MATAR UBA 5

Kallon Juna sukayi a tare suka ce “Ni ne”
Tab’e baki Baraka tayi Tace “I knew it kece Kika b’ata ke mayyar Ina ce haka? Duk abunda Kika tab’a sai ya b’aci ke Kuma safiya nasha fad’a Miki ki dai na kokarin Kare ta in ba Haka ba zan.b’allaki”
Cikin kuka Tace “Mummy wallahi ba itace ba nice na b’ata.”
A tsawace Tace “Safiya fice min daga nan ko na Zane ki”
Cikin kuka Mai sauti da tausayin Yar Uwarta ta haura sama da gudu.
“Ki yi kneel down Kuma yau a Haka Zaki kwana” Bata Musa ba tayi yanda Tace, Baraka ta Fara kalle kalle a fili tace “Ina yarinyar Nan take? Altine!!! Altine!!!” Daga nesa naji ta amsa da “Na’aaam” altine itace sabuwar ‘yar aikin Baraka.
Cikin girmamawa Tace “Sannu da dawo wa hajiya” a tsawace ta dakatar da ita “Dallah Malama ban kiraki don ki gaisheni ba, Ina Kika je har Kika bar mayyar Nan ta lalata min TV?” Tana maganar tana nuna Asiyah da Yar yatsa.
Cikin Rawar murya Tace “Hajiya Ina kitchen ne Shiyasa Amma fa safiya ce take kallon cartoons d’azu ban San ya akayi ba”
A tsawace “Would u shut up ur dirty mouth, by the way yau a Haka zata kwana Karki kuskura ki b’ata Abinci idan Kika Bata Kuma kin San sauran a bakin aikin ki bayan na ci mutunci ki” tana Kai Nan ta haura sama.
Altine tana matukar tausayin Asiyah hakan yasa ta bar gun, safiya sai da tabbatar Baraka tayi bacci ta fito, ga mamakin ta Asiyah na parlor Bata tashi ba.
Cikin tsand’a ta karaso Tace “Aunty Asiyah Dan Allah ki tashi Muje mu kwanta.”
Asiyah duk ta galabaita jikin ta ya jike sharaf duk da AC dake d’akin Bai Hana ta had’a zufa ba,cikin Rawar murya Tace “A’a Safiya so kike mummy tayi fushi dani?”
“A’a bana so Amma kin San daii bakya Mata gwanin ta komai kikayi ba dai dai bane a gunta to me amfanin yi? Dan Allah ki tashi”
Ta na Maganar tana jaan hannun ta Amma Taki tashi har ta gaji cikin sanyin murya Tace “Kina Jin yunwa ko?”
Kai kawaii ta d’aga alamun eh, safiya Tace “Sannu tun breakfast da kikayi ba kici komai ba kin wuni aiki Nan ma two slice of bread kawaii Kika ci bari naje na kawo Miki abinci”
Murmushi tayi ta d’aga kaai alamun to, tana fita ta shigo kitchen ta d’auko plate ta zuba spoon d’aya sai ji tayi ance “Safiya” a tsawace, a razane ta waigo ganin altine ce yasa ta sauke Numfashi a hankali.
Altine tace “Ke me kikayi anan?”
Ba tsoro tace “Abinci naxo d’eba wa aunty na”
Murya kasa kasa “Baki da hankali ne? So kike ki jaa min masifa ko?”
“aunty altine please ki barni na d’eba Mata ko da kad’an ne”
Wacce aka Kira da Altine a tsawace Tace “Ki fita” a razane ta fita, tana kuka.
A ranar Asiyah a kneel down ta kwana, sai da aka Kira sallar asuba Baraka ta fito a tsawace Tace “Ke mayya tashi ki fice daga nan, in kin so ki sake b’ata min wani Abu sai kin kwana kin wuni kina kneel down ” tayi tsaki ta fita, safiya ta shigo parlor da alama ita ma batayi baccin ba, riko hannun Asiyah dakyar ta tsaya kafafuwanta sun kumbara timm, tana tafiyaar tana kuka da taimakon Safiya Asiyah tayi wanka da Ruwan zafi ta gasa jikin ta tayi alwala a zaune tayi sallah sabida kafufuwan ta sunyi tsami baza ta iya tsayawa ba sabida irin azaba da gwiwowinta ke yi.
????????????????????????????????????????
Please wattpadd bana ganin Vote dinku da Comments.
Kuyi hakuri fans kwanaki kusan shida ban samu nayi muku typing ba, Kun San an koma makaranta Zama sai ya gagareni gashi Kuma ban gane karfin jikin nawa ba Ina Mai Baku hakuri.
Mu had’u a page na gaba
Milhaat ce
Yar Terawa
[ad_2]