MATAR UBA 7

Driver Baki ya bud’e ya tsaya Yana kallon ikon Allah, Baraka Tace “Sai ki san inda dare ya Miki maza ki Kama hanya ki tafi makaranta, tunda safiya Bata son had’a hanya dake.
Murmushin takaici tayi sannan ta nufi gate d’in ta San Kai ta fice.
Safiya ta Shiga motar, shi kuwa ya tada motar Audu ya bud’e Masa gate ya fita.
Tafiyar almost one hour ne tsakanin makaranta da gidan su a mota, in da kafa ne zai Kai more than two hours, a gajiye ta Isa makarantar tana Isa gate ta samu ana dukan latti, bata tsoron bulala sabida duka ya Zama Mata tamkar man shafawane, bulala goma aka Mata ganin yanda safan ta sukayi datti sai ta shige class, dayawa daga cikin ajinsu sunji d’adin ganin ta musamman shamsiyya har sai da ta rungume ta, Asiyah ganin shamsiyya sai taji kamar an wanke mata dukkanin damuwar dake damin ta, sai karfe biyu suka tashi.
Bayan ta fita sai faman neman Safiya take har sai da ta Shiga class d’in su, wat ce Tace Mata “Ai yanzun Nan driver ya fita da ita”
Kirkiran Murmushi tayi Tace “Nagode”
Sai ta fice daga makarantar, ta d’anyi nisa sai Taji ana Kiran sunan ta ganin Wacce ke kiranta ne yasa ta saki Murmushi.
“Asiyah ina driver d’inku?”
“Kinga sun gaji jirana ne suka tafi”
“Kamarya sun gaji yanzu fa a ka tashe mu?”
Murmushi kawaii ta Mata Tace “Zo mu rage Miki hanya to”
Asiyah dake dama duk kafafun nata zafi suke mata Bata Musa ba tayi saurin bin bayanta tare suka shige motar.
Suna Hira har suka Kai inda zasu rabu,Amma zatayi tafiya kusan na mintuna talatin Kan ta Isa gida godiya tayi was shamsiyya Kan ta fita.
Tana Isa gida Kai tsaye palor ta nufa ta Samu safiya da mummy nacin abinci ta Karasa gun Tace “safiya shine kuka tafi Kuka barni?
Safiya kallon ta kawai tayi tana yagar Naman dake hannun ta, Baraka Tace “Ke don uwarki Baki iya gaisuwa ba?”
Murya na rawa Tace “Ina wuni”
Muguwar harara ta wurga Mata sannan tace “dame Kika dawo?”
“Da kafa”
“Karya kike Munafuka daga makarantar nakune zakice min da kafa ai da baki iso ba har yanzu”
“Wallahi mummy da kafa na dawo”
“Ni Zaki dubi tsabar idona kimin karya,ok wato Saurayin kine ya dawo dake ko?”
Murya na rawa Tace “A’ a wallahi mummy ba Haka bane”
Asiyah batayi aune ba sai saukar Mari da taji Baraka tayi Mata, “bance ki daina kirana da mummy ba, Munafuka, tashi ki bani waje ki Shiga kitchen akwai garin kwake a bakar leda ki jika Kisha Kuma Kar ki yarda ki tab’a min sugar kinji na gaya miki.”
Mahaukaciyar Mari ta Mata hakan yasa ta buge goshin ta Alan tiles na gun sai jini take zubarwa Amma ko a jikinta.
????????????????????????????????????????????
Ina ganin Comments d’inku Kuma Ina Jin d’adin
Allah ya bar kauna.
Comments and share
MILHAAT CE
YAR TERAWA
[ad_2]