Uncategorized

MEEMA FAROUK Page 21 to 30

Koda tayi ƙoƙarin buɗe wa ya ƙi buɗuwa dole sai ta saka code, hakan yasa ta saka sunan Zulaiha but ya ƙi buɗe wa, sai da ta tsaya tayi tunani kafin ta tuna sunan da ake kiran MEEMA da shi, shima ta saka ya ƙi, ta saka sunan mahaifin ta Faruk nan ma ya ƙi buɗe wa, ta saka sunan Daddy domin a tunanin ta haka MEEMAN take kiran sunan Mahaifin ta but nan ma ya ƙi. The same ƙaramin jakan shima da akwai code, cike da jin haushi ta tashi ta fice sabida rashin cikan burin ta, amma dai a sannu a sannu zata riƙa sanya mata idanu domin ta gane Numban da take sanya wa.✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️✳️

             Suna shiga Part ɗin su Habiban babu kowa a parlour’n, sai tace mata, “she just seat there and called her mother.” koda ta je tana Toilet tana wanka shiyasa ta dawo tana mata murmushi tace, “Come, let’s go to my room.”

Tashi MEEMAN tayi ta bi bayan ta suka shiga ɗakin Habiban

Nuna mata kan gadon ta tayi tace mata, “set”. Sannan ta fice ta ɗauko mata Fresh Yo me sanyi ta haɗo da Cup, zuba mata tayi ta miƙa mata tace, “take drink”.

Murmushi MEEMAN tayi mata ta sanya hannu ta amsa tana me furta, “shukran”. Kafin ta sanya a baki ta ɗan kurɓa kaɗan

Habibah cike da fara’a tace, “You can also teach me Arabic because I really like it.”

“Ok insha Allah If you want I will teach you”.

“Thanks. But I want you to tell me about your country. In the past we wanted to come but Baba refused to bring us.”

Murmushi kaɗai MEEMAN tayi bata ce komi ba

Habiban na shirin magana sai ga Inna ta tura ƙofan ta shigo, kallon su tayi fuska a ɗaure tace, “uban me wannan yarinyan ta zo min a nan? Ke kika kawo ta ko Habibah ban miki kashedi ki fita harkan ta ba?”

Tura baki Habiban tayi tace, “kai Inna Wai me tayi muku ne da kuka tsane ta? Ni dai ina son ta tunda ƴar uwata ce kuma idan aka tsaga jini na dole sai an ga nata a ciki..”

“Uban ki tayi mana, ki je ki tambayi uban ki sai ya faɗa miki abinda tayi, tun wuri ki sallame ta ta bar min gida tun kafin in saɓa miki wlh, kuma ki zo ki tattara kayan ki ki wuce gidan Amina tunda ke ba kya jin magana, gwara ki je can ki zauna da ita ki riƙa mata aiki. Ki zo ki wuce kar ki sake kuma in dawo in tarar da ita wlh na gaya miki”. Bata jira cewar ta ba ta ficewar ta

Gaba ɗaya zuciyar Habiba babu daɗi don har ƙwalla ne suka taru mata a idanu, dole ta mayar da su ta saka wa fuskar ta murmushi saboda kallon da MEEMAN take mata tace, “Don’t worry. Inna is talking about the job she did for me.”

Gyaɗa mata kai kawai tayi ba tare da tace uffan ba.

           Shiru ne ya ratsa saboda Habibah ta kasa yadda zata yi ta sanar mata, “Let them go”. Tun da ita ta kawo ta kuma yanzu idan tace mata, “su tafi.” Zata iya gane Innar ta ce ta kore ta

Ita kanta MEEMAN duk da bata yarda da abun da Habiban ta sanar mata ba domin a jikin ta ta ji cewa faɗan da Innar ta yiwa Habibah a kanta ne. Shiyasa ta tashi tana kallon ta tace, “I’m leaving because I have a job. ”

“Ok, let’s go with you.” Habiban tafaɗa tana mata murmushi

Fita suka yi ta kaita har bakin ƙofan su Murjana, bata shiga ba tayi mata sallama ta koma

Ita kuma MEEMAN ta buɗe ta shiga

Umma da Murjana ce a Parlour’n while Umma tana sanar mata da abun da ya faru ɗazu. Shiyasa yanzu da ganin MEEMAN sai Murjana tace mata, “Zulaiha, come here, Ummah she’s calling you. ”

Tsaya wa tayi tana kallon su, sai kuma ta taka ta isa wurin su ta tsaya ƙiƙam a kansu tana kallon su

Murjana tace, “Umma says she will not guarantee that you will stay in this house. You have to go out to work. It is not possible for you to sit on the room of a girl who is being cooked in your mouth and eat and then go back to bed, you have to do the housework since my mother gave it to you.”

“Work?” According to MEEMAN full of surprise on her face

“Yes working or you Don’t do it?”

