MEEMA FAROUK Page 21 to 30

Hafsah da Yusra tuni sun haye kan shi
While shi kuma yana ci gaba da wayan shi, sai dai tunda ya ɗaura idanun sa a kan MEEMA ya ƙi ɗauke wa. Hannun sa ɗaya na a saman giran sa yana murza wa hakan yasa baza ka gane ita yake kallo ba
Ita kuma a jikin ta taji ana kallon ta shiyasa ta sake ɗaga kai a karo na biyu ta kai duban ta gare shi. Hakan yasa idanuwan su suka shige cikin na juna. Ko soconni bata ɗauka ba ta cire nata idanun tana jin gaban ta na faɗuwa matsananciya, tabbas tana ji kamar ta san wannan fuskar, a jikin ta tana jin kamar ta taɓa ganin sa
Shima haka a wajen sa. Shiyasa ya kasa cire idon sa a kanta yana son tuna inda ya san fuskar ta. Be ɗauke idanun nasa ba har sanda ya tuno ta kuwa. Ya tuna sanda ya je Umrah ya hayo jirgi daga Riyadh, ita ce wacce suka zauna a jirgi tare zuwa Abuja. A lokacin ya dawo da dare babu wanda ya sani shiyasa ya wuce gidan Abokin shi Hashim a barikin sojoji ya kwana. Tabbas ita ce. Hakan yasa ya lumshe idanuwan sa yana me sake buɗe wa a kanta, sallama yayi da wanda suke wayan ya mayar da kallon shi sosai a kan su har Laɗifa yace, “ku ne kuke nema na?”
“Eh ranka ya daɗe!” Inji Laɗifa cike da murmushi a fuskar ta
“Ok sorry I settled you, there’s something I’m doing what’s important in it.”
Hakan yasa MEEMA ta sake ɗago kai ta kalle shi jin abun da yace, sai suka sake haɗa ido tayi saurin ɗauke kanta
Shima haka janye nashi idon yayi yana kallon yaran nashi da cewa, “ku ɗan bamu wuri zamu yi magana My Babies.”
“Ok Daddy.” Suka faɗa a tare suna tashi da gudu suka yi cikin gidan
“Ina sauraron ku. I give you ten minutes to do what brought you here.”
“Ok Sir.” Laɗifa ta faɗa da sauri tana amsar Laptop ɗin hannun MEEMA ta buɗe
Ita kuma ido kawai ta zuba mata bata ce komi ba.
Nan ta soma mishi tambayoyi tun daga full name ɗin shi zuwa shigan shi siyasa
A taƙaice dai ba wani amsa mata sosai yake yi ba, wasu ataƙaice yake bata amsa. Daga ƙarshe duba agogon sa yayi yace, “lokaci ya cika. Ina da abun yi.” Sai ya tashi ya wuce be jira cewar su ba
Dole su ma suka tashi suka fice a gidan. Sanda suka hau mota Laɗifa take cewa, “I don’t think we will ever see him wlh, he is very well connected and it is beautiful, but I honestly didn’t like the way he answered our questions.”
MEEMA da ta kwantar da kanta a jikin kujeran idanun ta a rufe, tana jin ta but ko magana ta gaza yi sabida ɗan tunanin da ya hau mata kai, so take yi ta tuna inda ta san fuskar nan domin ya tsaya mata a rai. Sai da Laɗifa ta taɓa ta sannan ta ɗago kanta tana kallon ta
“I mean you’re silent what do you do?”
“Nothing.”
“Ok call Bro Idris and let him know we’re done.” Laɗifa tafaɗa tana ci gaba da tuƙin
MEEMA bata ce komi ba ta ɗauki waya ta soma neman layin Idris. Sai dai a kashe aka ce
Laɗifa tace, “maybe it is still not in Zaria. We’ll try again later.”
Da haka suka ƙarisa wajen aikin su.
Zuwa ƙarfe uku Laɗifa tayi dropping ɗin ta a gida. Lokacin da ta shiga Parlour Hajiya da Zabba’u suna zaune sun yi baja-baja da kaya
“These are your belongings, come and see if they do it for you.” Cewar Hajiya bayan MEEMAN ta zauna
Kallon kayan take yi bata ko motsa ba
Zabba’u da ke washe baki tace, “These items are all Hajiya’s choice for you. In fact, Hausa clothes will look good on you. God willing, they will please you.”
MEEMA kallon Hajiya tayi tace, “Thanks grandma, I am very happy.”
“Ok come and see. Look at everything that is not yours and you will be changed.”
Kanta ta gyaɗa kafin ta tashi ta iso gaban kayan ta durƙusa tana duba wa
While Zabba’u tana taya ta ɗauko wa
Atamfofi ne da lessi sai materials kala-kala. Sai takalma har da gyale
Ɗago kai MEEMAN tayi tana kallon Hajiyan a marairaice tace, “But how can I use them? I can’t.”
