MEEMA FAROUK Page 21 to 30

Hakan yasa ya dakata daga yin musu jagoran da yake yi ya nufe ta da sauri ya duƙa a gaban ta
Magana take mishi tana nuna su MEEMA da yatsa
Shi kuma yana bata amsar tambayar ta. Sai kuma ya tashi a bisa umarnin ta ya nufi su MEEMA ya sanar musu, “kuyi haƙuri Ƙanwar Yallaɓoi tace baza ku samu ganin shi ba.”
“To saboda mene?” Inji Laɗifa cike da haushi
“Haka tace in sanar muku.”
Kallon inda budurwan ke tsaye tayi. Tana nan har yanzu da waya a kunnen ta idanun ta na kallon wani wurin. Hakan yasa Laɗifa ta kalle shi tace, “kai mu je ka kai mu.”
“To.” Yafaɗa da sauri yana yin gaba
MEEMA da bata san ma me suke faɗa ba ganin Laɗifa tayi gaba yasa itama ta bi bayan ta tana jan gajeren tsaki, kasancewar akwai rana sosai duk tafiyan nan da suka yi daga bakin Gate zuwa nan duk ta gama takura, har wani gumi ne yake tsatstsafo mata sabida yanayin shigan kayan ta
Budurwan da itama ta biyo bayan su cikin ɗaga murya tace, “Hi.. Hi..”
Dole suka ja suka tsaya gaba ɗayan su jin muryan ta a sama wanda yake nuni dasu take yi
“Me nace maka? Ina zaka kai su bayan nace maka baza su samu ganin shi ba?” Tayi maganar a ɗaurewar fuska tana kallon House Men ɗin
Kafin yayi magana sai Laɗifa ta riga shi da faɗin, “kiyi hakuri ba wajen ki muka zo ba, shi wanda muka zo wajen shi shi ne yace a shigo damu don haka baza mu koma ba.” Sai ta ja hannun MEEMA suka yi ciki ba tare da ta sake bi ta kan ɗan rakiyan ba
Ita kuma ƙwafa tayi tana bin su da kallo har suka ƙule mata, sannan ta ja dogon tsaki ta wuce zuwa wajen motan ta ta shiga tabar gidan.
A dogon ginin Laɗifa ta ja tunga ta tsaya domin a ranta tana da tabbacin nan ne ya kamata su shiga. Sai ta soma Nocking ƙofan
MEEMA da ke kallon ta tace, “but who is that? What is she asking us?”
“Forgot her. I think she’s also a housewife, or his younger sister oho.”Cewar Laɗifa still tana ci gaba da Nocking ɗin
Babu jima wa aka buɗe musu. House maid ne ya buɗe yana kallon su da tambayar, “wanda suke nema?”
Laɗifa tayi mashi bayanin abin da suka zo yi
Yace, “ok ku shigo”. Ya shigar da su har cikin ƙaton parlour’n ya basu wurin zama. Sannan ya kawo musu drinks sai ya wuce kiran musu me gidan. Be jima ba ya dawo yace musu, “su biyo shi.”
Kallon MEEMA Laɗifa tayi tace mata, “let’s go.”
Tashi tayi ta bi bayan ta suka shiga wani ƙayataccen parlour’n sai dai shi be kai wancan girma ba, amma ya fi haɗuwa sosai da sosai
Wata matashiyar yarinya wacce a shekaru baza ta fi 8yers ba ke zaune a parlour’n tana buga Game a t.v, Remote ɗin na hannun ta tana sarrafa wa. Daga ita sai siririn wando da vest a jikinta, ganin su yasa ta tsayar da abun da take yi tana faman kallon su
Shi kuma house maid ɗin yace musu, “su zauna.”
Zama suka yi while Laɗifa sai baza idanu take yi a parlour’n kasancewar yayi mugun tafiya da ita, babu shakka kuɗi na inda suke, baza ka taɓa cewa a duniya kake ba idan ka ji ka a cikin parlour’n nan saboda tsantsan tsaruwar shi. Sosai haɗuwar sa ya tafi da ruhin Laɗifa kasancewar bata taɓa tozali da irin tsararren gidan nan ba
While MEEMA kuwa kasancewar ta taso a wanda ya fi shi sau miliyan shiyasa bata tsaya kallo ba domin babu abinda ya birge ta sai wani hoto da ta ƙyalla ido ta hanga. Hakan yasa ta sake ɗago kai ta sauke a kan yarinyan da ke zaune tana bin su da kallo sannan ta sake mayar wa a kan hoton. Yarinyar ce a cikin hoton ita da wata wacce bata kai ta Shekaru ba, sun rungume mutumin da ke a cikin hoton duk kan su suna dariya, tsananin kaman da suke yi da shi dole ka gane mahaifin su ne, babban Mutum ne domin ya sha manyan kaya me ruwan madara, riga da wando da malin-malin ɗin shi, a ƙalla bazai wuce shekaru 37years ba, amma tsaban kwarjinin shi da tsantsan kyawun shi dole sai ya cika maka ido. Shiru tayi tana kallon fuskar mutumin tana son zurfafa tunanin ta, sai muryan yarinyar ya dawo da ita a cikin hayyacin ta. Hakan yasa ta mayar da kallon ta wajen ta
Faɗa yarinyar take yiwa hause Maid ɗin a kan shigowar su MEEMA cikin parlour’n
Shi kuma yake sanar mata, “Mahaifin ta ne yace a kawo su wurin.”
