki,yau ma da yunwa suka kwana sannan Anisah zazzab’in yaki sake ta.
*WASHE GARI*
Qawartace ta kawo mata ziyara da alama fita zasuyi.
Qawarta ta naji Tace “Ina yaran ki suke?”
Kallon ta tayi cike da b’acin Rai tace “Kya jiki da wani zance yanzu Yan iskan yaran Nan ne zakice ‘ya ‘yana, na haifi mayu ne?”
Suna cikin magana ne Asiyah ta sauko daga upstairs cikin sauri, Qawar bakaraka Tace “Ganan d’ayar mayyar”
Wani irin kallo Asiyah ta Mata tace “Ni ba mayya bace”
A tsawace Baraka Tace “Ke don uwarki sa’ar kice maza ki bata hakuri”
Ba don taso ba Tace “Kiyi hakuri”
Tab’e baki tayi ta amsa da “Ya wuce”
Durkusa wa tayi a gaban ta Tace “Mummy Dan Allah ki taimaki Anisah ba tada lafiya jiya bamuyi bacci ba, mukai ta asibiti ko Kuma ki bani kud’i na kaita”
” bani da kud’i”
Qawar Baraka Tace “Kaai mummy Tace Miki Kuma naji kin amsa”
Harararta tayi Tace “Kinji na amsa ne bana son rashin mutunci, kin gama ne mu tafi?”
“Eh na gama” tashi sukayi da niyar fita.
Asiyah rike kafarta tayi Tace “mummy please”
Hankad’e ta tayi ta fita.
Suna tafiya Asiyah ta fara dube dube duk ta hargitse parlor Bata ga abinda take nema ba da sauri ta shige d’akin Baraka karkashin gado da ta Fara Dubawa ta koma ta d’aga pillow, ta koma Kan wall drop ta koma gaban mirror tsaki tayi ganin bata samu ba sai ta hango wata Yar karamar purse da sauri ta d’auka ta b’ude,Murmushi Naga tayi ta zaro duba d’aya da gudu ta fita ba ta zarce ko Ina ba sai chemist Mai chemist ganin yanda ta shigo da gudu ya sa ya tsorota Yana kallon bayan ta yace “Yarinya wa ya biyo ki?”
Sai sauke Numfashi take tace “Dan Allah malam magani zaka bani”
“Maganin me kike so?”
Tace “Zazzab’i yake damun Kanwata”
“Zazzab’i da Kuma me?”
“Ciwon Kai sannan bata da Karfi tana yawan Jin jiri”
Yace “Okay” karb’an kud’in yayi ya bata maganin ya fad’a Mata yanda zata Sha tana karb’a ta fice da gudu.
Da sauri ta haura sama tana Shiga d’akin ta ga Anisah na kwance cikin sanyin murya Tace “Anisah tashi Kisha magani”
Shiru bata amsa ba ta Kuma cewa “Anisah bacci kike ne?”
Bata amsa Mata ba.
Da sauri ta nufi inda take kwance tayi kokarin d’aga ta ta kasa dakyar ta samu ta d’ago kanta idon Anisah a kakkafe tayi saurin sake ta tana Kiran sunan ta “Anisah!!! Anisah” da sauri ta rike hannun ta tace “Anisah ki tashi, ki tashi Dan Allah” hannu tasa ta rufe idanun ta sannan ta gyara Mata kwanciyar ta, tana ambatan “Innalillahi wa Inna ilaihirraji’un”
????????????????????????????????????????????
PLEASE SHARE AND COMMENTS
*MILHAAT CE YAR TERAWA*
[ad_2]