Dariya suka yi mata
Hajiya tace, “You will learn, no matter what you say you can’t. Since you came back to our country you have to learn all our culture.”
Murmushi kaɗai tayi tana ci gaba da ɗaga kayan, wasu kuma sai ta kara a jikin ta kafin take ajiye wa
Hajiya tace, “You go with Zabba’u to take your sewing, then choose the style you want. Go eat and rest later and take it to your sewing shop.”
“Ok.” MEEMA tafaɗa tana tashi ta wuce ɗaki
Yayinda Zabba’u kuma ta haɗa kan kayan ta mayar a cikin leda.
Koda MEEMA ta shiga ɗaki wanka tayi ta saka riga da wando masu taushi ta fito Parlour. Abinci ta sawo ta zauna a gefen Hajiya tana ci tana sauraron hiran nasu. Sai da ta gama ta wuce ɗaki ta ɗaura after dress baƙi a saman kayan ta tayi Rolling da ɗan kwalin shi kafin ta fito suka fita. Drever ya ɗauke su suna shirin fita itama Ummee ta dawo gidan.
Koda ta shiga parlour’n ta tarar da Hajiya. Sannu da gida tayi mata kafin ta tambaye ta, “ina su MEEMA zasu je ta gan su a mota?”
“Kaya ne na ɗaukar mata wajen Dillaliya, ɗazu nace ta kawo min shi ne zasu kai ɗinki.”
Gyaɗa kanta tayi, sai kuma tace, “amma Hajiya da kin bari na siyan mata da kai na kar ɗawainiyar yayi miki yawa.”
Hajiya tace, “yanzu ma ban hana ki siyan mata naki ba, Ni nayi ra’ayi baza ki hana Ni abun da nayi ninya ba.”
“To Hajiya ai ba na faɗa bane abun.” Ummee tafaɗa tana murmushi
Shiru Hajiya tayi mata tana mayar da idanun ta kan t.v dake faman aiki shi kaɗai
Ita kuma Ummeen sai ta wuce sama inda ɗakin ta yake. Sai da tayi wanka ta sauya kaya kafin ta fito ta zuba abinci ta dawo Parlour. Tana cikin ci ne sai kuma ta kalli Hajiya da cewa, “Hajiya baki yiwa MEEMA magana a kan ƙadaran mahaifin ta ba, ya kamata a san abun yi sabida be kamata a bar su a can ƙasar babu me kula da komi ba, sannan akwai magada a ciki kamata yayi a sauke mishi nauyi tun yanzu.”
Hajiya da ta dawo da kallon ta kan Ummeen tace, “nayi tunanin hakan, sai dai be kamata mu tayar da maganar yanzu ba, mu bari zuwa nan gaba bayan ta sake sakin jiki sosai damu, har yanzu ina ganin damuwa sosai a tattare da MEEMA, har yanzu ba wai ta manta mutuwar mahaifin ta bane, shiyasa duk wani abun da zai saka ta farin ciki nake iyakan ƙoƙari na wajen naga nayi mata. Tunda ke kin gaza a matsayin mahaifiyar ta ki bar ni Ni inyi mata, Ni kaɗai take kallo take jin daɗi a yanzu.”
Cike da sanyin jiki Ummee tace, “Amma Hajiya mene ne na gori kuma?”
“A’a ba maganar gori bane gaskiya na faɗa. Yarinyar nan tana cikin damuwa tsantsa, ko fuskar ta kika kalla bata cika yin fara’a ba, wani abun ma tana yi ne kawai domin mu, don haka ba na son ma a cika mata maganar da zai riƙa tuna mata da mahaifin ta.”
“To shikenan.” Cewar Ummeen tana ajiye Plate ɗin abincin. Sai kuma ta ɗauka ta kai kichen ta haura sama.
Ba su wani jima ba su MEEMA suka dawo gidan.
Da dare suna cin abinci a dainning Idris ya shigo gidan. Kai tsaye wajen su ya nufa yana jan kujera ya zauna yace, “nima yau da Ni za’a ci abincin duk da na cika ciki na daga gida.”
Hajiya tace, “dama wa ya isa yace ban da kai za’a ci Mijin?”
“A’a gaskiya ban girka da kai ba, ka tashi ka bamu wuri.” Inji Zabba’u cike da barkwanci
“Wai kin ji Hajiya in tashi?”
“A’a zauna ka zuba abun da ranka yayi maka, idan ba ka kawo wa taya za su samu su ci?”
“Yauwa Hajjaju na Ni kaɗai, an dai Gwale wasu.” Yafaɗa yana dariya