MATAR UBA 7

???????????????????????????????? *MATAR UBA*
????????????????????????????????
_(A True Life Story_ )
*Short story*
“`Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)“`
Follow me on Wattpad @milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0
???? *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION* ????????️
_(‘Kungiya d’aya tamkar da dubu)_ _____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayi wa Yan Uwa Mata nasiha, idan yazo dai dai to akasi aka samu, Allah ubangiji Ina rokon ka ka bani ikon rubuta abinda zai amfani Yan Uwa musulmai, kamar yanda na Fara lafiya Ina rokon ka kasa na gama lafiya AMEEN.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* much Love.
???????? *MATAR UBA* ????????
_(A True Life Story)_
*Short story*
“`Story and written by FADEELAH YAKUB (MILHAAT)“`
Follow me on Wattpad @Milhaat
Join my group on Telegram https://t.me/joinchat/IhnmqM7EjtZ02IV0
???? *MANAZARTA WRITERS ASSOCATION*????????️
_’kungiya d’aya tamkar da dubu_
https://www.facebook.com/107980080946102?referer=whatsa
_____________________________
*MATAR UBA* Labarine Wanda ya faru dagaske banyi shi don cin zarafin kowa ba face don nayiwa Yan Uwa Mata nasiha,Allah ya bani ikon gama shi lafiya kamar yanda na Fara lafiya ameen.
Dedicated to *MUHAMMAD KARIM MK* Much Love.
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
Not Edited
CHAPTER 7
????????????????????????????????????????????
…………..Haka Rayuwa ta kasance wa Asiyah kullum cikin duka take, wasu lokutan Baraka na Jin tausayin amma Kuma Nana ke Kara hura wa abin wuta, safiya na matukar Kaunar Yar uwar ta, Baraka na Jin haushin hakan, hakan yasa kudiri aniyar raba su ko ta halin Kaka.
Da Murmushi ta ke saukowa daga steps tafiya take cike da takama da izza, ta nemi gu ta zauna a Kan wata doguwar sofa dake parlon, gyara murya tayi Kan ta Fara Kiran sunan altine.
Cikin sauri ta fito daga kitchen hannun ta d’auke da plate Hannun ta duk kumfa da alama wanka wanke take.
Wani irin kallo Baraka ta Mata sannan tace “Je ki wanko hannunki ki dawo Nan, cikin sauri ta Shiga kitchen d’in ba dad’ewa ta dawo, cikin girmamawa Tace “Hajiya gani na dawo”
Wasu makudan kud’i ta cire daga cikin purse d’inta Zaki Kai kimanin dubu d’ari uku, mikawa altine tayi had’e da fad’in “Ga Wannan dubu d’ari uku ne na baki su ki je ki nemi jari ki tattara tsumma karanki ki bar min gida”
Cikin rashin fahimta da fargaba altine Tace “Hajiya Dan Allah kiyi hakuri Ina son aiki na, Yan kauyen mu duka sun San Ina aiki Kuma suna alfahari dani Dan Al…..”
Hannu ta d’aga Maya had’e da fad’in “Bana bukatar jin komai daga gare ki,sannan babu abinda Kika min Haka kawai naji bana bukatar aiki kin gane ko?”
Cikin Rawar murya Tace “Hajiya Amma….”
“Altine idan Kika sake furta wata kalma anan zan kwace kud’in Nan Kuma na koreki kin fahimta?” A tsawace Baraka ke Maganar Nan.
Jiki ba Karfi altine ta fice daga parlon, Nan Baraka ta shiga Kiran Asiyah da safiya, da Sallama suka shigo sannan suka gaida ta cikin girmamawa ta amsa ta wani irin murmushin da yasa hankalin su ya kasa kwanciya, Baraka sabida kullum fuskar ta a tamke take idan kaga tan Murmushi tabbas akwai abinda take shiryawa ne.
Gyara Zama tayi had’e da gyara murya wata bakar leda ta d’auko dake gefen ta tun d’azu Maida kallon ta tayi ga Asiyah tace “gashi” had’e da Mika Mata ledar jiki ba Karfi ta mike ta karb’a.
Baraka ganin Asiyah bata bud’e ledar ba ta tsaya kallon ta Tace “Ki bud’e Mana” jiki na rawa ta bud’e,ga mamakin ta, Uniform ta gani da sandals har da safa irin na safiya, Baraka Tace “Zaki Koma makarant”
Yar karamar dariya Asiyah tayi tace “Nagode Mummy”
Baraka jin ta ambaci kalamar mummy ta tamke fuskar ta had’e da fad’in “Ke don uwar ki sau nawa na fad’a Miki Ni ba mummyn ki bace ki daina kirana da mummy”
Kai a kasa cikin sanyin murya Tace “Am sorry”
“Sorry for yourself, kina jina?”