Sai ta ja dogon tsaki tana ɗaukan Remote ɗin taci gaba da Game ɗin ta bata sake magana ba bare tabi ta kansu
While me aikin tuni ya fice
Su kuma suka zauna jigum babu wanda ya sake bi ta kansu. Har MEEMA ta gaji ta juyo da kallon ta ga Laɗifa tana cewa, “I’m so tired I’m leaving.”
Hannu Laɗifa ta saka ta riƙe nata tana marairaice fuska da cewa, “Please let us wait a little longer, since we have come so far we will sit and wait.”
Bata ce komi ba ta ɗauke kai ta mayar ga T.vn da yarinyar take yin Game. Sai kawai ta shagaltu da kallon Game ɗin domin tunawa tayi da itama sanda take gida, a lokacin da Abee ɗin ta yake lafiya, tare suke buga Game ɗin suna farin ciki da nishaɗi, kasancewar ta me matuƙar son game shiyasa ba sa rabo da buga wa tare, kala-kala take da su domin har ɗakin Games ne da ita… Hawaye ta ji sun cika mata idanu ta kai hannu ta share waɗanda suka silalo mata a kunci tana ɗan jan majina kaɗan.
_Barka da wannan rana me albarka. Ina ma ɗaukacin masoya na murna da zagayowar wannan rana ta juma’a. Allah ya sada mu da albarkatun ta yasa mu dace duniya da lahira. Ayi weekends lafiya._
????????????
*MEEMA FAROUK*
????????????
*NA_NAFISA ISMA’IL*
*WATTPAD_UMMUDAHIRAH*
*SARAUNIYAR TSOKANAR PERFECT*????????
*PERFECT WRITER’S ASSOCIATION* ????
“`(WE AIN’T PERFECT, BUT WE’RE ALWAYS TRYING OUR BEST TO MOTIVATED AND ENTERTAIN OUR REDERS????)“`
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*P.W.A✍️*
*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan littafin ga Shugaba adila *SAFNA ALIYU JAWABI,* Allah ya daɗa ɗaukaka ki Amin._
*NO_22*
Yanda aka shanya su a wurin ne yasa ran MEEMA ya ɓaci ta miƙe tana kallon Laɗifa fuska babu walwala tace, “Please get up and go. I’m very tired.”
Bata kai ga yin magana ba sai wata yarinyar ta fito a guje tana kiran sunan, “Aunty Hafsah.. Aunty Hafsah.” Tafaɗa kan kujeran da ƴar uwan ta ke zaune
“What’s wrong?” Ta tambaye ta tana ajiye Remote ɗin hannun ta
Ita yarinyar tuni ta mayar da kallon ta kan su MEEMA tana kallon su. Sai kuma ta nuna su da yatsa tana cewa, “Aunty waɗannan fa su wane ne?”
“Oho ki tambaye su ga su nan.”
“Baby come I want to ask you.” Cewar Laɗifa tana ma ƙaramar murmushi
Hakan yasa ta taso izuwa wurin ta
Sai ta riƙe mata hannu still tana mata murmushi tace, “what’s your name?”
“My name is Yusra.”
“Ok Yusra ko zaki kira mana mahaifin ki?”
Gyaɗa mata kai tayi kana ta juya da gudu ta hau upstairs
Tafiyan ta yasa Laɗifa ta kalli MEEMA tace, “Sister, sit down. Now she will be called for us, Let’s wait a little longer.”
Ɗauke kai tayi bata ce komi ba kuma ta ƙi zama
Babu jima wa sai ga Yusran sun fito ita da mahaifin nata. Daga shi sai jallabiya fara sol da waya a kunnen sa yana amsa call
Har suka sauko ƙasa Laɗifa idanun ta na kanshi, sosai take tasbihi da tsantsan kyawun da Allah ya yi masa
While MEEMA itama tunda ta kalle su sau ɗaya sai ta sami wuri ta zauna
Har ya iso wajen hankalin sa be kai ga su Laɗifa ba, sai da ya zauna a ɗaya daga cikin manya-manyan kujerun parlour’n sannan ya sauke fararen idanun sa a kan su