“Na’am I can’t”. Tayi maganar tana juya wa ta wuce ɗaki. Tana jin Murjanan na zagin ta but bata ko juya ba har ta shige

Umma tace, “wai me tace ne?”

“Cewa tayi wai baza ta iya ba, ki ji fa Umma?”

Ƙwafa Umman tayi tace, “bar Ni da ita bari Abban naku ya dawo ai ya kusa zuwa. Je ki kira min Sajjad a ɗaki”.

Tashi tayi ta wuce ɗakin Sajjad ɗin, koda ta je ta ganshi a kwance a saman gado yana ta sharan barci. Hannu ta sanya ta soma tashin shi tana kiran sunan shi

Daƙyar ya buɗe ido ya zuba mata yana kallon ta

“Umma na kiran ka”.

Shiru yayi kawai yana kallon ta

Ita kuma ta juya ta fice abin ta, ta koma wajen Umma tana sake zuga ta a kan MEEMAN

A lokacin da Sajjad ya fito shima Abban ya dawo

Sannu da zuwa suka yi masa

Ya amsa yana zama cike da gajiya

Umma ta tashi ta kawo masa ruwa kana ta zauna tana kallon sa tace, “dama yanzu jiran ka nake yi Abban Sajjad, a kan wannan yarinyan da ka kawo ta ka ajiye min babu aikin fari bare na baƙi haka zata zauna min a gida wato? Kuma ɗazu na ce tayi min aiki ƙiri-ƙiri Sajjad yace baza ta yi ba, to Ni ban gane abin da ake nufi da ita ba domin wlh baza ta zauna min a sashi ba ta aikin komi ba sai dai ta ci ta sha abun da ta iya kenan, idan haka ne sai dai ta koma sashin Zubairu gaskiya”.

Sajjad da ya buɗe baki ya soma magana Abba ya katse shi da cewa, “kayi shiru Sajjad ban son jin bakin ka. Ke kuma Jamila meye ne na son takura mata don Allah? Mene ne a kan aiki ca nake yi na ce zan kawo miki me aiki but kika ƙi? To ki barta kawai ta zauna tunda ko kin saka ta na tabbata bata iya ba, ba na son ki takura mata don Allah saboda zaki iya rusa mana shirin mu”.

“Abba wai meye shirin naku?” Cewar Sajjad

“Ka bari zuwa anjima zan sanar maka, sannan zancen auren ku mun tsayar da shi nan da wata ɗaya me zuwa domin so muke yi ayi-ayi”.

Umma zata yi magana ya katse ta da cewa, “Please Jamila ba na son musu kiyi abin da nace miki kawai, taso mu je ɗaki akwai maganar da zan faɗa miki”. Ya ƙare maganar da tashi tsaye

Haka ta tashi itama ta bi bayan sa kamar zata fashe

Suna shige wa ɗaki Murjana ta bi Sajjad ɗin da kallo dake ta faman farin ciki sai tace, “wai Yaya don Allah me ka gani a wurin yarinyan nan da zaka aure ta? In fact ma su Abba fa so suke yi su amshi kaf dukiyar ta su kora ta ta bar gidan nan”.

Fara’an fuskar sa ne ta gushe yana kallon ta yace, “whattt Are You saying? Ban fahimta ba?”

Sai a lokacin ma ta gane katoɓaran da tayi sai tayi saurin cewa, “suna so ne su amshi dukiyar ta su mallaki komi nata ya dawo hannun su shiyasa ka ga sun bar ta ta zauna, amma na san tunda ka kawo zancen auren ta sabida kai ne fa kawai zasu iya barin ta a gidan nan, kuma na san Abban zai buƙaci ka taimaka musu idan ta zama matar ka tunda ta ƙi yarda da su”.

Shiru Sajjad ɗin yayi be ce komi ba illa tunani da ya faɗa, sai da Murjanan tayi masa magana kafin ya ɗago ya kalle ta yace, “to Ni ina ruwa na idan har zan aure ta? Su dukiyar ta suke so Ni kuma ita nake so, in dai zasu bar Ni in aure ta wannan me sauƙi ne ai, bari in je wurin Abban.” ya tashi ya wuce ɗakin Abban da ya ga sun shiga

Itama Murjanan bin Bayan sa tayi da sauri.

      ********** *****

      MEEMA da ta shiga ɗakin; computern ta ta ɗauko dana Abee ɗin ta ta ci gaba da aiki, sai dai gaba ɗaya fuskar ta babu wani walwala aikin kawai take yi but tana tuna abubuwan da Murjana ta gama sanar mata. Tana ganin zaman ta a gidan ya kusa zuwa ƙarshe idan har zasu takura mata… Shigowar Murjana ya dawo da ita cikin hayyacin ta, da sauri ta rufe computern ganin ta a gaban ta tana kallon cikin computern

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button