Kai Asiyah ta girgiza alamun eh ba tare da ta kalli Baraka ba, tana kokarin b’oye hawayen da ke kokarin saukowa da ga fuskar ta.
Baraka Tace “Zaki Fara zuwa makaranta ba don komai ba sai don alkawarin da nayiwa Mahaifin ki, a lokacin da yake kwance a asibiti”
Safiya cikin Zuciyar Tace “Iko sai Allah yau kimanin shekaru shida Kenan da rasuwar Daddy Amma take cewa alkawarin sa, wani aji zata kaini yanzu dai na fi karfin primary sabida na girma, sai lokaci lokaci take Bari na je makarantar ko Kuma sai ta dai daici za a Fara exam sai ta hanani,Ya rabb gani gare ka, kayi saurin kawo min karshen wannan abun na gaji”
“Kuma ki sani aikin gidan Nan kece Wacce Zaki Rika yi Kama daga kan shara wanke wanke, ko da yake kin San komai ai na sai na fad’a Miki ba”
Safiya cikin kuka Tace “Haba mummy me yasa kike Haka ne aunty Asiyah ‘yace kamar kowa”
A tsawace Tace ” Safiya ban hanaki idan ina magana da mayyar Nan ki daina samin baki ba, ko da yake ba laifin ki bane nasan Shegiyar Yarinyar Nan tsinanniyace ta ke hura Miki kunne Amma ba komai, komai yazo karshe da yardan Allah, tashi ku wuce kuci abinci ko Wacce ta d’auki food flask d’in ta.”
A hankali suke tafiyar kamar tura su ake har suka Isa dinning table d’in bayan sun gama cin abinci ko Wacce ta Koma d’akin ta dake bayan sallar Isha ne.
*WASHE GARI*
Asiyah na murna zata Fara zuwa school duk ta tasan a barta a baya Kuma uniform d’in ya d’an ban ban ta dana safiya da alama senior class zata, bayan ta idar da sallah ta Fara gyare gyaran gidan Kan gari ya waye ta gama sai kamshi gidan yake, ta Koma kitchen ta had’a Breakfast sannan ta jera a dinning table Koma d’akin ta tayi wanka had’e da sanya uniform a jikin ta.
Bayan ta sauko ta Samu Baraka da mummy na cin abinci da Sallama ta karasa inda suke cikin girmamawa ta gaishe ta, kallon ta kawai tayi ta cigaba da cin Abincin ta, ganin bata kulata ba hakan yasa ta ajiye Jakarta ta jaa kujera ta zauna,kallon safiya tayi Wacce kanta KE kasa abincin ta take ci hankalin ta a kwance, Murmushi Asiyah tayi Tace “Safiya yau ba magana ne?”
Shiru bata d’aga kanta ba bare ta amsa, tambayar ta sake maimaita a karo na biyu, a tsawace Baraka Tace “Ke bana son hauka idan baza kici abincin ba ki tashi ki fita”
Shiru Asiyah tayi ta Fara cin Abincin cin abincin take Amma Bata Jin d’adin ta, shayi kawaii ta Sha sai ta fita, ta Shiga motar da mummy Tace dashi za’a Rika kaisu makaranta driver na zaune a gaban motar ta gaishe ya amsa yace “in d’ayar?”
“Tana fitowa” rufe bakinta ke da wuya sai ta hango Baraka da Safiya hannun su a cikin na juna, Baraka da kanta ta bud’e Mata motar, safiya na Zama ta fita da sauri toshe hancin ta tayi had’e da fad’in “Ni gaskiya mummy bazan iya xama da ita ba”
Murmushin gefen baki Baraka tayi sannan lokaci guda kamar ba ita tayi ba Tace “Kamar baza ki iya ba?”
“Mummy wallahi warin Kashi take Ni dai gaskiya ta fita ko a raba Mana motar” ta karasa Maganar cikin kuka had’e bubbuga kafarta.
Asiyah baki a bud’e take kallon su cikin mamaki na Jin abinda kunnuwan ta ke ji Kuma idanuwan ta ke gani.
“Kwantar da hankalinki kinji yanda kikeso Haka za’a yi”
Sai ta Maida kallonta ga Asiyah a tsawace Tace “Ke mayya fito nan” a tsorace Asiyah ta fito ganin irin tsawar da mata.